✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).
0️⃣4⃣Engineer Bello jibo matansa biyu Hjy Balkisu itace uwargida, yana sonta sosai bayan sunyi aure kusan shekaru biyar basu samu haihuwa ba ya yanke shawarar ƙara aure don shi mutum ne mai son ƴaƴa kasancewar sa tilo gun mahaifiyarsa sai ƴan uba da yake dasu.
tunda daga lokacin Hjy Balkisu ta rinƙa shige2 bata wajen wannan malamin bata wajen waccen lamarin Allah sai shi haka ya fasa ƙara auren suka cigaba da zaman su hakanan abin dai gaba yake har shekaru takwas.
Ba tare da sanin ta ba ya shirya ya tafi kano ya faɗawa Inna duk abinda ke faruwa duk da tasani babu yadda zatayi shysa ta fawwala wa Allah komi har ya karkato da hankalin yaronta gida, ba'a ɗau wani lokaci ba ta yanke shawarar haɗashi da ƴar wanta Zainab, babu b'ata lokaci aka sanya aure wata biyu soyayyah sosai Zainab da Bello suke gudanarwa wanda Balkisu bata da lbr.
A kano akayi komi aka shirya kai amarya gidan mijinta nan tashin hankali ƙarara ya bayyana fuskar Bello saida Zainab ta rinƙa kwantar mashi da hankali saboda ya gaya mata komai game da Balkisu, ranar da suka isa gidan sai addu'oi kawai Zainab take Allah ya kareta daga dukkan sharrin dake cikin wannan gida.
Tun daga bakin gate suke ta jin guɗa ba shiri suka fito ita da aminiyarta sadau tozali da amarya an lulluɓeta da mayafi ga muƙarrabanta ana ta guɗa hankalinta ya tashi sosai kar dai zatona sadau ya zama gsky ta faɗa tana kallon ƴan kai amarya na ƙarasowa garesu.
Sadau tace kedai bari aminiyata bata gama tsurewa ba saida suka iso gareta wai da sunan amana, ƴar uwa kuma abokiyar zama suka kawo mata ta hana kowa shiga bala'i sosai ta rinƙa masu kamar zata haukace, su kuma dasu kaga haka suka kira Bello tas suka zayyane masa yanda uwargida tayi masu daman shi bayan an d'aura aure wani aiki ya taso masa ya tafi sokoto.
Sai safa da marwa take takasa samun nutsuwa shin me zatawa Bello ne koh kuwa waccan jakar wai ita amarya, tun kafin ya kirata, ta rigashi ta inda take shiga batanan take fita ba har ɗakin Zainab saida tabita daga ita har wanda suka kawota saida balkisu da sadau suka zagesu ta uwa ta uba daman ita zainab mai haƙuri ce sai kuka kawai take da tunanin halin da zata tsinci kanta ciki saida ƴan kano sukai kwana uku sannan suka tafi lokacin Bello ya dawo daga tfyr hakanan suka barta cike da kewa.
Bayan wani lokaci da daɗi babu haka suke zaune itada balkisu.
Kwatsam watarana Zainab ta samu ciki, murna gun Eng Bello babu dama ƴan uwa da abokan arziƙi ya rinƙa buga waya yana faɗa masu baƙaramin farinciki suka tayashi ba.Karma Inna taji lbr tama rasa ina zatasa kanta tsabar murna, koda ya kaiwa balkisu lbr baƙinciki kamar ya karta duk wani kuɗaɗenta gun malamai suke ƙarewa don kawai azubar da cikin amma inaa cikin yaƙi zubewa daga ƙarshe ta hanyar masu aikin Zainab ta haɗa baki ana mata asiri ta abinci kona sha, baƙaramin wahala Zainab tasha ba, kullum babu lfy saida Inna ta haɗa da roƙon Allahu sannan ta samu lfy.
Har cikin ya girma lokacin haihuwa yazo cikin hukuncin Allah ta haihu lfy ta haifo santalelen ɗanta kyakkyawa mai kama da daddynshi murna gun dangi babu dama yayin da uwargida kamar ta suma tsabar baƙinciki ranar suna baƙaramin kuɗaɗe Eng Bello ya kashe ba shagali sosai akayi kayan sawan jinjiri kamar a boutique yaro yaci suna FARIIS, bayan suna da kwana biyu aka wuce da ita gida wankan jego.
