✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍.
*STORY*
&
*WRITING*
*BY*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).
0️⃣6⃣Sanye yake cikin shadda baƙa tasha aiki mai gajeran hannu kayan sun masa kyau idanun sa lumshe kamar mai barci jin alamar an bude ƙofa iska na kaɗowa ɗakin yasashi saurin buɗe idanu, a hankali ta ƙaraso ta tsaya daga gefen kujerar tana kallon sa duk azatonta wannan baƙon data watsawa miya ya wuce jin muryarsa tayi alamun wanda ya tashi daga barci yace,,,,
Lfy?, ya tmbyeta ganin ta tsareshi da idanu.
Saida ta wani taɓe baki tace nazo gun Yayana ne.Kulle idanunsa yayi tamkar baisan wa take tmby ba, jin ta soma gajiya da tsayuwa ne ta banko mai ƙofar da ƙarfi..
Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi ya zura takalmi ya biyo bayanta.
Wai Inna waye wanda yazo shekaran jiyannan?.
Inna ta gane sarai wa take amma sai cewa tayi wa kenan?.Kai inna wanda ynz naje ɗakin ya Ahmad na ganshi kwance.
Au FARIIS ne baki sani ba?.
Tana ɗaura ɗan kwali tace nikam bansan wani Fariis ba wllh.
Toh ɗan yayar maman kice takwarata mai rasuwa shine baki sani ba?.
Oh na kanji Abba Sunusi da Mamuh na yawan hiranshi yaje karatu koh.Yo ai tun kan a haifeki yake acan.
Amma Inna ya fiye haɗa fus.....
Sallamar sa ce ta katse mata maganar tana juyowa suka haɗa ido ba shiri ta fita tana cewa Inna bari na dubo Hafsa ko an gama kitson.Bayan ya gaida Inna yace tsarabar da na kawo yana mota na manta tun rannan.
Toh Allah yayi Albarka.
Ya amsa da 'Amin'.Bari Hafsa su dawo saisu nemo almajiri ya shigo dasu wannan magananniyar tmbyna take wai batasan kaba.
Kallon Inna yayi yace Hafsa?.
'' Ah'ah JIDDAH ".
Ko da baisan sunanta ba yasan ƴar shagwaɓan nan ce nima bansanta ba ya faɗa atakaice.
Haɓa ta riƙe ynz kaima bakasan taba ƴar gwoggon kace Mamuh ta jigawa fa.
Alamar ya gaji da hirar yace Oooh.
Umarun yafiya kulle baya son Mamuh na shiga jama'a hatta fa in zatazo gida bayaso mutum ne mai tsauri da ƙyar ya yarda da zaman Jiddah nan lbr ta rinƙa bashi amsarshi bai wuce eh, ayyah iya maganarsa kenan don shi mutum ne wanda magana ke masa wuya gashi Ahmad tun safe ya tafi shagonsa na ɗinki.
Hafsa ce ta dawo daga kitso ta gaisheshi duk da sun gaisa da safe data kai masu abinci.
Lfy kawai yace mata ya cigaba da danne2 awayarsa.
Ina Jiddah take? Yaya Sunusi jirana fa yake Allah zanyi tafiyata na barku cewar inna tana ɗaukar mayafinta asaman gado.
Tana waje cewa tayi na kiraki mutafi Hafsa ta bata amsa.
Yawwa ɗan dubo almajiri kinji, toh Hafsa tace ta fito nemo almajiri.Fariis dake zaune yana jinsu shima ya miƙe tsaye yace muje na kaiku.
Na zata fita zakayi ai?.
Ina son naje gidan abokina can layin gidan sarki, suna tafe suna hira sai ga hafsa da almajiri boot ya buɗe suka shiga kwashe buhun abincin su shinkafa, wake, taliya, manja, semolina da kuma tsarabar kayan marmari irinsu gwanda lemo da aka bashi jiya dasu kaje ziyara.
Inna taji daɗi sosai nan ya barsu suna shiga da kayan, shi kuma ya zauna cikin mota haɗe da ciro wayarsa ya dannawa abokinsa kira.
Tunda ya fara waya ta zuba mashi manyan idanunta ko ƙiftawa batayi maganarshi hankali kwance da nutsuwa yake fitar da kalma ɗaya bayan ɗaya sai murmushin da yake mai kayatarwa.
Yana cikin magana a wayar ya ɗago yana kallon ƙofar windown motarshi kawai take kallo saida yaja dogon tsaki tare da watsa mata bazan kallo aikam da sauri ta dawo cikin hayyacinta bata tsaya ganin kallon da yake mata ba ta bar wurin da sauri..
Tunda ga nesa ya hango su shi sai ynz ma ya kalleta sosai hafsa tafita tsayi doguwar atampa ce kalar purple mai ratsin ja sanye ajikinta da mayafi ƙarami shima purple babu kwalliya fuskarta amma tayi kyau.
Da sauri ya ɗauke ido ganin sunzo dab da motar, ya gyara zaman hularsa ta madubi.
Yi hakuri mun barka zaune tun ɗazu cewar Inna tana zama gaba.
Babu komai ya faɗa yana tada motar, har suka isa babu mai magana cikin su rufe motar yayi sannan yabi bayansu.
A babban falo ya tarar da mutan gidan an shimfiɗa ƙaton carpet anata gaggaisawa ga kulolin abinci agefe har ƙasa ya gaishesu shima ya zauna can nesa yana sana'arsa ta danna waya.
Dattijon arziƙi da kamala Abba Sunusi ya fito riƙeda casbaha a hannun sa ya samu kujera ya zauna yana cewa kaga Fariis auta na Abuu Allah ya jikanta da rahma duk suka amsa da amin yayin da wasu ke sharar hawaye.
Jiki asanyaye ya gaida kakan nashi wanda ya haifi Umminsa sai da aka ɗan taɓa wasa da barkwanci sannan akace su Hafsa su raba abinci.
Bayan Hafsa da Nazifa sun zubawa kowa Jiddah ta ɗauki plate ta zuba nata ta koma kusa da Inna sai ga Ahmad da Nura sun shigo,,,,
Yawwa nazo adaidai mikomin nan ki zuba wani yunwa nakeji tun ashago ya faɗi haka yayin daya zauna kusa da Fariis dake magana da Nura (k'anin Mamuh shine autan su).Cokali ta ɗauka zata fara ci Ahmad yace bakiji me nace ba bani ki zuba wani ya wurga mata harara.
Fuska ahaɗe ta ɗago tana kallonshi wai dama dani kake?.
A harzuƙe yayo gun ta, su Abba sunusi dake can suna tattaunawa hankalinsu yayi nisa gaba d'aya hankalinsu ya dawo gun Ahmad dake shhirin dukanta.
Karka soma taɓata kaji nagaya maka Baba ce mai wannan maganar, Inna tace in dai faɗan sune kwa gaji da gani ita rashin kunya shikuma bashi da hakuri.
Suna mashi magana bai masan suna yiba tana ganin yayo gunta ta kwasa aguje bai ankaraba sai ji kawai yayi anshakeshi ta baya duk ta ruɗe ta cukwikuye masa riga................