EPISODE 21

22 2 7
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*

                *BY*
*UMMU DILSHAD*

Wattpad @UMMU_DILSHAD

*INTELLIGENT WRITERS ASSOCIATION..®️✍️(Onward together).*

*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

                   ✍️21

Yareema Nagama marin Ɗahira da sakina. ya koma ya zauna bakin sakina buɗe cike da mamaki dama mu kanmu dake cikin falon. ɗahira kuwa miƙewa tayi tsaye ta kama ƙugu tana masifa "Nusaiba wannan  wani irin iskanci ne zaki fake da wani Aljani ki mareni cikin jama'a sabo da tsabar raini? to bari kiji wallahi bazan yarda ba in kin yaudare su ni bazan yaudaru ba, mu har a faɗa mana Aljanu muda muke tare da babban dodo. to wallahi saina rama" ta ƙarasa maganar tana tafiya cikin zafin nama zata nufi gurin Nusaiba kafin ta ƙarasa sai Yareema ya miƙe tsaye da sauri ya nuna ta da hannu ya ɗaga murya yana faɗin "Da izzar mulkin Allah zaki faɗi yanzu" nan take Ɗahira ta faɗi ƙasa tana numfashi da ƙyar. gabaɗayan mu da muke ɗakin muka miƙe tsaye cike da tsoro da mamaki. Yareema ya koma ya zauna yana duban mu cikin natsuwa yace "Karkuji tsoro ku zauna" muka zauna muna kallon ikon Allah. ya juyo ya dubeni yace "Ummu Dilshad ina sakon danace ki ɗaukar min a gurin Nusaiba?"

Da sauri na miƙe nazo na kawo mai wayata ya karɓa  ya daddanna sai ga sautin muryar Nusaiba tana kuka tana bada labarin dukkan abubuwan dake faruwa a Ƙungiyar MUNE. da kuma gabaɗaya hirar da mukayi da ita a lokacin da yareema yace in tsaya.

Ana gama saurara sai Hajiya Bilkisu mahaifiyar Nusaiba ta fashe da kuka cikin kuka take magana tana faɗin "Innah lillahi wa innah ilaihirraji'un. Wallahi wannan abubuwan da Nusaiba ke faɗi suna daga cikin abun da suka sa nake tsanar haihuwar ƴaƴa mata sabo da tunda na samu cikin ta nake mafarkin wata ƙungiya wacce ta kasance itama ta mata ce zalla wanda abubuwan da ake aikatawa a ciki sunfi waɗannan muni, aduk sanda na kwanta bacci sainayi mafarki irin haka sannan sai ace min abun dake cikina ma mace ce kuma zatayi shugabanci a irin wannan ƙungiya hakan yasa sam naji na tsani in haife ta musamman bayan da nayi scarning akace min macece naso na zubda cikin ba tare da mahaifinta ya sani ba, wannan abu ne wanda sam ban taɓa faɗama kowa ba nayi yunƙurin zubar da cikin Nusaiba har so uku amma yaƙi zubewa.

Ta ƙara fashewa da kuka mai ƙarfi. gaba ɗayan mu tausayin tane ya kamamu sai da tayi kuka sosai sannan Yareema ya dubeta cikin murya mai ban tausayi yace "Bilkisu kiyi shiru ki godema Allah domin dukkan abubuwan da suka faru ni shaida ne kuma baki da laifi hatta cikin Nusaiba da kikaita ƙoƙarin zubarwa nine na dinga hana dukkan wani abu da kika sha ya ƙarasa inda zaije ya zubda cikin wanda duk waɗannan abubuwan da kikai tayi gabaɗaya sharrin Bulus ne amma ina mai tabbatar miki cewa da izinin Allah komai yazo ƙarshe domin yau zakuji wasu abubuwan daga bakin wacce aka shirya waɗannan abubuwan tare da ita. Amma kafin nan zan muku matashiya , a lokacin da nace muku na taɓa tafiya na bar Nusaiba da Bulus in zaku iya tunawa har nace muku sunyi wani faɗa da Ummu Dilshad wanda da ƙyar aka shirya su. a tsakankanin waɗannan lokutan ne Bulus ya haɗa kai da wata Ƙungiyar mata zalla da ake aikata Alfasha da bautar shaiɗan"

cike da mamaki muka haɗa baki mukace "Shaiɗan!" yareema ya jinjina kai yace "Eh Shaiɗan, saboda dukkan wasu Alfasha da wata halitta zata aikata a doran ƙasa tana yin bautane ga shaiɗan inma ta sani inma bata sani ba , saboda Allahu Subhanahu wata'ala yasha kawo mana ayoyin dake nuni da girman kai da ƙinyin biyayya da Shaiɗan yayi mai gurin yima Annabi Adamu sujjadar daya umarce shi da ita, kamar a Suratu Baqara Aya ta 34,

( وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ أَبَىٰ وَاسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ )

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 15, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now