*✍️MARUBUCIYA✍️*.
*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*Daga Alkalamin👇
*Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*
*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*
Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin
أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!
✍️_8
Ganin yadda nayi tsanin firgitane yasa ya sauke murya yace *"UMMU DILSHAD"!*, Jikina bai dena rawaba na amsa da *na'am KAKA!* Na faɗa ina zare ido.
Murmushi yayi yace " ki kwantar da Hankalinki kinji ko, ni ba abun tsoro bane nima Halittar Allah ne kamar ku ban bancin mu kawai shine ku kuna da gangan jiki mukuma Ruhine damu kawai dan Haka ina mai nuna miki cewa Allah shine kaɗai abun tsoro, kuma karki kuma cemin kaka kinji kina iya kirana da 'ƊAN UWA IBRAHEEM' Kuma ako da yaushe kidinga tuna cewa ALLAHU SUBHANAHU WATA'ALA ya fifita halittar bil'adam tareda ɗaga darajar su fiye damu halittar Aljanu, dan haka mu ba ababen tsoro bane, kinji ko?
gyaɗa kai nayi tare da faɗin "Eh naji Yaya Ibraheem" amma duk dahaka akwai sauran tsoro a tattare dani.
ganin hakan yasa yace UMMU DILSHAD Kice...
*( وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ )*sai na faɗi abun da ya faɗa.
sai ya kuma cewa, kuma cewa.....
*( وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحْضُرُونِ )*
Shima na faɗa, sai yace kiyi ta maimaitawa har sai kinji gabaɗaya bakya jin tsoron komai sai Allah da ya Haliccemu.
to kawai nace sannan na shiga mai maita abun dayace in tayi, cikin ikon Allah kawai sai najini sakayau babu wani tsoro a tattare dani gabaɗaya, kawai saina yi shiru ina maimai tawa a zuciyata.
shirun dayajine yace yawwa Ummu Dilshad hakan ke nuni da cewa yanzu bakyajin tsoron komai kenan ko? carab nayi na amsa da "Eh sai Allah kaɗai nakejin tsoro Yaya Ibraheem"
YOU ARE READING
MARUBUCIYA.....
SpiritualBAYYANAR ƁOYAYYAN SIRRI NA MUSAMMAN, LABARI MAI ƁANGARORI GUDA BIYU, MASU ƊAUKE DA CHAKWAKIYAR AL'AMURAN RAYUWA DA SOYAYYA ME BAN AL'AJABI. "WANNAN SIRRIN DA ZAI BAYYANA YANA DA MATUƘAR AMFANI GA DUKKAN JINSI NA HALITTAR BIL'ADAMA IN JI (YAREEMA ƊAN...