BARRISTER FARIIS

6 0 0
                                    


 
   ✨ ✨✨✨✨✨
        *BARRISTER FARIIS*
     ✨✨✨✨✨
 

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).

          *P.W.A*✍️

*STORY*

*&*

*WRITING*

          
  UMMUH ABUU SADEEQ
          (Cuty pie).
        
      1️⃣1⃣

8:30am

Zaune yake dak'in Abba yana mashi nasiha sun dad'e Abba yace Allah ya kaika lfy, ya amsa da Amin daidai lokacin Nura ya iso wajen yace tfyr kenan? "

   Eh, d'akin Baba suka k'arasa ak'asa ya zauna ya k'ara gaishesu cike da girmamawa.

" Allah ya tsare agaida su Firdousi da Nawwal cewar Baba, Inna kuma tace kayi ƙoƙari kan abinda na gaya maka d'azu Allah kaika lfy.

Baba tace bari in kirawo Jiddah, Inna itama ta mik'e tsaye tana fad'in ka gaida babanka Allah ya sauke ka lfy duk suka fita sai shi kad'ai yana danna wayarsa ".

Lokaci2 ya kalli agogo tun bakwai yake nan gashi har tara da biyar ya tashi zai fita ita kuma ta shigo watau saida ta gama b'ata masa lokaci tazo fuskarsa a had'e yake dubanta dogon rigar barci purple ce sanye ajikinta ya d'an wuce gwiwa da hula a hannu saman gado ta haye ko gaisar dashi batayi ba ta kulle idanu.

  Sosai yaji haushi yadda tayi kamar bata ganshi ba shi fa yanayi ne sabida su baba ba don yana sonta ba.

Kan madubi ya ajiye abinda ke hannun sa ya fita ba tare da yace da ita k'ala ba har mota su Abba da Ahmad, Nura, Hafsa, Nazifa suka rakashi saida suka daina ganin motar suka koma gida cike da kewa..........


1:36pm

A Abuja ta masa don bak'ara min gudu ya shatata ba horn ya danna liba ya buɗe masa gate yana washe baki tare da masa sannu da zuwa yana gama parking motar ma'aikatan gidan suka ƙaraso suna masa barka da dawowa liba ya d'auki jaka zai kai masa ciki yace ah'ah ya barshi, kasancewar yau saturday yana jiyo hayaniyar k'annansa a field can ya nufa basu ma hangeshi ba suna ta volleyball baiyi aune ba sai jin ball yayi ya daki kansa Auuuch ya fad'a dafe da goshin sa.
 
  Da Momy suka had'a idanu harara ta watsa masa Fido ce ta tafi d'auko kwallon don turn d'in tane bata gama k'arasawa ba ta saki ihu wanda ya jawo hankalinsu Baby da gudu suka rungumeshi Momy na kiransu suka yi mata banza.

  Asim ya cilla sama yana mashi wasa sai dariya yake Fido tace Yaya ina kaje ne har 6 days?, munyi kewarka sosai fa cewar nawwal dake amsar jakarsa.

Murmushi yayi yace muje na gaida momy tukun saina fad'a maku.

    Baby dake tsaye tana kallonsa tace your welcome.
  
   D'an kallon ta yayi yace thank you gaisar da Momy yake tayi banza dashi haɗe da barin wajen k'annan basuji dad'in yanda momy tayi masa ba har d'aki suka rakashi suna masa surutu.
 
" ku jira nayi wanka da sallah sai muyi hira koh?, suka amsa Yaya muma za muje  muyi sallah mu dawo.

Yana kwance ya gama gyara d'akin yana jiran su Nawwal su dawo amma shiru basu dawo ba ga yunwa yana ji amma bai son fita jin an bud'e k'ofar yasa shi kallon wajen duk azatonsa su Asim ne yana ganinta ya had'e fuska kamar bashi ba.

  Uwale ta ajiye abincin sannan suka gaisa da Fariis tana tmbyrshi ya karatu naita tmbyrka sai nawwal ke fad'amin kayi tfy sannu da hany.. bata k'arasa ba Baby ta hau zaginta.

