BARRISTER FARIIS

4 0 0
                                    


   ✨ ✨✨✨✨✨
        *BARRISTER FARIIS*
     ✨✨✨✨✨
 

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).

          *P.W.A*✍️

*STORY*

*&*

*WRITING*

          
  UMMUH ABUU SADEEQ
          (Cuty pie).

        
      0️⃣8⃣

         
A matuƙar razane Fariis ya ɗago idanu yana bin Inna da kallo shin gsky ne abinda kunnuwansa suka jiye masa wannan wace irin magana ce haka.
   
  Tim su kaga wayar hannunta ya tarwatse jin maganar tayi tamkar ganga akwakwalwarta cikin kuka tace Inna me kike faɗane ni jiddah'n kike nufi......

     Mamuh ce ta wanka mata maruka masu lfy ba shiri ta faɗi ƙasa tana kuka mai ban tausayi.

   Abba, Baba talatu babu wanda yayi yunƙurin hana ta kukan kuka take bilhaƙƙi Baba talatu ce tashiga rarrashinta kiyi shiru jiddah ki daina kuka kinji.

    Hawaye na zuba idanunta tace Baba don Allah kice inna ta bar maganar nan wll.....

   Mamuh zata kuma dukanta Abba yace ƙyaleta maimuna ya maida kallonsa ga inna, naji duk abinda kikace amma zanyi tmby ɗaya zuwa biyu juyar da kanshi ga fariis yayi wanda yayi shiru yana jin duk abinda ke faruwa saidai sam hankalinshi ba'a kwance yake ba.

  " Fariis kaji duk abinda inna ta faɗa shin duk girman gidanku babu wanda zai iya dafa abinci ya baka anya an maka adalci kuwa? ".

  " Ba tare da ya ɗago ba yace Abba tunda na dawo saidai naje restaurant naci abinci don Momy tayi tfy Daddy ma baya nan babu kowa gidan wannan shine dalilin da yasa nace inna ta nemo min 'yar aiki muryarsa a raunane ya ƙarashe maganar karansa na farko kenan daya taɓa yiwa babba ƙarya a rayuwarsa"
 
Neman 'yar aiki daban aure ma haka, kamar yadda yake so ayi mar cigiya kafin ya tafi wannan ne gskyr zance Abba ya fad'a.
  
Jiddah wani sanyi taji a ranta da Abba yace hakan,,

Don Allah yaya ka yarda da abinda nazo dashi, ku duba halin da nake ciki, Bello kaɗai na haifa matarsa na neman rabani dashi Abba nasan ba kasan wace ce Balkisu ba, nan ta faɗa mashi wasu halayen Momy amma baice komi ba yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa Bello ya kai shi karatu nesa kenan, don Allah Abba ka tausayamin a haɗa auren nan shine cikar burina na alkhairi ga marigayiya da kuka ta ƙarashe maganar.

Zaka auri JIDDAH...... yaji Abba ya tmbyshi.

Da sauri ya ɗago yana kallon jiddah dake kuka kwance jikin baba talatu maganar tazo masa a bazata tayaya ma Abba zai masa irin wannan tmbyr kansa asunkuye yace duk abinda kuka zaɓamin nasan alkhairi ne Abba.

    Mamuh ce tayi saurin kallon Fariis tace Abb.., hannu ya ɗaga mata banason jin komai jikinta asanyaye da za'a bata dama da tayi magana amma hakan bazata samu ba tarbiyyan gidan ne in babba na magana babu wanda keyi har sai an bashi dama.

  Inna wani daɗi taji, Abba yace Allah ya maku albarka Baba talatu ma taji daɗi sosai amma banda mamuh dake ta saƙa da warwara azuciyarta.

    Ameen inna da Baba suka amsa fuskokinsu cike da annashuwa kuka mai tsuma zuciya jiddah keyi koh sautin kukan ma bakaji sai shesheƙa, a hankali Abba ke bata hakuri sai ma ƙara ƙarfin kukan take saida Baba talatu ta zazzageta sannan ta miƙe tabar ɗakin tana kuka.
  
    Da idanu duk suka bita banda fariis da kema kanshi faɗa meye dalilinsa na amincewa bayan yarinyar bata mishi ba tun kallon farko da yayi mata sam a tsarinshi baya da niyyan aure ynz ko aikin kansa bashi dashi yaushe2 ma ya kammala makarantar da har zaiyi aure?, anya bai tafka kuskure ba tmbyoyin da yake wa kansa kenan shin waye zai bashi amsoshin nan?.

(Nidai nace uhuuummm).

   Yaya Abba nagode Allah ya jiƙan mahaifa Allah ya ƙara mana danƙon zumunta Allah ya raya zuri'a gefen mayafinta tasa tana share hawayen dake fita idanunta.

   Ameen, baba talatu tace tana mai jin soyayyar jikokin ta Fariis Allah yamaka albarka Allah yasa yadda ka faranta mana kaina a faranta naka yabaku zaman lfy da zuri'a tagari.

    Ameen cewar Mamuh tana kallon Fariis Allah ya jiƙan yaya Zainab Allah kakai haske gareta Allah ya mata rahma ya Allah.. itama kuka ne ya kwace mata.
   
  Sosai addu'oin nan sukayi tasiri azuciyar sa ji yake kamar yai ta kuka ko zai samu sauƙi da rashin mahaifiyarsa a hankali yayi ta karanto addu'oi har ya samu nutsuwa cikin hukuncin Allahu.

   Muryar Abba suka ji yana faɗin Alhamdulilahi Allah ya tabbatar da Alkhairi Allah ya maka albarka FARIIS, ameen ya faɗa kansa ƙasa.

  Yaya ina Neman wata alfarma ta biyu?.
 
   Muna saurarenki inji Abba.

Yaya dama jibi nake son a ɗaura auren in Allah ya kaimu nan da wata guda kuma sai ta tare.

Duk da kansa asunkuye sai da yaji maganar kamar saukan mashi a ƙirjinsa wai me tsohuwar nan ke nufi ne ya tmby kansa.

   Mamuh so take taji me Abba zaice sai taga yayi murmushi irin tasu ta manya yace Fariis ka nason a ɗaura auren jibi?, duk da yasan ba lallai yak'i amincewa ba, yakama ta afita haƙƙin yaro in yana so toh in kuma yace a'a magana ta ƙare.

   Yasan kaddara ce ta kawosa kano wannan karon amma ya zaiyi da hukuncin Allah, "Allah ya kaimu abinda yace kenan".

  Ko bayan ranshi yana alfahari da Fariis kasancewarsa mai biyayyah ga iyaye bazan gaji dasa maka albarka ba Fariis tashi kaje.
  
Ƙarfin hali da juriya ne kawai tattare dashi jiki ba kwari ya miƙe su Baba da Inna suna ta sa masa Albarka.

    Baba tace Malam gobe sai a sanar dasu Suleiman su fara shirye2n tfy jigawan koh?.

Gsky ne in na fita sallar magriba zamuyi maganar dasu ko akwai wata alfarmar ne zainabu ya tmbyi Inna cikin zolaya.

   Murmushi tayi Ah'ah yaya wannan ma daka min ina matuk'ar godia gareku ngd.

   Maimunah ki sanar da umar gobe su Manu na tafe.
 
Toh Abba Allah ya sanya alkhairi.
   
   Da addu'a Abba ya rufe taron don samun albarka cikin lamarin,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

BARRISTER FARIISWhere stories live. Discover now