✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).1⃣3⃣
Ku duba kayan nan wanda Ahmad ya d'inka ne inna ta fad'a tana mik'a masu Anty Mariya, Gsky sunyi kyau Allah ya sanya alkhairi nima gatawa gudunmawar cewar Maman Ilham, Atampopi 3 da lace 2 shadda d'aya da talkalma uku, Anty Mariya ma ta had'a mata magunguna masu kyau na mata masu gyara jiki da amfani, herbal islamic medicine taje suka had'a mata, Nura ma ba'a barshi a baya ba saida ya bada tashi gudunmawar.
Baba dake zaune ta miƙe tana gyaran zaman hijabin wuyarta tace saina dawo Nura na waje yana jirana, sallama tayi masu zataje gaisuwar rasuwar yar k'awarta data rasu jiya da dare.
Sai da suka gama duba kayan tsaf Maman Ilham ta matso kusa da Inna tace Daddy kwana biyu baizo mana ba, ga Fariis shima tunda ya tafi bamu kirashi ba.
Inna tace ko auren Fariis ma baisan dashi ba don baya gari kuma na gargad'i Fariis kar ya gaya masa saidai kawai yaga ankawo masa suruka domin Bello sai Balkisu ".
" Hkr Inna zakiyi don ba banza matar nan tabarshi ba sai an had'a da rok'on ubangiji Anty Mariya ta fad'a".
" Ina da shawara in kun yarda toh? ".
Mece ce shawarar ki fad'a muji indai ta k'aruwa ce cewar inna.
" Cewa nayi mezai hana bazamu biyowa Balkisu ta duhu ba? "
Anty Mariya tace kamar ya Maman Nazifa (ilham) haka take kiran ta.
" Yawwa so nake Jiddah taje a matsayin 'yar uwarshi da tazo karatu sanin kanku ne Balkisu bata da mutumci muddin taji wannan aure kamar yadda tayi na marigayiya babu zaman lfy wannan ma hakan zata kasance kuma dole mu karɓo martabar gidan ".
Anty Mariya ta zaro idanu waje tana bin Maman Ilham da kallo.
Inna tace ah'ah ki canja wata shawarar dai, gsky kam inji Anty Mariya.
Wannan ce kawai hanyar da zamu bi don samun kwanciyar hankalinsu nasan Jiddah akwai nutsuwa don yaran nan babu wata shaƙuwa a tsakaninsu ta wannan hanyar ce zasu fahimci junansu tare da soyyayah mai tarin yawa da burgewa don Allah ku duba in shawarar bata yiba sai a samo wata.
Anty Mariya tace ai Yaya Bello'n yasan Hauwa'u hakan baza ta yuwu ba ko kuwa Inna?
Inna data yi shiru tana nazarin maganar tace bana tunanin yasanta kinga ba wani zuwa suke ba, kuma ni banason matsala kinga Jiddah yarinya ce k'arama banason abinda zaije ya dawo ana danasani.
" Inna karku damuwa fatanmu samun nasara kawai, sauran aikin ku barmin zanyi da kaina amma banason su Abba da Baba su sani tsakaninmu hud'u har da Yaya Mamuh zan sanar mata komai nasan zata amince ".
" Allah yasa mana hannu cikin ayyukan muna Alkhairi Allah ya k'ara zumunci cewar Inna "
Maman Ilham tace Amin ai yiwa kaine Allah ya basu zaman lfy.
Anty Mariya ce ta ɗauki wayarta ta kira layin Fariis, saidai yana ta ringing bai ɗaga ba, alokacin da ta kira wayarsa shikuma yana wajen Daddy da ya dawo daga tfyr da yayi, misseds call ɗinta da ya tarar shine yasa ya ɗanji kunya ta kamashi don bai kirasu ba tun bayan da suka yi waya ranar da ya dawo, ko da ya kira shiru yayi don baisan me zaice ba." Kasan kayi laifi shiyasa kayi shiru ".
" Anty ayi hkr ya gida yasu Baba? ".
