*✍️MARUBUCIYA✍️*.
*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*Daga Alkalamin👇
*Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*
*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*
Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin
أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!
✍️_6
Ganin tabbas da gaske Hajiya Zilai kemaganar yasa Hajiya Ruƙayya miƙewa tsaye bayan ta gama kafeta da idanuwa, cikin takaici tace "Hajiya Zilai! tashi ki fita kibar gidannan tunkafin inyi miki abun da baki taɓa zatan zan iya miki shiba"
Sororo Hajiya Zilai tayi tana kallonta cike da mamaki, itama sai ta miƙe ta ƙare mata kallo sannan tace "wai dan Allah Hajiya meye na faɗane mara kyau da har zai sa kiyimin irin wannan cin kashin da wulaƙancin har haka?
kama ƙugu Hajiya Ruƙayya tayi tace "ke kike ganin hakan a matsayin wulaƙanci amma ni gani nake nayi dai dai ne saboda a tunani na koda wani ne yabaki wannan shawarar kyace bakyaso bawai ke ki wanko ƙafa ki taho har ki iya buɗe baki kicemin wai mu haɗa ƴar ki RUMANA da ɗana MIKTAR ba kema dai kin san hakan ba mai yiwuwa bane ko?
cikin mamaki Hajiya Zilai tace "to amma saboda me zaki faɗi haka? nidai gani nayi babu wani aibu a cikin wannan auren in banda Alkairi da kuma fatan samun ƙara ƙarfafa zumunci a tsakanin iyalen wa da ƙani ko?
gaskiya ne kam, amma kuma hakan ma yana iya zama sanadin raba kan zumun ci saboda kinga dai na farko bazan taɓa yima ɗana cushen wata ba inbaya so koda kuwa ƴar ƴar'uwa tace balle dangin miji, na biyu kuma kinga wannan yaro nawa Muktar shi kaɗai ne Allah ya bamu ɗa namiji, kuma kema ƴarki ita kaɗai gareki dan haka gaskiya banaso suzo suyi aure su haifo ɗa ɗaya ko ƴaɗaya kuma ni gaskiya ina son jikoki dayawa dan inaso in sha Allah ta tsatson Muktar a samu zuri'a da yawa kona Zainab, kinga ko in suka haifi ɗa ɗaya naji shiru ba'a ƙaraba gaskiya aure zan ƙaramai kukuma na tabbatar bazaku taɓa jin daɗin hakam ba tunda nasan kinaji da ƴarki kamar yadda nake ji da ɗana, dan haka gaskiya ban amince da wannan haɗin ba abarshi kawai karma ki sake yin tinani irin wannan.
YOU ARE READING
MARUBUCIYA.....
SpiritualBAYYANAR ƁOYAYYAN SIRRI NA MUSAMMAN, LABARI MAI ƁANGARORI GUDA BIYU, MASU ƊAUKE DA CHAKWAKIYAR AL'AMURAN RAYUWA DA SOYAYYA ME BAN AL'AJABI. "WANNAN SIRRIN DA ZAI BAYYANA YANA DA MATUƘAR AMFANI GA DUKKAN JINSI NA HALITTAR BIL'ADAMA IN JI (YAREEMA ƊAN...