✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).
2⃣5⃣ & 2⃣6⃣Gidan shiru tamkar babu kowa acikin sa tun bayan kwanaki huɗu da suka wuce ya zamana babu wani mai walwala kullum suna tsammanin farkawar sa amma har yau babu wani alamun da ya nuna hakan daga gare shi, sosai Daddy da Sagir suka damu kullum cikin zullumin hakan suke, ɓ'angaren momy kuwa tun ranar da abun ya faru take cikin damuwa na rashin cin nasara sai dai bata nuna hakan ba gudun kar azargeta.
Amma takan shiga ta dubashi duk da bata t'aba had'a kalmar sauk'i agareshi ba sai dai tace Alhj har ynz bai farka ba iya abinda take cewa kenan ta k'ara gaba, yanayin yadda Momy ke nuna kiyayyarta k'ara2 yana ciwa Daddy rai amma babu wani mataki da yake ganin zai d'auka face idan ya samu sauƙi zai d'auke shi daga k'asar baki d'aya yana ganin hakan shine maslaha.
Nawwal kuwa ciwon idanu ya sanya ta gaba saboda koke2n da take kullum, don Sagir ya gargad'e su kada su nuna alamun masaniyar faruwar al'amarin, sunci kuka ita da Jiddah sosai har sai da Baby taji tausayin su, gidan dai tamkar anyi mutuwa haka ya kasance.
Yau ma kamar ko da yaushe d'akin shiru kamar babu kowa, a hankali ya fara motsa ƙafafunsa, Daddy dake zaune agefen sa tabbas ya ga lokacin da k'afar ke motsawa hamdala yayi ga ubangiji subahanu wata'ala, sannan ya bugawa Dr Aminu waya ya fad'a masa cigaban da aka samu ta b'angaren motsawar k'afafun nasa, ya masa fatan samun lfy da cewa insha Allahu zai shigo da dare don ynz akwai aikin da yake kanyi nan sukayi sallama, Sagir na shigowa Daddy ya gaya masa kuma shima ya gani da idanunsa, addu'ar su Allah ya bashi lfy da k'arfin jiki.
Ta dad'e zaune awajen ta rasa yadda za'ayi ta k'arasa shiga ciki, Daddy ta hango yana tahowa cike da girmamawa tace " Daddy barka da warhaka ".
Maimakon ya amsa mata sai ya jeho mata tmby ' ya kika zauna anan baki shiga ciki ba Hauwa'u? '.
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da 'yan yatsunta bata ce komai ba, yanayin kunyarta da nutsuwarta yana burge Daddy ' Ki k'arasa mana Sagir na ciki '.
Toh Daddy, daga bakin k'ofar ta tsaya tayi sallama Sagir ya bata izinin shigowa, bayan sun gaisa ta tmby shi ya mai jiki?.
'' Jiki alhmdllhi, ɗazu maa k'afafunsa sun fara motsawa har ynz dai bai farka ba. ".
Shiru tayi bata k'ara cewa komai ba, bata jima a d'akin ba ta fito, a bakin ƙofar fita suka had'u da Baby bata tsaya kallon hararar da take watso mata ba ta wuce.
*************************
Juya maganar yake a kwakwalwar sa tayaya zai tabbatar da hujjojin da Dr labaran ya gaya masa lallai sai ya shiryawa wannan binciken sosai gudun kar a samu matsala, har ya isa gida zuciyarsa cunkushe da tmbyoyi kala2, jiki babu kwari ya k'arasa ciki Daddy ne zaune yana waya sai Nawwal dake zaune Momy na d'iga mata eye drop a idanunta, da sallamarsa ya shiga ya nemi gefen Daddy ya zauna sannan ya k'ara gaida Momy, bayan Daddy ya gama wayar ne ya juyo yana kallon Sagir yace,,,,, Dafatan kasamu ganin sa?.
' Eh na samu ganin sa har munyi magana kuma ya sanar dani iya abinda ya sani! '.
' Ina jinka '..
Jim kad'an yayi sannan ya fara cewa '' A ranar da abin ya faru an samu b'acewar wutan lantarki da kuma na CCTV camera's wanda a lokacin an sami shigowar wasu mata biyu wanda ba'a ga fitarsu ba, kuma ba'a san su waye bah babbar matsalar rashin sanar da ma'aikatan asibitin faruwar hakan, sai daga baya aka gane matsalar ba daga nepa bane tsinke wayoyin wutan akayi, a sannan shi kuma Dr labaran ya gama night ward round ya tafi quarters d'insu Nurses suka kirashi suka sanar dashi b'acewar wutan bayan site d'in su da akwai wutan sai da ya duba ya gano tsinke wayar akayi inda ya rink'a fad'a har nazo na sanar dashi Fariis baya motsi ni kuma a lokacin na dawo daga kallon rigimar wutan da ake ne ina shiga na tarar dashi kwance babu numfashi wannan ne iya abinda ya sanar dani nima na fad'a masa abinda na ganin.