" Duk muna lfy ya gida "." Lfy alhmdllh, Inna ce ta karɓi wayar tana faɗin, idonka kenan Fariis tunda kayi tfyrka ko waya ba ka kira kaji lfyr matarka ba, bayan kasan haƙƙin Allah da amanarsa na gareka gsky banji dad'in abinda kayi ba ".
" Kuyi hkr Insha Allahu sati me zuwa zanzo "
Maman Ilham itama saida ta amsa wayar tayi masa fad'a sosai, hkr ya basu sannan ya katse wayar, wayar ce ta kuma ringing murmushi yayi kafin ya ɗaga yace Magdaline, daga can tace kaga alert na kud'in dana cire koh?.
" Yes nagani, kayan sun ƙaraso ne? ".
" Eh zuwa anjima zansa akawo ma har gida, da sauri yace No basai sun kawo ba zansa a d'auko karki damu ngd, zai kashe wayar tace " Ni har ynz baka gayamin meza kayi da lefe har 2 set of boxes ba ".
" Cousins d'ina ne zasuyi aure su biyu, so never mind yana gama faɗin haka ya katse wayar, gaba d'aya shi baisan ya zaiyi ba, ga Inna ta hanasa ya gayawa daddy shi ba wani kud'i yake dashi ba, d'an kuɗaɗensa ya bawa magdaline friend d'insa da suke ordering kayan aure daga kamfani yace ta haɗa masa kayan lefe, baisan wannan wane irin aure bane ya dad'e da tabbatarwa rashin mahaifiya babban asara ce ya jima yana tunanin yadda zai b'ullo da al'amuran, nauyi kawai aka d'aura masa, ji yayi kansa na masa d'an ciwo2 baisan lokacin da barci ya saceshi ba..
JIGAWA
Jiddah tayi wani irin kyau sosai, fatarta tayi luwai2 da sheƙi, amma ta rame don kullum cikin kuka take, duk k'annenta sun tafi makaranta daga ita sai mamuh, hankali kwance take barci ji tayi an ƙanƙameta da sauri ta bud'e idanu ga mamakinta sai taga Hafsa da Nazifa aikuwa ta rungumesu tana dariya.
" Anty tace min bada ku za'azo ba ashe wasa take min ".
" Nina ce kar a fad'a maki, kin ganki kuwa me kike ci ne haka anya amaryarmu ba wani abin da kike shafawa? cewar Nazifa cike da zolaya ".
" Harara ta watsa mata tace bansani ba 'yar rainin hankali ".
Hafsa tayi dariya gsky Jiddah kinyi haske sai dai kin rame.
Harararsu tayi, tace zanje na gaida iyayena tunda ku surutu ne aikin ku ba irinki ta nuna Nazifa, tana ganin Nazifa ta biyo ta da gudu ta kwasa aguje.
Maman Hafsa tace oh ni Hassana kudai in kuka had'u bakwa rabo da shirme, Maman Ilham tace Allah dai ya shiryesu ba irin Jiddah da girma ya hau kanta, zumb'ura baki tayi don batason mgnr auren nan, bayan su Maman Ilham sun huta ne suka firfito da kayan akwatinan da Fariis yasa company suka kawo aka shiga bubbuɗewa, baƙaramin naira ya kashe ba kama daga akwatin set biyu, atampopi, shadodi, arebian gown, laces, materials, takalma, mayafai, hijabai, jakunkuna, sark'oki dadai sauransu dasu kayan cosmetic, masha Allah lefe yayi kyau, Jiddah na ganin an bud'e ta wuce d'aki ta rink'a kuka.
Haka mak'ota suka rinƙa shigowa suna kallo sai yabawa da irin tsadaddun kayan ake har dagin Abbanta sun yaba sosai washegari akayi ƙayataccen walima don Abbanta yace babu wani events da za'ayi tunda an d'aura aure.
Gefe guda Fariis yana nashi shirye2n ga batun aiki dazai fara within this week, sosai abubuwa suka cakuɗe masa da yawa.
Bashir k'anin Momy ya dawo gidan da zama sai abinda ya ga dama yake sai yawan club da kawo 'yan mata Fariis kam kome zasu yi babu ruwan shi...............