✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).
1⃣5⃣Misalin ƙarfe tara da talatin da biyar fitowarta wanka kenan taje gaban mudubi tana shafe2, ta fesa turaruka masu sanyin k'amshi ta jawo hijabi dake gefen gado ta saka duk abinda take bata da kuzari ga jikinta ciwo yake sosai, gefen Anty sadiya ta kwanta don duk sunyi barci da wuri.
Kukan ilham ne ya tashesu ashe cikinta ke ciwo da k'yar ilham ta koma barci Maman ilham zufan dake goshinta ta share duk sanyin d'akin ita zafi takeji ciwon jariri babu dad'i duk ta rud'e.
" Kinga yarinyar nan kalli yanda ta kwanta duk ta kudundune tashin ta zanyi ta tafi d'akin mijinta ai be kyautu muna kallonta ta kwana anan ba ga d'akin mijinta wllh bansan lokacin da barci ya kwashe ni ba ".
Tashinta Maman ilham tashiga yi, tashi kisa kayan barci wannan towel ɗin sai ya zame kina barci ai, jiri take ji amma haka ta daure tasa kayan da tafito mata dasu, rigarce shara2 fari tas da wondonsa dogo, kayan sun manne mata ajiki sosai kana iya gano komai na jikinta, zata kwanta Anty Mariya tace ke Ina zaki kwanta ga d'akin mijinki muje na raka ki ".
Kallon Maman ilham tayi taga ta harareta ba shiri ta sunkuyar dakai hawaye na zirara saman kumatunta, lallai yarinta na damun ki Jiddah cewar Anty Sadiya da tun ɗazu batace komai ba.
" Ku haka akeyi rarrashinta zakuyi ba wai ku tirsasata ba tashi muje Jiddah share hawayenki cewar Maman Hafsa saida tayi mata fad'a kan koke2n nan da take zai iya haddasa mata ciwon kai saida ta tabbatar Jiddah tashiga ɗakin kafin ta wuce.
Daga bakin k'ofar ta tsaya tana k'arewa d'akin kallo komai fari ne a d'akin hangoshi tayi zaune saman gado yana operating system har zata juya ta tuno maganar Maman Hafsa ba shiri ta zauna ganin jiri na neman kayar da ita, tafi minti goma sha biyar takure awajen amma ya shareta duk da yasan da shigowarta, a hankali ta fara rera kuka tana sauke ajiyar zuciya rufe system d'in yayi yana binta da kallo cikin tfyrsa ta k'asaita ya k'araso in da take rakuɓe kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita, anan tayi barci sai kusan k'arfe d'aya na dare ya dawo ɗakin, idonsa ne ya sauka kan kayan barcin dake sanye ajikinta tsaki yaja ya ɗan kawar da kansa gefe haɗe da d'aukanta cak kamar wata jaririya,,,
Cike da magagim barci ta ɗan buɗe Idonta da suka rine tana kallonsa so take ta sauka amma taga fuskar tasa da kwayar idanunsa sun canja launi zuwa ja saman gadon ya ajiyeta ya kuma fita, be jima ba ya dawo hannunsa rik'e da cup kan stool ya zauna ya jawo drawer ya ɓalli wasu pills kona menene oho yana gama sha ya d'auko blanket mai laushi haɗe da pillow ya shimfid'a ak'asa sannan ya kashe fitilar ya kwanta.Kiran sallahn farko na asubahi shi ya tasheta, da sauri ta tashi ganin baya d'akin ya sanyata ziro ƙafafunta ƙasa da sauri ta fice aɗakin, koda ta isa nata ɗakin su Anty Mariya sai shirye2n tfy suke toilet, fuskarta a ɗan haɗe ta shige toilet tayi wanka da alwal, bayan ta idar da sallah ne ta gaishesu tana shahwaɓe fuska ynz don Allah Anty tafiya zakuyi kubar ni?.
Kwarai kuwa, sai kuma kin haihu cewar Maman ilham, Anty Mariya tace ni kam nan da wata biyu zanzo kinji d'iyata ta rungume Jiddah, da kyar Anty Sadiya ta lallaɓata tayi shiru.
6:30am suka fito Jiddah mak'ale jikin Maman Hafsa tana k'ara yi mata fad'a, Ahmad ne ya danna horn da ƙarfi alamar su shigo su tafi, haka duk suka shige suna ɗaga mata hannu hawaye kawai ke fita a idanunta, Anty Sadiya ce ta kirata tace Jiddah wad'annan kwalaben dana nuna maki d'azu karkiyi wasa wajen yin amfani dasu kinji 'yar albarka, a hankali ta gyad'a kai kamar karsu tafi haka take ji ba irin ya Ahmad abokin faɗanta, tana gani motar tasu ta fice daga gidan, sabon kuka ne ya ɓille mata kamar ranta zai fita, ko kallon inda take beyi ba yaje ya rufe gate ɗin gida, kaitsaye d'akinsa ya wuce ya shirya cikin coat black and white ya fesa turare mai sanyin kamshi ya d'auki jakar laptop d'insa ya rataya ba tare da ya damu ya dubata ba yayi locking k'ofar ta waje ya shige motarsa, gidan su ya nufa ya tarar su daddy na breakfast kujera yaja ya zauna k'annensa suka gaishe shi suna taya shi murnar fara aiki babu abinda daddy keyi sai murmurshi shima murmushi yayi yace "Good morning".