  " Mayya zakizo ki wuce koh kuwa?, kin cika masa kunne da surutu kamar an kiraki jin muryar sa tayi yana fad'i,, kema ban kiraki ba ya nuna mata hanyar k'ofa ".

Zata zauna ya dakatar da ita karki soma zama min ad'aki tashi ki fita ganin yanayin fuskar tasa ta fita haɗe da buga masa k'ofar...
 
Har tana bigewa da k'ofa tashigo d'akin hankalin ta atashe da sauri ya tashi saboda ya fara barci yana binta da kallo lfy Fido?.

  Bata bashi amsa ba ta hau bud'e kulolin abincin alhmdllh ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya.

  Yaya ngd Allah da bakaci ba wllh momy na gani itada Anty suna zuba wani abu barcin dole ta samu shine dana fito nagansu a kitchen suna zuba abu amma bansan ko mene ne ba.

  Shiru yy yana saurarenta saida tayi shiru yace shikenan banason ki k'ara fad'awa kowa may be pepper ko maggi ta k'ara jeki karta nemeki.

  Toh amma ni hira nazo muyi fa ynz me zakaci?, Daddy ma yaje sudan da Momy kawai suke waya.

Basar da zancen yayi da faɗin Fido magana muje ki rakani eatery da murna tace shysa nayi mugun kewar bross.

  Murmushi kawai yayi yana mamakin maganganun data fad'a babu kowa falon suka fita Idi direba yakaisu don bazai iya tuk'i ba ya gaji sosai koda suka dawo d'aki yashige bayan yaci abinci ya kwanta................

Ta dad'e tana barci tana tashi tayi wanka ta shirya cikin dogon riga na material kalar shuɗi2 yaji stones cikin wanda ya Ahmad ya d'inka mata Hafsa ce tashigo itama taci kwalliya sunyi kyau su uku suka yi ankon.

  " Baki gama ba har ynz cewar Hafsa tana kallon madubi ".

  ' Na gama takalmin nan ne banason sawa gashi Anty Mariya tace shi zansa '.

  To kisa hakanan mana idonta ne ya sauka kan madubi " wannan kud'ad'en fa?, ta juyo tana kallon Jiddah.

   " Bansan na waye ba yanda kika gansu haka nima so ba ruwan ki ".

Ganin Baba yasata aje kud'in tana gyara gyale, au bazaku tfy ba sai yamma tayi koh?.

Shirya wa muke fa cewar Jiddah tana d'aukan mayafi dake saman gado Nazifa ce ta shigo itama tayi kyau turare zata fesa ta hangi kud'in hannu tasa tana jujjuyawa kai Baba cewa fa nayi kiban dari biyu insa kati kikace min baki dashi wannan na waye toh?.

Amsan kud'in Baba tayi inajin Mariya ce ta ajesu don ita tafito d'azu, an tmbyi Anty Mariya ko nata ne tace ah'ah su Ahmad duk sunce banasu bane sai can Nura yace ina ganin mijinta ya ajiye.

   Salati Baba tayi tace dama da nace kije kuyi sallama ashe baki jeba Allah dai ya shiryeki.

  Mamuh dake yiwa hisham wanka tace ba inda zaki Nazifa ku tafi abinku zata yi kuka Anty Mariya tace yaya ki barta don Allah kinga Maman Nazifa (Ilham) bazata ji dad'i ba bayan tace suzo kinji.

  Carab inna ta amshe da fad'in hafsa ku tafi na yarje maku.

  Ahmad ya harare ta dalla muje kona fasa wllh, komai zakace tunda zaka kaimu an wuce wajen Nazifa dake kusa da ita tace ki rufa mana asiri nidai babu ruwana yana ajiyesu ko shiga beyi ba yace sa'a d'aya zaku ci saboda Hafsa zan dawo da saidai ku hawo na haya ya barsu nan tsaye.

Taɓe baki Jiddah tayi tace Allah da ya Ahmad kad'ai ke da mota duk duniyar nan da an shiga uku da wulak'anci Nazifa ta kwashe da dariya kedai bari ya Ahmad akwai aji hafsa dake jinsu ta hararesu suka k'arasa ciki..............


BARRISTER FARIISWhere stories live. Discover now