✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).Wannan shafin naki ne zaysal ummah ina sonki da yawa.....
0️⃣7⃣
Gaba ɗaya ta ƙanƙameshi yama rasa ya zaiyi ko kwakkwaran motsi ta hanashi yi ga idonta kulle hannun ta ya riƙe jin tana neman yage masa kaya cikin muryar tsoro tace don Allah kar kabari ya dakeni wllh bana son duka.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke murya asarƙe yace " Naji sake min riga ".
Kafin ta bashi amsa Nura ya kwashe da dariya yace dama kin buɗe idanu don Ahmad gashi can zaune yana kwasan daɗi.
Har ynz taƙi buɗe idanu don ita bata yarda da Nura ba saida taji ya hankaɗata, ta faɗi tim kan carpet sannan ta ware manyan idanunta cike da tsoro take dubansa kamar bashi ya tureta ba abinci kawai yake ci suna hira da Nura.
A ɗarɗar ta wuce ɗakin Baba talatu ta kwanta cikin barcin take jiyo ihu kaɗan2 don ita batada nauyin barci ta kasa komawa barcin ihun ya isheta gashi taƙi tashi daga kwancen ga faɗuwar gaba dake damunta kwata2 barcin bai mata daɗi ba.Hafsa, Nazifa tagani sun shigo aguje kafin ma su mata magana ta diro daga gadon amma takasa magana sai ido data tsaresu dariya suka kwashe " uwar tsoro ga Mamuh tazo da Hisham"
Mtsssw ta harari Nazifa '' Kefa baki iya ƙarya ba don Allah kubari nayi barcina duk kun isheni da ihu kun hana mutum hutawa wll..... da gudu Hisham ƙaninta ya rungumeta.
Laah ashe da gsk ne muje naga Mamuh da Abba ku kazo?.
Aa mu biyu muka zo ya bata amsa.Cinyar Mamanta ta hau tana dariya kai Mamuh ko ki gayamin meyasa bakizo dasu Siyama ba tana wani marairaicewa wai ita adole me uwa.
Kedai har ynz da saura bako gaisuwa kin wani hayemin cinya goɗai2 dake .
Ta turo baki gaba, toh mamuh ina yini kunzo lfy ya hanya ina Abbana dasu Siyama da Affiyah dafatan kuna lfy?.
Baki buɗe Mamuh ke binta da kallo, Inna tace ke kuwa anji kewarku ai sai a amsawa Jiddatuna koh kuwa?.
Ɗan murmushi Mamuh tayi kafin ya islamiyah kina zuwa kuwa don nasan halinki.
" Wllh ki tmbyi Hafsa tare muke zuwa koh Inna?.Inna tace, '' Ni shaida ce kullum kuwa bakya fashi "
Baba talatu ta kwashe da dariya suna jima suna hira sai ga Abba Sunusi dasu Ahmad sun dawo masallaci sunje sallar la'asar tana ganinsu ta wuce ɗaki gunsu Hafsa.
Bayan sun gaisa da Abba yake tmbyrta da fatan kin baro su Siyama da Safiyyah lfy?.
Suna lfy Abba.Alhmdllh in kin gama gaisawa da 'ya'yan naki ki sameni ɗaki duk su inna suka bi bayanshi Fariis da Ahmad suka gaishe ta tana murnar ganin ɗan 'yar uwarta.
Ahmad yace Mamuh irin wannan bazata haka koh ki faɗa mana zakizo anya lfy?
Kallon sa tayi tana hararanshi ya gane me take nufi ba shiri yabar wurin yana dariya yasan halin Mamuh bata wani sakewa dashi kasancewarsa ɗan fari.
Masha Allah Fariis da ahanya na ganka bazan ganeka ba ka girma tubarkallah, Mamuh ke maganar.Kanshi aduƙe yace insha Allah in nasami lokacin zan rinƙa zuwa.
