EPISODE 19

3 0 0
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.
   

Daga Alkalamin👇

*Ummu Dilshad*

*Wannan littafin na kuɗine, ₦200 ne kacal zakuyi Mobile Transfer (0158547894, GTBANK, SHAMSIYA ABDULLAHI). Ko Card na MTN zaku ɗauki hoton shi ku turo ta *(07013872581).*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

                      ✍️_19

Ina ta kiran sunan ta amma bata amsawa gashi kuma ko motsi batayi sai dai ta riƙemin hannuna gam nayi iya yina in ƙwace na kasa, sosai na tsorata da yanayin da Nusaiba tashiga, ga kuma mamaki danni a gabaɗaya abun da Yareema Ibrahim ya faɗamana ban taɓa jin irin wannan ba a tarihin Nusaiba, sosai na tausaya mata dole tayi kuka dan bala'oin sun mata yawa.

Ina cikin zancen zuci ne sai naga ta miƙar da kanta ta koma ta zauna har alokacin hannayen mu suna tare sai naga ta kalleni tayi murmushi tace "Ummu Dilshad ba yanzu ya kamata kisan abun da Nusaiba keson faɗa miki ba, ba ke kaɗai ba hatta waɗanda kuke haɗuwa aɗakin nan zakuyi matuƙar mamaki idan kukaji babban sirrin dake faruwa"
da sauri na ɗago na kalli Nusaiba, abun da na fahimta ne yasa nayi saurin zare hannuna daga nata domin nasan Yareema ne Nusaiba bace, murmushi yayi yace Ummu Dilshad kenan duk da kincemin kin daina tsoro amma gashi yanzu kin nuna alamar tsoro anya ma kinayin addu'oi sosai kuwa.

gyaɗa kai nayi alamar eh nace "Eh yaya Yareema inayi amma kasan in abu yazo maka da bazata ne sai ahankali yanayin jikin ka zai ɗauki sauyin, amma ni banji tsoro ba"

murmushi yayi yace "Nayar da dake, Yanzu abun da nakeso dake shine bayan mun gama tattaunawar mu ta yau in kowa ya watse inaso ki tsaya ki saurari dukkan abun da Nusaiba zata faɗa miki in Allah ya kaimu ranar da za'a ƙara yin sabon zama sai in fayyace muku dukkan abun da kukai magana akai in sha Allah"

gyaɗa kai nayi nace "Allah ya kaimu da rai da lafiya"

Ameen ya amsa dashi yana rufe baki sai ga Hajiyar Muktar nan tazo ita dashi muktar ɗin sai dai yau ba'azo da ƙanwar muktar ɗin ba.
sukai sallama nida Yareema muka amsa, hajiya ta samu guri ta zauna batace komai ba sai yareem ne yace mata "Sannu da zuwa Hajiya" da kamar bazata amsa ba sai kuma naga ta amsa da sauri ina tunanin ko ta fahimci cewa ba Nusaiba bace domin Nusaiba bada Hajiya take kiranta ba.

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now