Romantic Love Story

20 2 0
                                    

  ✨ ✨✨✨✨✨
      *BARRISTER FARIIS*
      ✨✨✨✨✨
 

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).

          *P.W.A*✍️

*STORY*

*&*

*WRITING*

          
  UMMUH ABUU SADEEQ
          (Cuty pie).

  الهم صلي ءال محمد وال ءالي محمد كما صليت ورحمت، وبركت وال ءالي ابرحيم بل ءلمين انك حميد المجيد.

.........✍, Ohh Allah if this good for me! my deen, future, dunya, and akhira make it easy for me open the doors and give me barakah, if it bad for me! my future, present, deen and dunya close it for me blocked it and take me away from it make me happy with your degree of life.
   
NOTE: banyi littafina don wani | wata ba ƙirƙirarren lbr ne wanda nayi shi da kaina, ban yadda a juya min littafi ta kowacce siga ba, yin haka ya saɓawa dokata don Allah akiyaye.

   Allah yasa mu amfana da darusan dake cikinta, kuskuren kuma Allah ya yafe mana Ami, yasa yadda na fara rubutawa lfy na gama lfy.


BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM....

    0️⃣1⃣

Nmadi Azikwe International airport Abuja.

   Landing jirgin kenan bayan wasu mintuna passengers ɗin suka fara fitowa.

A hankali yake saukowa daga matakalar jirgin cike da ƙasaita da taƙama kamar bai son tafiya gefe guda ya samu ya tsaya yana ƙarewa airport ɗin kallo kamar yau ya fara zuwa Abujan, sanye yake cikin riga long sleeve blue da black jean sai kamo jacket black mai gashi gashi, yayin da kuma ƙafarsa ke sanye cikin wani black toms, rana ce takwalo da sauri yaja hular jacket na jikinsa ya rufe kansa, box ɗinsa ya ɗauko tare da barin wajen don baƙaramin rana ake ba, gashi har ynz bai ga wanda akace zai zo ɗaukarsa ba, mai adaidaita ne yazo wuce wa yace ina muka nufa?, sai da ya shiga yace Asokoro.
  
A bakin wani haɗaɗen gida ya sauke sa ya bashi kuɗin shi har ya fara tafiya mai adaidaitan yace ga canji da hannu ya masa alamar ya barshi, yaja adaidaitansa yana mai jindadin canjin da akabar mashi.
  
   Ba tare da ya kwankwasa ƙofar gate ɗin ba yashige, Lance Corporal Liba (mai gadi) yana jin redio kallo ɗaya ya masa ya cigaba da tafiya don baya jin zai iya magana yadda rana ke damusa, liba ne ya taso duk da ya daɗe rabonsa da ganin shi hakan baisa ya manta shi ba da sauri ya cimmasa, sannu da dawowa yallab'ai andawo lfy?.

" Alhmdllh abin da yace kenan ya barsa nan ".

  Wajen redion sa ya koma ya cigaba da jin labarai yana mamakin rashin ɗauko wannan bawan Allah.

Gidan shiru sai kukan geese kawai kake ji ba ƙaramin sauyi gidan yasamu ba don an sake abubuwa da yawa, gida ne mai girman gaske mai ɗauke da sashe biyu, na farkon ya nufa a hankali yake tafiya saboda gajiyar zaman jirgi.
 
Kujeru ne masu kyau set biyu a falon na farkon adon baki da blue sai brown da ja da center table tsakanin kujerun sai chineese carpet shimfiɗe a ƙasa gefe kuma locker ce ta littattafan karatu sai TV dake kan wani lafiyayyen standard falon dai ya haɗu sosai.
 
  Bene ya haye sannan ya ciro mukulli dake zip ɗin gaban akwatin shi ya buɗe ƙofan.

    A bakin ƙofa yaja ya tsaya yana mai bin ɗakin da kallo baƙaramin kura yayi ba, ɗaura akwatin kan royal cushion ɗin dake falon yayi sannan ya juya falon ƙasa, jin wayar sa na ringing yasa shi kallon mai kiran sai da ya zauna sannan ya amsa da muryarsa sassanya.

   " Hello Daddy "
 
FARIIS ina fatan kun sauka lfy?.

  " Lfy alhmdllh "

Masha Allah zan kiraka zuwa anjima in ka huta.

  " Toh amma Daddy nadawo gida ɗakina duk ƙura ba agyara ba gashi babu kowa gidan ".

  Sai da na gayawa Balkisu fa a tabbatar an gyara ma ko'ina.

" Daddy adaidaita ma na hawo zuwa gida babu wanda yazo d'auka na ga yunwa inaji ace shekara uku bana gida amma babu wanda yazo tarbata don Allah yaushe zaka dawo? ".

