EPISODE 9

25 2 0
                                    

*✍️MARUBUCIYA✍️*.

*_INTELLIGENT WRITERS_ _ASSOCIATION...®️✍️_*
*_(Onward together)._*

Daga Alkalamin👇
*Ummu Dilshad*
Wattpad @UMMUDILSHAD.

*Dedicated to, Hafsat Hafnan (Lovable Auta💖)*

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

Karku manta ku daure kufara karanta wannan addu'ar dama wasu addu'oin da sukazo bakinku kafin ku fara karanta kowani page na wannan book ɗin

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

✍️_9

Da sauri na girgiza kai bakina yana rawa nace "A'a yaya Ibraheem bana so kabar shi kawai ba sai ka ɗibarmin ba"

murmushi yayi ya koma ya zauna yace "Ummu Dilshad kenan bakyaso in ɗibar miki daga cikin labaran dana tanadarma Nusaiba amma kin iya zuwa ki laɓe kina Rubuce duk abun da kikaji domin ki maidashi littafi ko?"

gyaɗa kai nayi da sauri ina faɗin "Eh yaya kayi haƙuri inma kace wannan ma kar in rubuta wallahi na barshi yanzu ma zan tafi dama nazo wucewa ne inje gidansu ƙawarmu *Habiba* in biya mata muzo mu gaishe da Nusaiba dan takirani satin daya gabata tacemin bata da lafiya shiyasa bata zuwa makaranta" na ƙarasa maganar da nufin miƙewa inbar gidan, da sauri yace dawo ummu Dilshad ki zauna.

jiki a sanyaye na dawo.

sosai ya saukar da murya yace "Ummu Dilshad inaso ki natsu ki faɗamin me kike tsoro naga daga nace zan ɗibar miki labarai kika tashi da sauri zaki tafi?", ina so kibani amsa a natse.

komawa nayi na zauna na tattaro natsuwata nace "Yaya Ibraheem ba komai nake tsoro ba sai wahala wallahi banason duk wani abu da zan sha wahala musamman in akace an haɗa da mutanen ɓoye to sam bana sonshi, kuma ina me tabbatar da harsashen cewa muddin in ka ɗibarmin saikasa wani daga jinsin ku na Aljanu sun kasance tare dani ko ajiki na kokuma a gefena kuma in mutum baiyi yadda kukeso ba kuna wahalar dashi ko ku hanashin yin wasu abubuwan, nikuma gaskiya banason ko ɗaya daga ciki.

murmushin dai ya kumayi kamar yadda ya saba sannan yace "maganarki gaskiya ce Ummu Dilshad, domin kuwa dayawa daga cikin marubuta kusan duka ma zance duk suna da Aljanu inma dai farare kokuma baƙaƙe.........
carab na karɓe zance da faɗin "amma dai bandani ko yayana?

MARUBUCIYA.....Where stories live. Discover now