✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).
1⃣6⃣Da asuba yana tashi ya ganta duk ta yaye duvet d'in daya rufa mata daga ita sai towel da rigar atampar dake jikinta sai barci take hankali kwance, toilet ya shiga yayi wanka sannan ya fito yayi sallah ya shirya cikin coat mai kyau har lokacin tana barci ya fita ya gyara gidan tsaf ya dawo ɗakin ya zauna yana saka black socks a ƙafarsa, da addu'a a bakinta ta tashi tana binsa da kallo, d'an juyowa yayi baice da ita komai ba ya rataya jakarsa saida yakai bakin k'ofa ya sake juyowa yace ya jikin?.
" Alhmdllh, ina kwana ta fad'a tana sauka daga gadon, yau ce rana ta farko da gaisuwa ta tab'a shiga tsakanin su ba tare da ya amsa mata ba ya fice, da sauri tabi bayanshi tace unguwan nan fa tsoro take bani ni dai gsky bazan iya zama ba.
Tsayawa yayi ya kafeta da fararen idanunsa masu ɗaukar hankali yana kallon ta, kasa magana tayi tsabar kwarjininsa ga kuma rikitattun idanunsa daya watsa mata su ɗan turo bak'i tayi tana hawaye dariya taso ta bashi ya gimtse yace jeki d'auko kayanki, da murna ta tafi yana ganin ta wuce ya kalli agogon hannunsa bakwae saura minti goma sha biyar parking lot ya nufa ya d'auki motarsa bayan ya wangale gate sannan ya fito yayi locking k'ofar ta waje.
Wayam babu shi a falon abin ya bata haushi ta window ta lek'a babu motarsa yunwa take ji ko tsayuwar kirki bata iyawa dinning table ta nufa don taga flask da kayan shayi kuka ta fara tana tuno gida sai abin da tayi niyya take ci gashi ynz saidai tasha abinda bataso tana hawaye tana shan shayin bayan ta gama ta mayar da akwatin data ɗauko tana so tayi barci amma takasa sai juyi take saboda tsoron da ya dabaibayeta.
Main house yaje kamar kullum tare suke yin breakfast, dama momy ba da wuri take fita aiki ba shysa bata tashi barci da wuri, suna tsaye shi dasu nawwal suna jiran fitowar Daddy daga gun Momy, motar Bashir tayi paking duk suka bishi da kallo ganin yana tangad'i kamar zai fad'i alamar tatil yake da giya, a haka ya ƙaraso ya jingina da motar.
Fido tace Uncle Bash jiya Anty Baby bata da lfy hankalin mu ya tashi muna ta neman ka mukai ta asibiti baka dawo ba har Yaya ma naje ɗakinsa bayanan ko ta tmbyshi tana kallonsa.
Fuskarsa a murtuƙe yace ku shige motar, da mugun kallo Bashir ke jifan Fariis har suka fice daga gidan, hannusa rik'e da cigarette ya fesar da hayak'in yace zanyi maganinka ya shige ciki yana tangaɗi.
Da wuri ya tashi aiki yana shirin fita Sagir na shigowa, are you off?.
" yes, a hanya saida ya tsaya ya siya fruits sannan suka cigaba da tafiya, ' were are we heading to naga ba hanyar gida ka d'auka ba koh gidan Amarya zamuje Sagir ya k'arashe maganar yana dariya ".
Ko kallonsa beyi ba ya cigaba da tuk'i saida ya kai bakin gate ya fito ya bud'e gate Sagir ya k'arasa shiga da motar shikuma ya rufe gidan, Ikon Allah abinda Sagir yace kenan suka shiga ciki yana yaba tsarin gidan.
Ganin yaki masa magana tun ɗazu yasa Sagir cewa " wai mene ne haka ina ta magana kayi shiru are you okey? ".
' Fariis dake tsane ruwan jikinsa da towel yace am alryht kaina ke ɗan min ciwo '.
" Ayya hard luck ka samu kaci abinci sai kasha magani, wai Ina Amaryar ne kar dai tana ciki kayi locking gate? ".
Shiru yayi baice komai ba har ya gama shirinsa yafita, da ido Sagir ya bishi da kallo inda sabo ya saba da halin Fariis wataran ma in baiga dama ba zakaita masa magana ya kyaleka shiyasa baya wani damuwa saboda yafi kowa sanin halin abokin nasa.
Ahankali yake Knocking k'ofar can cikin barci taji ana buga k'ofar kaɗan2 sannu ahankali ta bud'e idanu tana bin k'ofar da ake bugawa da kallo saukowa tayi ta lek'a d'an ramin ƙofar bata ganin komai cike da tsoro ta bud'e ganinsa tsaye fuskar nan tasa agimtse yasata ƙara tsoracewa muryarsa taji cikin kunnenta yana faɗin ki sameni a falo, ba tare da tayi wani dogon tunani ba taje ta ɗauko akwatin kayanta ta fito, Sagir dake zaune ya taso da sauri yace ' Amarya da kanki kawo na tayaki ' murmushi ɗauke da fuskarta tace Allah kabarshi zan iya d'auka fa, babu yanda ta iya haka ta barma Sagir akwatin suna tafe yana janta da hira.
