WASA FARI GIRKI, EPISODE 1

241 13 5
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*
   

*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*

Daga Alkalamin👇
              *Ummu Dilshad*

Wattpad @UMMUDILSHAD.

Instagram @Official_Ummu_Dilshad

*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

*Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin, SABO DA TSARO*

*أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.*
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!.

Dukkan godiya da yabo suntabbata ga Allahu Subhananhu wata'ala, daya bani damar fara wannan littafi na MARUBUCIYA, Tsira da Aminci su ƙara tabbata ga shugaban halitta Annabin ƙarshen zamani da yazo mana da gaskiya, wato _Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wasallam. Allah ya bani iko da damar rubuta abunda zai amfanar dani da kuma ku masu karatu da dukkan Alkairai🤲🏻

                      ✍️_1
*MINNA*
*SASHI NA FARKO*

Misalin ƙarfe 4:30pm, na yammacin wata Ranar Litinin Takwas ga watan Afirilu, Shekara Alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da shida (Monday, April_8_ 1996).

A unguwar *Hospital Road*, wani madai daicin  gida ne mai kyau ta bayan babban Asibitin general Hospital dake minna, nazo wucewa naji muryar wata baiwar Allah tanata salati tareda da faɗin sunayen Allah dakuma dukkanin addu'oin da sukazo bakinta, wani lokacin ma har bata faɗa daidai sakamakon tsananin ciwon naƙudar dake matuƙar damunta da hanata sukuni, jitake kamar bayanta da mararta zasu tsage dan azabar ciwon da takeji, mutum ɗaya ne a gefenta yana ta faɗin "sannu *BILKISU* , yakamata kitashi mu taka zuwa Asibitin ko a ƙafane tunda babu nisa inkuma bazaki iya zuwaba sai in kaiki a mota kiga dama nurse ce mana tayi nan da awa biyu mu koma to kuma ai yanzu ma kaɗanne ya rage awanni biyun su cika, lallaɓa kitashi muje" ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin ɗagata tsaye.

shikaɗai ya kamata ya sakata a mota, yajata ya ƙarasa da ita Asibitin da gidan su ke bayan shi.

yana zuwa aka shiga da ita ɗakin haihuwa (Labour Room), nurses mata biyu ne likita ɗaya keta ƙoƙarin karɓar haihuwa sai dai duk da azabar ciwon da wannan baiwar Allah bilkisu kesha har alokacin haihuwar akwai saura domin kuwa koda suka aunata 3cm take dan haka sai suka umarceta da cewa ta tashi ta dinga motsa jiki acikin ɗakin haihuwar batare da ta fita waje ba, da ƙyar ta iya amsa musu da Toh tana nishi......

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now