EPISODE 10

21 2 0
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.

*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*

Daga Alkalamin👇
*Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.

*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

✍️_10

Bayan fitan kowa daga gidan sai Yareema Ibraheem ma ya tafi, yana tafiya sai nan take Nusaiba dake zaune akan kujera ta faɗi ta kwanta akai, sai da tayi kamar mintuna goma sha biyar ne sannan ta fara salati tare da yin wata irin doguwar Hamma. A hankali ta fara buɗe idon ta tana kallon sama kamar wacce ta tuna da wani abu da sauri ta miƙe ta zauna tana zare ido tana ƙarema falon kallo, shidai Muktar na zaune yana kallon ta bai cemata komai ba dan shima yanata tunanin abun da zai faɗa matane idan ta tanbayeshi.
ganin dai cewa ta tabbatar babu kowa a fallon ne yasa ta buɗe baki tace Abban Haneef ina su Umma da Abba suke kuma naga basa nan? ta ƙarasa tanbayar tana kallon agogo sannan ta maida dubanta ga muktar tace kuma naga daga sanda sukazo zuwa yanzu gurin awa uku kenan, dan Allah me yake faruwa ne?

ganin tana nema ta shiga damuwane yasa ya miƙe da sauri ya dawo kujerar da take ya zauna kusa da ita, ya kama hannayenta biyu yace Ummu Haneef ki kwantar da hankalinki kinji ba wani abu bane ya faru, kawai muna zaune ne sai wannan ciwon kan naki mai zafinnan ya fara damun ki sai kuma can kika fara Hamma da ƙyar kike magana, dana tanbayeki sai kikacemin bacci kikeji nayi nayi dake ko Ruwa ki tashi ki kawoma su Umma amma sam kika kasa yin haka to shine fa bacci ya kwashe ki ganin haka yasa su Abba sukace bari su wuce kawai sa ƙara dawowa su dubaki wata rana wai dama sunzo suga yadda jikin naki yake ne kinsan dayake mun yi waya da Abba yake tanbayata ya kuke sai na cemai jikin nakine ƴan kwanakin nan yake ɗan damun ki yasa ko makaranta bakya iya zuwa.

yana gama faɗin haka sai ya dafa kafaɗar ta yace "sai dai gaskiya ummu Haneef kin bani kunya sosai yadda kika kama baccin nan "

da sauri ta waigo ta kalleshi tace "kunya kuma wace irin kunya kake magana akai"

Murmushi yayi yace ai ba kunya kaɗai kika bani ba harma jin daɗi nayi bayan su Abban sun tafi, dan yadda naga suna kallon mu dagake harni sai na fahimci kamar suna zargin ko ciki gareki to alokacin sai naji kamar in nutse aƙasa dan jin nauyin yadda suke kallon mu. bayan sun tafi kuma haka kawai sai na tsinci kaina cikin Farinciki tareda addu'ar dama Allah yasa da gasken cikin gareki.

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now