BARRISTER FARIIS

11 0 0
                                    


   ✨ ✨✨✨✨✨
        *BARRISTER FARIIS*
     ✨✨✨✨✨
 

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).

          *P.W.A*✍️

*STORY*

*&*

*WRITING*

          
  UMMUH ABUU SADEEQ
          (Cuty pie).

      3⃣5⃣ & 3⃣6⃣

10:02am.

Safiyar litinin tun asubah da ya dawo daga rakiyar Daddy laptop ke gabanshi yana sake duba wasu bayanai da ya tattara akan case d'in su Jaga Adeyemi a watannin da suka gabata, wayarsa da keyn mashin d'insa ya d'auka sannan ya k'arasa inda take kwance tana barci ta had'a zufa sosai saboda zazzab'i mai zafin gaske ta kwana dashi tun jiya, kanta ya tab'a yaji zafin da sauk'i ba kamar d'azu ba, A'c ya kunna mata sannan ya gyara mata kwanciya ya fice.

Da mashin d'insa ya fita gudu kawai yake shararawa akan titi, can headquarter of police ya paker bike d'in kana ya nufi cikin office d'in Dpo Umar Dogara bayan an bashi izinin shiga.

Hannu ya mik'a masa suka gaisa sannan yaja kujera ya zauna yana fuskantar Dpo.

' Barr aiki alhmdllh, file d'in dake gabanshi ya mik'awa Fariis yace da akwai bayanai sosai aciki na zurfafa bincike akansu har ynz dai sunk'i su bani had'in kai wajen cigaba da amsa min tmbyoyi suna can ana lallasa su kafin su fad'amin '.

Murmushi Fariis yayi ya bud'e file d'in yana dubawa, sannan ya d'ago kansa yace Dpo akwai wasu tmbyoyin da nake son yi masu zan iya ganin ko da mutum d'aya ne?.

" Ah sosai ma kuwa, umurni yaba wani sergeants ya fito da mutum d'aya, duk ya jigata jikinsa afarfashe aka fito dashi, Fariis ya matsar da kujerarsa kusa dashi yana bin shi da kallo atsanake yad'an shak'a iska ya furzar ta hancinsa yace,, ka bani amsoshin duka tmbyoyin da zan maka, so ka bud'e kunnen ka da kyau in ka min k'arya ya rage naka wane ne " Tijjani Maje? ".

Cike da mamaki ya zaro idanu sai kuma ya basar yana dariya, a zafafe Fariis ya gwara masa kansa ya d'auke shi da gigitaccen mari, Dpo dake zaune ya kallon su yace BARRISTER ka bari su wahaltu zasu fad'i gsky.

Ak'ek'ashe yace iya wuya bata kisa sai da asha wahala tohm kuwa babu wanda ya isa ya tilasta ni fad'in abinda banga dama ba, a fusace Dpo yace wani sergeant ya mik'o masa wani k'arfe mai kaifi sannan yasa aka rik'e masa shi ya kama hannayensa ya datsa masa k'arfen, gaba d'aya sai da 'yantsunsa goma suka zube k'asa tuni jini ya balle masa, tsale yake yana yarfe hannayensa cikin azaba yace wllh zan fad'a,,,,

" Kai ku mayar dashi ciki ku casa min d'an iska mu zai kawowa burga zaka d'and'ana kud'arka banza mai kama da samudawa, Dpo ya fad'i haka yana juyawa kan kujerar da yake zaune, dukansa suke yana ihu sannan yace zai faɗa,,, kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace Tijjani Maje abokan juna ne shida Sir Sambo yawale tare suka kafa kungiyarsu ta saida kayan maye, sun jima basa shiri kan wasu kud'ad'e da sukayi asarar su wanda shi Sir Sambo yake zargin Tijjani da ribartansa, kasa cigaba da maganar yayi tsananin zafin da hannunsa ke masa kuka yake yana rok'on Dpo ya taimakeshi,,,,

Fariis ya kalli Dpo yace ayi masa afuwa ni zan tafi zuwa gobe zan kuma dawowa Insha Allah. 

' Shikenan Barr Allah ya kaimu '. ya mik'a ma Fariis hannu yana masa godia.


Yana shigowa d'akin ya zube kayan dake hannunsa aƙasa, sakamakon wani mugun fad'uwa da gabansa yayi lokacin da idanunsa suka sauka akanta sai juyi take a saman gadon, da sauri ya k'arasa ya tallabota zuwa jikinsa yana tab'a wuyanta sannan ya d'ogo fuskarta yana k'are mata kallo, sulalewa tayi zata kwanta da sauri ya rik'e ta yace,,, ' No tun jiya baki ci komai ba, tashi ko youghurt ne kisha ga magani ur temperature is high, ledan da zubar dasu aƙasa yaje ya ɗauko sannan ya dawo ya zauna agefen gadon ya rungumota zuwa jikinsa ya yanko dankwaleliyar namar kaza ya kai mata baki, kawar da kanta tayi ta koma ta kwanta, bai takurata ba shima ya kwanta agefenta yaja duvet ya rufesu don shi ɗin ma baya jindaɗin jikinsa kwata kwata...

BARRISTER FARIISWhere stories live. Discover now