" Allah ya nuna mana "
Ameen ya faɗa a laɓɓarsa tare da ɗago kai daidai lokacin Jiddah tazo kiran Mamuh shi ya fara janye idanunsa.
Abba yace kizo yana ɗakinshi ta juya zata wuce Mamuh ta kirata " ungo kai min jakata ɗaki.Toh, ta amshi jakar.
Suna tafe Mamuh na jansa da hira sai sunne kai yake kamar wata surukarsa kunyarta yake ji sosai sunyi matuƙar kama da Umminsa da Nura suka haɗu suka wuce ɗakinsu yana zuwa ya kwanta don ya gaji gashi yana son zuwa gun abokinsa amma Abba Sunusi yace ya tsaya akwai maganar daza suyi mai mahimmanci.
Yaya Abba wata magana muhimmiya nazo da ita amma bansan ya zaku ɗauketa ba wannan shine dalilin da yasa nakasa hakuri har saida na kiraka jiya da dare kuma nace maimuna tazo yau don a dubi maganar ta fuskar fahimta ta ƙarashe maganar tana duban Abba Sunusi.
Abba yace " Bissimillah muna jinki, faɗa mana meke tafe dake ?".
Gyara zama tayi sannan tace ina son ayi maganar agaban Fariis.
Baba talatu tace toh can ta hango su Jiddah dagani fita zasu yi da alama abu take nema don sai dube2 take yawwa Jiddah kirawo Yayanki a ɗaki.
Ya Ahmad fa sun fita da Uncle Nura basu daɗe bama.
Fariis ake nufi Mamuh tace ba tare da ta kalleta ba.A hankali ta buɗe ƙofar don ita tsoro yake bata tunda ya hankaɗata ga hannun ciwo yake hankali kwance yake barcinsa kan cushion saida ta ƙare masa kallo azuciyarta tace ashe kyakkyawa ne saidai sam bakada fara'a bata san a fili ta furta ba.
Idonsa ya buɗe yana binta da harara bata san lokacin data kai bakin ƙofa ba bata zaci maganar ta fito fili ba da ƙarfi tace Baba tace kazo bata jira amsarshi ba don tasan ba lallai ya bata ba.Daga bakin ƙofar tace Baba gashinan zuwa, inna tace toh shigo mana koh fita zakuyi ne?.
Eh amma ni bazanje ba takalmin Hisham nake dubawa zai rakasu hafsa ne.Zoki zauna tunda kinga takalmin koh?.
Eh, bata kawo komai ba ta zauna da sallamarsa ya shigo ya ƙara gaida su Abba ya nemi gefen inna ya zauna yana nazarin wace magana ce haka.
Muryar Abba yaji yana cewa toh muna jinki.
A nutse ta juyo tana fuskantar Fariis sannan tace jiya Fariis yazo min da maganar yana son a sama mashi wacce zata rinƙa dafa masa abinci da gyare2n ɗaki shine nace mezai hana yayi aure tunda ya mallaki hankalin kansa tayi maganar tana jiran taji me Abba Sunusi zaice amma taji shiru.
Fariis shiru yayi yana jin Inna shi yama manta sunyi maganar jiya, Jiddah dake kusa da Mamuh tana danna waya ba tama san me suke cewa ba don hotunan ƙannenta take kallo.
Inna ta cigaba da cewa nayi tunani amma bansan ta wani siga zaku ɗauka ba.....
Abba ya katseta kwana2r ya isa haka zainabu kina ɓata lokacin mutane ina da abubuwa masu yawa na ajiye don na saurareki don haka faɗi koma mene ne da izinin Allah zamu fuskanceta duk yadda tazo komu karɓeta akasin haka.
Baba talatu tace gsky ne malam, ita dai mamuh bata ce komai ba.
Abba ina son haɗa FARIIS da JIDDAH Aure..............................
Tofah ku biyoni don jin yadda zata kaya......