Ƙofar bayan motar ya buɗe mata ta tashiga sannan ya ajiye mata akwatin acikin booth shikuma ya zagaya mazaunin driver ya zauna don yaga abokin nasa 'yan sarautan sun motsa, shiru tayi tana bin ko'ina da kallo yayin da Fariis ke kishingiɗe jikin seat idanunsa a lumshe.
Sagir na gama parking ya zagaya ya bud'e mata k'ofar da sauri Idi driver ya k'araso ya d'auki akwatin ita dai kallon Sagir kawai take duk atunaninta jigawa zai maidata Ina kuma ya kawota, shigewa ciki sukayi yayin da suka barshi cikin motar bashi da niyyar fita.
Shigarsu falon yayi daidai da fitowar mu Momy, a matuk'ar razane ta tsaya bakinta na rawa tace wace ce ke?, a tsorace Jiddah ta koma bayan Sagir don yanda Momy tazaro idanu ya firgitata, Daddy dake saukowa daga stairs yace sannunku da hanya.
Cike da ladabi ya sosa keya ya gaida da Daddy, itama Jiddah ta gaishe shi bayan sun gama gaisawa Daddy ya kalli Jiddah dake zaune a gefen Sagir fuskarta babu annuri yace Masha Allah ya sunanki?.
Muryarta na ɗan rawa kamar zata yi kuka tace HAUWA'U, Allah ya taimaka kisa idanu sosai kinji hauwa'u?, ahankali ta gyad'a kai tace nagode saidai kuma bata fahimci me yake nufi ba, Momy dake tsaye tana jinsu taja tsaki tare da watsa masu harara ta haye sama da sauri kamar zata tashi sama.
Baby ce suka shigo ita da Fido da alama unguwa suka je, Fido ta zagayo da kyau haɗe da tab'e baki tace Uncle Sagir wannan wace ce, d'an kallon Jiddah yayi kafin yace " Lil sis koh gaisuwa babu Anty'n kice ".
Uhuuum nikam ba Anty'na bace ta fad'a atak'aice, ko ba'a sanar da ita ba wannan 'yan uwan Fariis ne saboda ga kamanni ta gani tsakanin shi da Daddy da kuma wannan marar kunyar.
Daddy ransa ab'ace yace Firdousi karna sake jin haka ki bata hkr, tasan Daddy baya d'aukan raini murya can cikin tace Uncle Sagir kayi hkr tana gama fad'an haka tabi bayan Baby da ta wuce tun d'azu.
Girgiza kai kawai Daddy yayi ya kira Uwale yace ta kai Jiddah part d'insu Baby, jikin Jiddah asanyaye take bin Sagir har zuwa d'akin da Uwale ta kaisu, d'akin ya tsaru duk da ba wani tarkace bane acikinsa.
A nutse ya zauna kan kujerar dake fuskantar ta yace Jiddah Ina son kiyi hkr ki zauna da kowa lfy duk da ina da yak'inin hakan nasan ko ban fad'a ba kinsan gidan su Fariis ne don kinga kamanni, idan kika zauna da Fariis zaki fahimci halinsa mutum ne mai sauk'i da yiwa mutane uzuri bashi da matsala ni Sagir shak'ik'anin amininsa ne mun taso tun muna secondary, ni cikakken bakano ne kuma lauya mai zaman kansa don Allah kiyi hkr komai zai daidaita nan gaba da izinin Allah zaki kuma san dalilin yin haka munyi magana dashi zaki cigaba da karatunki ina fatan ba zaki fad'awa kowa matsayinki ba kamar yadda suka buk'ata ki tsaya a matsayin ke k'anwata ce kinji?.
' Cikin jindad'in dad'in kalaman Sagir tace Insha Allah zanyi yadda kace nagode! '.
Murmushi yayi lokacin Uwale ta shigo hannunta d'auke da k'aton tire, Sagir yace mama Uwale kullum ina son ki rink'a kawo mata abinci amana ce agareki duk da nasan kinsan da hakan, Uwale tace shikenan Allah ya maku albarka nan ya fita ya barsu ita da Uwale.
Yanzu Momy kin yarda yarinyar ta zauna damu haka nan babu dangin komai tsakaninmu da ita don kawai tana kanwar abokinsa sai ya kawo ta gidanmu, taje ta kama haya mana in bazata iya zaman hostel ba gsky Momy bana sonta.
' Ke damuwar ki kenan Baby baki san matsalolin da nake fuskanta ba sosai nake kashe kud'i bana ganin amfaninsu, ba irin wannan shegen yaron ynz fa ko gaisuwar kirki bata had'ani dashi ga matsalar shaye2n Bashir bansan ya zanyi ba kwata2? '.
" Momy ni a ganina kawai ki fawwalawa Allah komai shi zai yaye mana damuwarmu ".
' Yaushe ne addu'ar zata karb'u bayan kullum ina yi haba Baby abubuwa sun min yawa ga matsalar ki gata Bashir da wanne zanji duk ba kwajin magana ke in banda yawace2 babu abinda kika iya, wanda nake son ya lalace bai lalace ba sai nawa ya kamata na sake sabon shiri.
ALLAH yasa mudace da ALKHAIRI amma Allah mai jinƙan bayinsa ne akoda yaushe kuma a kowane lokaci buwayarsa ta yawaita kidaina faɗin haka kina iya saɓo Momy, cewar Baby tana ficewa daga ɗakin...............