✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).
2⃣9⃣ & 3⃣0⃣Tunda suka yi sallahr asubahi Anty Mariya ta hanata komawa barci sai da tasa mata lalle a 'yan yatsunta sannan tayi mata kitso k'anana2, duk da Jiddah bata so, bayan ta wanke lallen Anty Mariya tasa ta gaba sukaje kitchen inda tabarta ta had'a masu breakfast ita kuma ta tafi shiryawa.
Duk aikin da take fuskarta a had'e don bak'ara min takurata Anty Mariya tayi ba, tana cikin feraye arish aka turo k'ofar kitchen d'in, wasu mata biyu ne da ganinsu yare ne, ta gane d'ayar wacce ta kawo masu abinci jiya ce, cikin girmamawa suka k'araso suna gaisheta da gurbatacciyar hausar su, kasa amsa masu tayi don manya ne sosai, gaishe su tayi maimakon su amsa mata sai d'ayar ce ta amsa wuk'ar dake hannunta tana fad'in,,
' Kiyi hkr Anty wannan aikin mu ne, kasa magana tayi duk sun hana ta yin komai gefe ta tsaya tana ganin yadda suke yin komai cikin tsafta da kwarewa, ba yadda ta iya haka ta fito tabar su suna aikin '.
' Har kin gama abinda na saki, Anty Mariya ta tmbyeta tana kallonta '.
Sai da ta k'arasa shigowa d'akin tace Ah'ah masu aikin ne suka ce na bari zasuyi, kin kyauta ai kije ki shirya kafin su gama abincin ki kai masa, b'ata fuska tayi ta k'arbi kwalban turaren da Anty Mariya ke mik'a mata sannan tashige toilet d'in.
Ko da ta fito wanka Anty Mariya bata d'akin, a tsanake ta gama shirinta sannan ta fara gyara d'akin, wayar da ya bata tun ranar da ya kirata ta bud'e masa gate ta hango a k'asan gadon da alama wanda suka gyara d'akin jiya basu lura da wayar ba, saman mirror ta ajiye kana ta cigaba da aikin, cikin k'ank'anin lokaci ta gyara bedroom d'in sai kamshin burner na turaren wuta ke tashi dama ta wanke toilet tun kafin tayi wanka.
A kitchen ta tarar da Anty Mariya na jera kayan breakfast ɗin akan wani haɗaɗɗen tray mai kyau, kusa da Anty Mariya ta matsa inda ta miƙo mata trayn tana faɗin,,, ungo ki kai masa kinga ire2n wannan aikin ke ya dace ki rink'a yin su da zarar ya kawo ki gidan nan, abinda zan fad'a maki na k'arshe wllh JIDDAH ki rik'e FARIIS da kyau domin shi kyautar Allah ne agareki saboda sau da dama abinda muke so baya zama alkhairi agaremu, kinsan duk yadda auren naku ya kasance cikin k'ank'anin lokaci kuma mai wuyar mantawa, ire2n su mazaje ne na gari waɗanda kowace mace ke burin aure, kiyi amfani da hankalin ki wajen yin abinda ya dace, tana gama fad'an haka ta ajiye trayn ta fice daga kitchen d'in.
Jikin Jiddah asanyaye tabi Anty Mariya da kallo har ta fice, idonta ta janye ta maida kan trayn dake ajiye agabanta, hawaye ne yashiga sintiri a fuskarta kuka take sosai, toh mene ne laifin ta bayan sune suka buk'aci sirrin b'oye kada kowa yasan alak'arsu, ya kamata su mata uzuri duba da yadda ta amince da auransa bayan babu wata shak'uwa da soyayyah atsakanin su.
Yana daga tsaye a bakin k'ofar babban falon yaga fitowar Anty Mariya daga kitchen, sai da suka gaisa sannan shima ta masa fad'a sosai, duk abinda Anty Mariyan ta fad'a masa gsky ne zuciyarsa duk babu daɗi haka ya nufo kitchen ɗin don ya sallami masu aikin.
A bakin ƙofar kitchen ɗin ya tsaya yana kallon yadda ta kifa kai tana kuka, ba tare da yace komai ba yaja tsaki ya fice, hawaye ne ya kuma b'ille mata sai da tayi mai isarta sannan ta cire ɗan kwallin dake kanta ta goge fuskarta, abincin ta d'auka ta nufi sashensa, a hankali ta tura k'ofar d'akin kamar mai sanɗa, kishingiɗe ta sameshi ya d'aura k'afa d'aya akan centre table dake gabanshi yana latsa waya.