*✍️MARUBUCIYA✍️*.
*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*Daga Alkalamin👇
*Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*
*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*
Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin
أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!
✍️_13
Ina godiya, na faɗa tare da ƙoƙarin zaunawa, Bismillah na faɗa sannan na zauna ina kallon Yareema Ibraheem tareda zuba kunnuwa ina sauraron abun da zaice.
gyaran murya yayi yace "Ummu Dilshad sati biyu da suka gabata kin tanbaye ni gameda matsayin abun da kike rubutawa tun daga randa kika fara yimana laɓe har zuwa ranar da za'a gama warware komai in Allah ya kaimu ko?"
gyaɗa kai nayi tare da faɗin "Eh yaya yareema"
To ina mai tabbatar miki da cewa shima naki yana da amfani domin kuwa kece zaki fara rubuta naki labarin ma, yanzu ke zaki yanke ma kanki shawarar kodai ki buga a takadda kokuma ki fara ɗaukar shi kina posting a Online saboda kema naki yana da matuƙar muhimmanci domin hakan ke nuni da cewa kema shaida ce gameda dukkan abubuwan da Bulus yayima Nusaiba bayan Aljanu da Ruhi na fatalwa dake nan a Facebook waɗanda duk sanda kika fara posting suma zasu fara karantawa wanda a sati biyu da suka gabata nace duk wanda yake ganin abun da nake faɗa ba gaskiya bane to ya shiga facebook ɗin yayi searching ɗin kalmar *VALAK* In sha Allah zai ga accounts ɗinsu na facebook dasuke amfani dashi kamar na Bil'Adama. Inaga dai kamar na gama baki amsarki ko?
Eh ɗan uwa Yareema ka gama kuma na gode, to amma inna fara posting ko wallafa nawa kenan hakan yana nuni da cewa na Nusaiba bashi da amfani kenan?, kuma in aka karanta nawa kuma aka karanta nata labaran zasu zama iri ɗaya kuma sai nake ganin masu karatu zasu gundira da karanta abu guda ɗaya daga marubuta biyu, dole in sun karanta ɗaya subar ɗaya.
Murmushi yayi yace "Inaah dole zai zamana akwai banbanci sosai saboda ita Nusaiba akan ta ne abun ya faru ke kuma ƙawarta ce dan haka dole sai nata labarin yafi naki bayyanar da wasu abubuwa na musamman wanda duk inda bazai fito a naki labarin ba zakiji na faɗa aduk sanda nazo dai dai gurin a bayanina, Ummu Dilshad inaso kisani wannan Labarin da zaki fara posting ko wallafawa labarine na musamman wanda yake ɗauke da abubuwa masu muhimmanci na rayuwar Al'umma kuma akwai wata halaka dake tunkarar bil'Adama wacce ta hanyar littafinnan zaki bayyanar da iya abun da kikaji anan wanda akwai wasu ɓoyayyu kuma da dole sai ana Nusaiba zasu bayyana waɗannan abubuwa kuma sune zasu farkar da Bil'Adama daga gyangyaɗin baccin asara da bala'in da suka faɗa wasu kuma suke kan harnyar faɗawa dan haka nakeso ki jajirce kiyi iyayin ki gurin ganin wannan abu ya tabbata duk da nasan akwai ƙalubale na musamman da zaki fuskanta amma in kika daure kika yi haƙuri sai komai yazo ya wuce kuma kiga cikin ikon Allah ansamu nasarar abun da ake nema, Allah yasa mudace.
Ameen na amsa dashi sannan nace, na gode sosai, babu komai kawai yace sannan ya kalli sauran jama'ar ɗaya bayan ɗaya sannan ya kalli malam Yahuza yace "Malam kafin in cigaba da yi muku bayani ina so in sanar da kai cewa inaso ka haɗama, Haj Ruƙayya, Ummu Dilshad, da kuma Nusaiba magun guna na musamman wanda bazan faɗa maka anan ba sai Allah ya kaimu Anjima da daddare zan ziyarceka har gurin bada maganin ka wanda ni da kaina zan nuna maka tareda faɗamaka dukkan nau'oin magungunan da nakeso aba kowacce daga cikin su, abun dayasa bazan faɗa anan ba shine inna faɗa Ummu Dilshad zata rubuta a nata labarin kuma banaso ya bayyana anata sai ana Nusaiba.Ummu Dilshad kinji banbanci na farko ko?
YOU ARE READING
MARUBUCIYA.....
SpiritualBAYYANAR ƁOYAYYAN SIRRI NA MUSAMMAN, LABARI MAI ƁANGARORI GUDA BIYU, MASU ƊAUKE DA CHAKWAKIYAR AL'AMURAN RAYUWA DA SOYAYYA ME BAN AL'AJABI. "WANNAN SIRRIN DA ZAI BAYYANA YANA DA MATUƘAR AMFANI GA DUKKAN JINSI NA HALITTAR BIL'ADAMA IN JI (YAREEMA ƊAN...