EPISODE 4

35 2 1
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.
   

*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*

Daga Alkalamin👇
              *Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.

*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

                      ✍️_4

Saboda irin son da Amadu Ado kanti ke nunama Nusaiba ne yasa yaron ya shiga ran Abba sosai, dan dama koda yazo garin yazone domin neman sana'ar yi dan haka Alhajin ya ɗaukeshi kamar ɗan shi tunda dama alokacin Umar bai gama karatu ba balle ya miƙamai ragamar kasuwancin amma duk da hakan yakan bi mahaifinnasu kasuwa inba shi da abunyi ko gurin zuwa.

sosai suke jin daɗin aiki tare domin Alhaji bashi da ƙyashi ko baƙin ciki kuma gashi da tausayin duk wani wanda ke ƙarƙashin shi, shikuma Amadu yana da ƙoƙari sosai gurin nuna iya gaskiyar shi ga kasuwancin.

Sosai soyayya ta shigi kowani ɗaya daga cikin su, sai dai duk da irin mugun halin da mahaifiyar Nusaiban ke nuna ma ƴartata bai hanata hango wani irin abu mara kyau gama da Amadu ba domin sam bai kwanta mata ba, hakan yasa wata rana bayan dawowar Alhaji Yusuf daga kasuwa da daddare ranar a ɗakinta yake bayan sallar isha'i suna zaune a falon ta bayan ta kawo mai Abinci yana ci suna taɓa ƴar hira.

Sai tace mai "niko Alhaji inka gama cin Abinci inaso inyi magana da kai in bazaka damuba".

murmushi yayi ya kalleta yace "basai na gamaba Bilkisu Uwar gida sarautar mata faɗi ina cin abinci ina saurar ki in dai Alkairine"

Alkairi ne in sha Allah duk da dai bansan yadda zaka ɗauki abun ba, saboda ba dolene abun da nake hange yazama kaima kana hangen shi ba musamman ma in yadda tayi yawa tsakanin mutum da mutum wani lokaci ido yakan rufe aka ganin laifin wanda ake tare dashi......

katseta yayi da faɗin Bilkisu zanso ki faɗi duk abun da kikeso ki faɗi direct dan bana son ɗanwaken zagaye.

ba haka bane Alhaji, dama gameda Amadu ne nakeso in tanbayeka inji tun kafin ka yanke shawarar bashi auren Nusaiba yakamata ace shin kasan ɗan wani garine?

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now