✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).When we stop to compete with others and starts to be unique on our own to grow strong individually to join forces with those we copied before as an eternal friend and partner.
1⃣9⃣MONDAY kamar yadda ya saba da wuri ya gama shiryawa, shadda ce blue mai tsadan gaske sanye ajikinsa da hular zanna bukhar itama blue kayan sun haska fresh skin ɗinsa, kaitsaye d'akinta ya nufa don sauri yake ya ajiyeta school d'in da zata fara zuwa yau.
Bai ganta ad'akin ba amma saukar ruwan da yaji da kuma k'amshin sabulu ya tabbatar masa wanka take, k'ofar ya rufe ya zauna agefen gadon yana duba agogon hannunsa, ta daɗe kafin tafito d'aure da towel azabure haɗe da waro daradaran idonta ta juya zata koma ya tashi da sauri ya damk'o towel d'in dake ɗaure ajikinta ihu ta tsala tare da k'ank'ame towel d'in wanda kad'an ya rage ya cire mata shi durƙushewa tayi awajen ta cusa kanta atsakanin cinyoyinta tana hawaye murmushin gefen baki yayi sannan ya sakar mata towel d'in yace " Five minutes na baki ki sameni awaje ".
Tana kuka tana shiryawa sosai abinda ya bata haushi saida ta b'ata sama da awa guda sannan tafito, tun daga nesa ya k'ura mata idanu tafiya take tamkar mai tausayin k'asa riga da siket ne ajikinta da k'aramin mayafi blue kalar atampar idonsa ya d'auke ya kunna motar, a hankali tasa hannu zata bud'e back seat muryarsa ta doki kunnenta Ni drivern kine? ya kafeta da idanunsa masu matuk'ar haske.
Badon taso ba ta buɗe gaban motar tashiga, wani irin fisgar motar yayi saida ta riƙe ƙofar motar, suna isa makarantar ya fito itama tafito ya kulle motar yana gaba tana binsa abaya sai kallon 'yan makarantar take kowa harkar gabansa yake ganin ya shiga wani office itama tashiga.
Hannu ya mik'awa mutumin dake zaune idonsa sanye da glass yayi suka gaisa, mutumin ya juyo ya kalleta yace you can have a seat madam, ya nuna mata kujerar dake gefen Fariis saida ta kalleshi taga baya kallonta kafin ta jawo kujerar ta zauna ta gaida mutumin.
Bayan sun gama maganganun da zasuyi da harshen turanci Mr Abu Daniel yayi murmushi ya mik'a ma Fariis hannu yace You are welcome Barrister.
Ɗan murmusawa yayi yace Thank you, Daidai kunnenta ya matso saida ta lumshe idanu tsabar dad'in kamshin jikinsa in a low voice ya rad'a mata you know what brings you here so be careful ya ajiye mata kud'i kan ciyarta ya fice.
Ta kusan minti goma sha biyar a office d'in tana cika forms da kuma signing sannan ya miƙa mata wasu textbook guda hud'u da time table, Mr Abu Denial dakansa yayi directing d'inta zuwa department ya had'ata da 'yarsa Ruth inda suke zaune itada ƙawayenta sun haɗa group ko ta kansu batabi ba ta samu seat nesa dasu ta zauna.
Lecture'n awa ɗaya sukayi aka fara watsewa ganin haka itama ta d'auki textbook d'inta tafito waje daidai wani umbrella tree ta zauna tana k'arewa makarantar kallo kusan duk an watse sai 'yan tsurarru hawaye taji ya ciko mata idanu batasan kozai dawo ya d'auketa ba gashi ko sunan unguwar bata sani ba ji tayi an dafata ta baya da sauri ta juyo tana k'ok'arin maida hawayen.
Wata kyakkyawar budurwa ce fara tas tayi murmushi tare da zama kusa da Jiddah tace suna na Salma Uba Jankaro ni 'yar Minna ce ina zama da Uncle d'ina anan wuse zone1 naga lokacin da Mr Deny ya kawoki ina fatan zamuyi zumunci.