!BA'AMA FARABA! EPISODE 3

38 3 0
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.
   

*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*

Daga Alkalamin👇
              *Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.

*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

                      ✍️_3

Sosai likitan idon daya duba ta ya dinga faɗa, kafin daga baya yace danma Allah yasa abun yazo da sauƙi, amma kuma ba wani sauƙi bane domin kuwa nan gaba abun na iya zamar mata matsala, sakamakon ɗan taɓa saman jijiyar gani da bulalar tayi amma ayanzu kun burin zai saɓe sai dai akwai yiwuwar bayan ta girma ta iya rasa kaso talatin daga cikin ɗari na daga ganin ta, musamman in tayi ƙiba sosai kokuma ƴar dai dai saboda alokacinne gudun jinin jijiyar sai samu ɗan presure ɗin da saiya dinga taɓa saman inda bulalar ta taɓa.

bayan sun dawo gida Alhaji Yusuf ya shigo da niyyar yimata faɗa sosai sai daikuma a yanayin da ya sameta ne yayi matuƙar taɓa mishi zuciya domin gaba ɗaya wunin ranar kasa komai tayi sai kuka kawai takeyi abun gwanin ban tausayi suna shigowa ta tafi da gudu ta rungune Nusaiba tana faɗin "dan Allah Nusaiba ki yafemin dake da mahaifinki wallahi sharrin shaiɗanne.

Tabbas kuwa abunda ta faɗa gaskiya ne sharrin shaiɗanne saboda duk abubuwan da takeyi Bulus shine yake sata, wanda sam bada yarda ta yake yin hakan domin tun kafin mubar Asibiti mukayi faɗa sosai wanda har nace mai wallahi muddin ya kuskura ya maida Nusaiba kirista to saina kai ƙarar shi fadar mahaifina duk da cewa baban shi shima Hakimin baƙaƙen Aljanune amma mahaifina yafi nashi isa da mulki domin shi sarki ne gabaɗaya bama na fararen Aljanu kaɗai ba, kuma yasanni sarai tun muna yara domin makaranta ɗaya mukayi ta primary har secondary a makarantun ƴaƴan sarauta tunda shima mahaifinshi yana da sarauta wanda bayan mun rabu dashi ni na tafi makarantar *UNIVERSITY OF MADINA* na karanta likitanci a musulumci shikuma banma san wacce yaje ba kota ƴaƴan Aljanuce kota bil'adama oho to sai kwatsam muka kuma haɗuwa dashi bayan Auren Mahaifiya da mahaifin Nusaiba, wanda dama can ni ina tare da ahalin gidansu ne amma sam ba acikin jikin su ba dan yanzune ma karona na farko a shiga jikin bil'adama, kuma kasancewata da ahalinsu ya samo asaline tun iyaye da kakanni sakamakon ajinin Alhaji Yusuf Akwai sarauta kaɗan saboda kakan shi na takwas babban Malamin fadar sarkin Kano ne me suna *MALAM ATIKU* Sakamakon irin gudun mawar da yake ba fada yasa sarkin wannan lokacin ya ɗauki yarshi yar wajen fulani ya bashi auren ta wato *GIMBIYA FATIMA* to alokacin mahaifina ne yake tare da Gimbiya Fatima yana ƙoƙarin bata gudunmawa me amfani a rayuwarta, mukuma lokacin ƴaƴan shi mu ɗari biyar ne kuma nine ƙarami acikin su  amma babba agurin mahaifiyata shiyasa duk inda nake nakan dan ganta kaina da babba ɗan sarki, duk da awannan lokacin  banfi shekaru casa'in ba amma duk da haka duk sanda za'a haifi wani daga cikin ahalin su dani ake zuwa gurin taimakawa gurin karɓar haihuwar.

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now