BARRISTER FARIIS

8 0 0
                                    

   ✨ ✨✨✨✨✨
        *BARRISTER FARIIS*
     ✨✨✨✨✨
 

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).

          *P.W.A*✍️

*STORY*

*&*

*WRITING*

          
  UMMUH ABUU SADEEQ
          (Cuty pie).

        
     
   3⃣8⃣ & 3⃣9⃣ & 4⃣0⃣



☀☀☀☀☀☀☀☀☀☀☀

Sha takwas rabiyul awwal ranace ta walimar daliban da Allah yayi wa babbar baiwar haddar Alqur'an mai girma, ina d'aya daga cikin dalib'ai masu hazaƙa da kwazo duk cikin mahaddatan nine k'arami dududu banfi shek'aru goma aduniya ba, nayi nasarar lashe gasar musabak'a na manya2n littattafan addini hakan yasa makarantar Nurul Islam d'aukar babban kambu fiye da sauran makarantun.

Na amshi kyaututtuka daban2 kama daga malamai da manyan mutanen da suka halarci taron, daga b'angaren iyayena kuwa farin cikin su bazai misaltu a wannan ranar ba kyautar tasu ta musamman ne agareni duk da Ummina bata da lfy sosai sakamakon ciwon data kai wata guda tana fama dashi, wanda bansan wane irin ciwo bane saboda duk bin kwakkwafina ank'i sanar min, wannan dalilin yasa su Inna tahowa jinyarta su biyu.

An gudanar da walima cikin aminci makaranta ta bawa zakaran dafin da ya lashe gasar overall kyautar kujerar Hajj da mota sabuwa dal da kuma naira miliyan ɗaya da dubu d'ari biyar, wanda nine na lashe gasar kowa ji yake da ni abin burgewa da kuma alfahari ga iyayena martabansu ya d'aga fiye da zato, babu abinda nake sai kuka har muka dawo gida, abu kamar wasa har dare ko abinci nakasa ci saboda zazzab'i da ciwon kai daya kamani mai zafi.

Ganin zazzab'in ba sauk'i aka samun drip agida, babu daɗewa na samu nayi barci sai dai mafarkin da nayi cikin dare mara dad'i shi yayi sanadiyyar tashi na afirgice, wanda bazan iya tuna komai ba kuka kawai nake k'ank'ame da Ummina tana rarrashi da bani baki na daina kuka ranar farin ciki ne bana kuka ba tare da min nasihohi na rik'e addini sallah na kiyaye dokokin Allah, tare da kalamai masu tausasa zuciya.

Bayan taga min nasihar kamar ba dare ba haka suka zauna suna ta hira dasu Inna, ƙofar ɗakin da aka banko ne ya katse masu hirar tasu, wasu tirka tikar mazaje ne suka bayyana ciki bedroom d'in duk fuskarsu rufe da mask suna sanye da bak'ak'en kaya kowanne hannusa rik'e da manya2n bindiga sun saita kunami k'iris suke jira su saki harsashi, atsorace dukansu suke kallon 'yan fashin, hannu ogan yasa a baki alamar suyi shiru yayin da ya tako har zuwa inda nake kwance ya fisgoni saida goshina ya bugi tiles dake malale ad'akin.

Daddy ne ya fad'o cikin d'akin Momy na biye dashi abaya kasancewar ranar a d'akinta yake, aruɗe Daddy yace su fad'i duk abinda suke buk'ata amma kada su tab'a iyalinsa, dariya kawai 'yan fashin ke kyakyatawa suna tafa hannayen su, cike da izza ogan nasu yake fad'in ashe kana son iyalanka to ba wani abu muke so da yawa ba duka kud'ad'en da wannan yaron naka ya samu ayau d'in nan ka tattaro had'e da naka kadarorin ka bani su, cikin sauri Momy tace akwai wasu kud'ad'enta ad'aki ya had'a duka a basu indai bazasu tab'a kowa ba.


Saboda tsananin firgicewa Inna ta tashi aruɗe taje gabansu tana rok'on suyi hkr kada sumin komai saboda rashin imani irin na ogan yasa k'afarsa ya hamb'areta tare da murk'ushe mata k'afafu, ciwon k'afar da kika tana fama dashi wannan azzalumin shine silarsa.

Jikin Daddy na rawa ya tashi 'yan fashin na binsa abaya suka je d'akinsa ya tattaro duk wani abu nasa na kud'i ya damk'a masu kana suka dawo d'akin....... " da kyau Alhajin naira Engineer nasan bamu tab'a kaso d'aya na daga cikin arzikinka ba, so ka tsumayi ziyarar da zamu kawo maka akaro na biyu nan gaba, amma bazamu barka hakanan ba dole sai mun kashe wannan yaron...

BARRISTER FARIISWhere stories live. Discover now