*✍️MARUBUCIYA✍️*.
*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*Daga Alkalamin👇
*Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*
*MY......(Janaf) fitowa ta musamman kikayi a page na biyu na littafin MARUBUCIYA sosai nake gode irin ƙaunar da kike nunamin, ke ta musamman ce a gurin duk wani mataki da zan taka a duniyar Rubutu kina cikin sahun farko gurin kasancewa ɗaya daga cikin sanadin samun dukkan wasu nasarori nawa, sosai nake ganin girman ki da darajarki a ido my, Sonso fisabilillah❤️*
*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*
Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin
*أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.*
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!
✍️_2
Washe gari da sassafe malam yahuza ya iso gidan kamar yadda yayi Alƙawari.
Direct Alhaji Muktar yayima malam yahuza mai ruƙiyya iso izuwa babban Falon su na sama, ya samu guri ya zauna shikuma sai ya wuce bedroom ɗin su can ya tarad da Nusaiba tana saka kaya bayan shafa mai da tagama hakan ke nuna cewa daga wanka ta fito.
cikin kulawa ya kalleta yace ki hanzarta ki fito falo malam na jiranki, toh ta amsa mishi dashi cikin girmamawa, sannan ya juya ya fice.
fitowarshi falon yayi dai dai da shigowar wasu mata guda biyu da namiji ɗaya manyan dattawa ne amma ba tsufa sosai ba ɗaya daga ciki zata kai shekaru Arba'in da biyar ita kuma ɗayar bazata wuce shekaru Arba'in da biyu ba, shikuma namijin bazai gaza shekaru Hamsin da bakwai ba.
anatse bakunan su ɗauke da sallama aka musu iso sannan suka shigo, cikin girmamawa naga Muktar ya ɗan rusuna ya gaishesu ɗaya bayan ɗaya ya kira mace ta farko da *UMMA* ta biyu kuma naji yace mata *INNA GAJE* sai kuma naji ya kira namijin da *ABBA*.
bayan sun samu guri sun zauna ne sai Abba ya kalli Muktar yace mishi "Alhaji Muktar, Allah dai yasa lafiya kuma da fatan ba wani laifin Nusaiba tayi maka ba da yasa ka kirawomu gabaɗaya kace kanaso muzo gidannan da sassafe duk da dai na yadda da tarbiyyar Nusaiba amma abun da ɗaure kai tunda yau fa kusan shekarunku shida kenan da yin aure amma ba'a taɓa jin kanku ba kuma baka taɓa yimana irin wannan kiran na gaggawa ba, to waima ina Nusaibar take naga kuma bata nan gurin Allah dai yasa lafiya"
YOU ARE READING
MARUBUCIYA.....
EspiritualBAYYANAR ƁOYAYYAN SIRRI NA MUSAMMAN, LABARI MAI ƁANGARORI GUDA BIYU, MASU ƊAUKE DA CHAKWAKIYAR AL'AMURAN RAYUWA DA SOYAYYA ME BAN AL'AJABI. "WANNAN SIRRIN DA ZAI BAYYANA YANA DA MATUƘAR AMFANI GA DUKKAN JINSI NA HALITTAR BIL'ADAMA IN JI (YAREEMA ƊAN...