   Sosai ya tausayawa ɗan nasa kayi hkr jibi zan dawo kaji?.

  Shikenan Allah ya dawo da kai lfy.
   
'Ameen'.

   Ka kula da kanka Allah ya maka Albarka.

    Lumshe idanunsa da suka canja kala yayi, ya kurawa silin ido yana tunano mahaifiyarsa da tun yana ƙarami ta rasu gashi ynz bashi da wani gata sai Daddynsa, Momy bata son shi ko kaɗan.
  
   Sai da ya share ɗakin ya gyara ko'ina tsaf sannan yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya T shirt fara da bakin wondo yayi kyau sosai, ya ɗauki key motarsa ya fito koda ya sauko ƙasa babu kowa, yayi mamakin rashin ganin kowa ciki har da masu aikin gidan.
   
  Ɗakin Momy ya shiga yayi sa'a kuwa ƙofar abud'e take ahankali yayi sallama amma shiru babu amsa har ya juya zai wuce ya jiyo muryarta tana faɗin,,,,
 
   Waye haka ke ta rabka sallama kamar zai kashe min dodon kunne?.
   
Ya bata amsa da FARIIS ne.
 
    Ina zuwa toh, sai gata tafito ɗauke da jakarta alamar fita zatayi, au ashe ɗan masu gidan ne ya dawo tana wani matse fuska.

Bai damu ba don yasan halinta nan ya gaisheta ta amsa mashi a wulaƙance tare da raɓwa ta gefen shi zata wuce da sauri yace

' Momy banga alamar akwai masu aiki agidan nan ba? '.

    Tsaya wa tai tana kallon shi tabbas babu don na koresu! ta cigaba da tfyrta.

  Ganin ta barshi tsaye yasa shi bin bayan ta da sauri..

  ' Naga kamar baki san da dawota ba koh? '.

  Sai da ta zauna a motar sannan tace, toh In na sani uwarka zan ma, tadakawa direba tsawa uban mika tsaya jira ja mota mutafi ta watsa mashi harara suka wuce.

    Tsaye yayi yana bin motar da kallo zuciyar shi na suya shi azaton shi ko ta canza, tunda ya daɗe rabonsa da gida ashe gskyr masu magana da suke cewa mai hali baya fasa halinsa.

   Gun Mai gadi ya ƙarasa yana tmbyrsa.
Tun yaushe masu aiki suka bar gidan nan?.
 
     Oga yau kusan sati ɗaya kenan mai gadi ya bashi amsa.

  ' Okey wake dafa abincin da kuke ci? '.

   Ai tunda hjy ta sallamesu sai dai mu siya da kuɗinmu gaba daya ta kori masu aikin daga ni sai direba, hatta masu goge2, da masu wanke mota da wanda suke kula da shukoki duk babu su mu biyu ke yin duk waɗannan aiki.
     
Ido kawai ya zuba wa liba dake ta kwararo bayanai.

     Ngd, sunanka don yashige min?.

  Washe hakoran shi yayi corporal liba nake ya ƙarashe maganar tare da ƙamewa irin na tsofaffin sojojin bariki, bayan sun gama magana ya figi motar sa restaurant yaje ya cika tumbinsa tare da take away ɗin anjima sannan ya zazzaga gari sai kusan biyu na rana ya dawo gida.
   

    A falon ya tadda ƙannansa kwance kan carpet da gudu dukkansu suka rungume shi suna gaishe shi.
 
   Yaya ashe dagaske ne yau zaka dawo, cewar kanwarsa Nawwal.
   
" Murmushi yayi eh mana ya makaranta kuna karatu koh? "
  
Fido tace,, sosai ma yaya.

"Good, kaifa? ya tmby Asim wanda ke kokarin amsan ledan hannunsaa".

     Asim wadda shine ƙarami yace yaya Allah muna jin yunwa me ka taho mana dashi.
 
  Acici shiyasa ka zama big boy, ya miƙa mashi ledan bari naje na huta.
  
  Toh yaya wllh Momy batayi mana abinci ba cewar Nawwal.

   Zaro idanu yayi kai haba dai to meyasa?.

Nima ban sani ba duk takori masu aiki daga muci biscuits sai drinks koh kuma in zata dawo daga wajen aiki tayo mana take away.

   Jim yayi yana nazarin maganar shikenan naji bari na huta anjima sai mufita yawo ko asim yaja mashi hanci.
   
Duk suka sa dariya ya haye sama don agajjiye yake sosai, sai da yayi wanka yasa short niker ya kwanta kan makeken gadon shi sai barci...............

BARRISTER FARIISWhere stories live. Discover now