EPISODE 14

15 2 0
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.
   

*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*

Daga Alkalamin👇
              *Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.

*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

                      ✍️_14

"Dalili na farko in baku manta ba acikin labarin dana baku da farko ai zaku iya tunawa da *Amadu Ado Kanti* ko yaron ka kai Alhaji Yusuf wanda ka tsinta kasa ka shi a inuwa shikuma yayi ƙoƙarin saka a rana?"

gyaɗa kai Abba yayi yace "Sosai na tuna Amadu Ado Kanti wanda naso bashi auren Nusaiba kafin in fasa inba Muktar"

Abba nayin shiru sai Yareema Ibraheem ya chigaba da faɗin "To kaga wannan fasa auren da kuma korar da kayima Amadu? ba ƙaramin ɓatamai rai tayi ba dan atarihin Rayuwar shi gabaɗaya bai taɓa yunƙurin ganin ya ɓata wata mace ba tare da ya samu nasara ba sai akan Nusaiba hakan yasa yabar gidan ka zuciyarshicike da baƙin ciki da kuma burin ɗaukar fansa akan ka kokuma Nusaiba abun da baka sani ba shine har haɗa baki yayi da wasu ƴan ta'adda da nufin suzo suyi maka satar kayan shagonka gabaɗaya jin haka danayi sai naje gurin a daren da suka shiga kasuwa nayi wani siddabaru wanda da sukazo gabaɗaya suka nemi shagon da aka turosu suka rasa, ina maka bayani ne game da wancan lokacin wato bayan ka koreshi da wata ɗaya yaso yayi maka wannan ta'asar.

to dayaga bai samu nasara ba sai ya koma gidan su can Katsina yaje ya dinga shirya maka asiri yana jifanka dashi amma sakamakon cewa kai jajirtaccene gurin yin ibada da Addu'oi  duk abun dayayi sai ya lalace tun kafin ya ƙaraso gareka,  To ganin hakane yasa ya koma kan Nusaiba tun ma balle dayaji labarin cewa tayi aure tofa shine hankalin shi yayi matuƙar tashi ya dinga jifanta da asirai kala kala amma itama sam basu kamata ba.

Ya daɗe yanayi bai taɓa kamata ba har sai lokacin da tayi sakaci da yawan yin addu'oi da kuma karatun Qur'ani sakamakon sakacin da matan Bil'Adama kanyi wani lokaci sai kaga mace wai bata iya tsayawa ta bautama ubangijinta kokuma sai ta rage kaso a ƙalla 70% cikin 100% na lokacin da take bama ubangijinta gurin ibada wanda suna kafa hujjane da cewa aiyuka sun ƙarum musu saboda hidimar yara mai gida da kuma shi kanshi gidan, kuma sam hakan bai dace ace sun bar Allah saboda Al'amuran Duniya ba dan alokacin da ka saki Allah shima sakeka yakeyi koda kuwa kana da tarin buƙatu da damuwa bazai taɓa yaye maka ba harsai ka ɗaga hannu ka roƙeshi kuma ka gyara tsakanin ka dashi gameda aikata zunubai. duk da dai dama bawa baya taɓa tsallake abun da Allah ya hukunta masa domin akwai wani Hadithi na manzon tsira SALLAHU ALAIHI WASALLAM DA YAKE CEWA:

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now