EPISODE 15

29 2 0
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.
   

*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*

Daga Alkalamin👇
              *Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.

*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*

*⚠️END OF FREE PAGES⚠️*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

                      ✍️_15

Ta samu ganyen magarya Busashshe ko ɗanye mai kyau da yawa ta tanade su, sannan sai na ce mata ta ƙara buɗe kunnuwanta da kyau taji dukkan abubuwan dana faɗa ta riƙesu a kanta kuma ta tabbatar da ta aikata su tacemin to, sai na fara faɗamata kamar haka.

'''Zaki samu Ruwa mai tsabta a buɗaɗɗen abu kamar kwano ko roba sai ki ƙirga ganyen magarya guda bakwai ki daddakasu suyi laushi saiki zuba acikin ruwan sannan ki saita fuskarki a ruwan kidinga karanto abubuwan da zan faɗa miki yanzu kitabbatar numfashin ki yana shiga ruwan. sai ki karanta:

(1) Fatiha ƙafa 1.
(2) Ayatul Kursiyyu ƙafa 1.
(3) Suratul A'araff daga aya ta (106 zuwa ta 122).
(4) Suratul Yunus daga aya ta (79 zuwa ta 82).
(5) Suratul kafirun.
(6) Suratul falaƙ kafa 3.
(7) Suratul Nass ƙafa 3

kuma kina iya ƙarawa da waɗannan Addu'oin, wato

"Allahumma Rabbinnas Azhibilba'as Washfi Antash shafi laashifa'a illaah shifa'uk, Shifa'an laah yugadiru Saqaman. ƙafa 3

da kuma

Bismillahi Urqeenee minkulli shai'in Yu'uzeenee, wamin sharri kulli nafsin Allahu yash feenee, Bismillahi Urqeenee. ƙafa 3

kitabbatar kin dingayin hakan safe da yamma a ƙalla har tsawon kwanaki bakwai kina sha kuma kina wanka dashi a guri mai tsabta, shima in sha Allah zaki ƙara jin daɗin jikinki sosai.

tacemin "To Abba na gode sosai kuma in sha Allahu zanyi to amma su duk waɗannan ayoyi da addu'oin da kace da kuma ganyen magaryar duk menene amfanin su a gareni.

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now