Sai da tayi wata uku masu lfy daƙyar ta yadda ta koma haka suka cigaba da rayuwa itada yaronta Fariis da mijin ta mai kaunarta, Fariis shi kaɗai yayi rayuwarsa tunda aka haifeshi momy bata taɓa ɗaukarsa ba saboda ƙiyayyar da take masu shida uwarshi.
Fariis nada shekara tara mahaifiyarsa ta kwanta jinyar kusan wata guda har dai Allah ya amsa ranta yasha kuka don daita kaɗai yasaba rayuwa tunda daddy matafiyi ne kusan saida aka had'a da addua ko magana baya yi saida aka rinka addu'o'i, Momy ji take kamar ta kwanta ƙasa taita mulmula don abin nema ya samu dangi sunsha kuka kasancewar Zainab mutuniyar kirki babu ruwanta Alkhairin Allah ya tabbata gareta amin.
Dagin mahaifiyarsa sunso su riƙeshi amma Daddy yace sam bai yarda ba, abar mashi Fariis in yana ganinsa tamkar mahaifiyarsa ke tare dashi.
Haka yataso dagashi sai mahaifinshi tun bayan rasuwar Umminsa ya koma zama da Daddy apart ɗin Momy babu ruwanta dashi Daddy ke mai komi hatta abinci sai daddy ya zage Balkisu sannan take barinshi yaci, ganin yadda momy batason Fariis ya yanke shawarar kaishi boarding ƙasar waje, aikam Momy ta tubure ala dole babu inda zashi gashi har lokacin ko ɓari bata taɓayi ba, saida Daddy ya gama komai ya ɗaukeshi suka tafi kano ya masu sallama daga can suka wuce Gabon.
Tunda ya tafi saida ya gama secondary sannan ya dawo gida Momy bata taɓa zuwa makarantar ba amma dangin Umminsa dana Daddy suna zuwa, ba irin Daddy da baya daɗewa baije ba.
Koda ya dawo ya tarar Momy ta haifi jaririyarta Nawwal babu canji ko kaɗan daga halayyar momy, a kano yayi hutunsa saida result ɗinsu ya fito sannan ya koma gida inda ya fara shirye2n tafiya jami'a, a Gabon yayi karatunsa kaf inda ya karanci Law.
Fariis ya kasance shiru2 bashi da wani abokin hira sai daddynshi da kuma abokinsa na makaranta shi mutum ne mai zuciya ko kad'an baya son raini idan ka zauna dashi zaka fahimci bashida matsala ga haƙuri da juriya suke ƙara masa kwarJINI.
Kyakkyawa ne shi ba fari ba wankan tarwad'a ne yana da tsayi sosai fuskarsa zagaye take da saje ga idanu dara2 da dogon hanci ziir yana da pink lip's ga yalwatacciyar gashi ko'ina ajikinshi yana da kyau mai matuƙar ɗaukar hankali.Hauwa'u Umar ƴace ga Maimuna ƙanwar Ummin Fariis data rasu, su biyar maman su ta haifa ya Ahmad shine babba sai ita Hauwa suna kiranta da Jiddah sai Siyama, Saffiyah da Hisham.
Zamanta gun Inna ya samo asali ne tunda suka zo hutu kano da yake ta gama makaranta shine tace bazata koma ba nan zatayi karatunta saboda admission ma ake shirin nema mata a BUK idan result ɗinsu ya fito.
Jiddah ba fara bace kuma ba baƙa ba tana da manyan idanu masu haske tamkar anɗiga zaiba ga cikan gashin gira dana kai hancinta dai2 da ƙaramin bakinta mace ce mai alkunya batason fita sam shiyasa basa shiri da ya Ahmad don idan akace za'aje unguwa da ita sai ranka ya ɓaci kota ƙi zuwa ko taɓata maku lokaci ko zaka mutu idan ka aiketa bazata ba in ba dai wajen yana da nisa ba shine fa zata je.
Duk wani aikace2n gidan ita ke yinshi akwai ta da tsafta ga hkr bata da hayaniya sam gata dai shekarunta sha takwas tana da hankali da nutsuwa ga tsoron masifa da mugun son barci lolx.Daman shi Ahmad gun Inna ya taso tun yana ƙarami Hafsa kuwa jikar tace ta wajen ƴaƴan kishiya.
Wannan kenan.............................