✨ ✨✨✨✨✨
*BARRISTER FARIIS*
✨✨✨✨✨
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*
( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
UMMUH ABUU SADEEQ
(Cuty pie).
0️⃣2⃣Haba Balkisu ya zaki kori masu aiki?.
Cike da masifa tace sun tsufa wasu nake son ɗauka..
Ohk ai da sai ki gayamin koh?, gashi yau kwanan fariis biyu gidan nan sai dai yaje waje ya siyo abinci ai bai dace ba.
Watau daga dawowar ka har ya faɗa maka koh?.
Kwantar da murya yayi ah'ah su Nawwal ne ke faɗa min ɗazu.
Oho, ni dai bazan iya dafa abinci agidan nan ba kuma ba za'a ɗauko masu aiki ba, gwara ma kusan yadda zakuyi ta shige toilet ta barsa nan, shi mamaki yake kwata2 duk abinda Balkisu za tayi mashi baya bashi haushi sai abu ɗaya sam baya son tana ma Fariis ire2n abubuwan nan to fah anan suke samun matsala.
Jiki asaɓule ya wuce ɗakin Fariis, ya same shi zaune yana danne2 a laptop.
' Sai da ya rufe lapto ɗin sannan ya ƙara gaishe shi, Daddy ɗazu nashigo kana barci '.
Eh na ɗan runtsa ne kaci abincin kuwa?.
' Eh Daddy ya bashi amsa '.Kasan dai halin balkisu sai kayi hkr, ina fatan komai lfy?.
' Babu damuwa Daddy, amma da ina son naje kano koh zuwa gobe ne don na gama shiri '.Cikin ɓacin rai daddyn yace me zaka je yi akanon?.
Kwantar da murya yy zan je nakai ziyara ne don Allah Daddy kar kace ah'ah.
Sai da ya ɗau sakanni kafin ya bashi amsa shikenan Allah ya kaimu.
' Amiin ngd '.Nima gobe zan koma don sabida kai na dawo.
Murmushi ya sake yana mai jindaɗin kaunar da mahaifinshi ke masa, bayan fitar mahaifin ya cigaba da aikin gabansa, bashi ya sauko falon ƙasa ba sai yamma lis don zaman kaɗaici ya riga da ya saba indai har ya dawo gida.
A falon ya iske Momy da wata mata sai mace gefen su zaune suna hira, ko kallon su bai yiba balle su sa ran zai gaishe su ya fice, da ido duk suka rakashi murya ƙasa2 matar ta kalli momy " Aminiya kar dai yaron ɗan wajen kishiyar ki ne mai rasuwa?.
Hmmmm kedai bari shine.
Lallai ya girma amma yayi aure ne?.
Sadau tmbyoyin nan na miye haka kinfa san bana son yaron nan tun ba yau ba.
Ni kuwa na sani, koh gaishe mu fa beyi ba haka kuma kike zaune dashi?.
To ya zanyi Hjy Sadau yau kwanan sa biyu kenan daya dawo karatu ƙasar Gabon.
Kece ba kya neman mutane sai in an gaji a nemeki, kin manta ni wurin shekaru nawa ai da tuntuni na baki shawarar yadda zaki yi maganin shi.Gyara zama tayi sosai don jin shawarar aminiyarta wllh al'amuran ne sai ahankali ynz dai miye abun yi?.
Kaji ƴar gari suka tafa suna wata makirar dariya, yarinyar da suka zo tare ne ta kalli agogon hannunta tace mama lokaci fa na ƙurewa kinsan kuma ina jin barci ta ƙarashe maganar tana zumɓure baki.
" Ina zuwa Amal bari mu gama magana sai mu tafi kinji? ".
Toh ta bata amsa.Yawwa shawarar da zan baki akwai wani malami dake nan zaria ya iya aiki sai ki sami lokaci muje ki faɗa masa yadda kike so ayi dasu koh kuwa?.
Wllh kuwa ngd sosai ynz sai yaushe zaki tafi?.Gobe nake son tfy kinsan nagaya maki Amal ce zata fara makarantar nan university.
To shikenan sai mutafi tare goben amma yarana sai na je gida na taho da ƙanwata sabida ta zauna dasu.
Ta mike tana gyara zaman mayafinta mu zamu tafi sai ki shirya da wuri goma anan zatayi min.
kuɗi ta ciro ta miƙawa Amal ga wannan ki ƙara kuɗin provision.
Ngd , har waje tara kasu sai da taga fitarsu ta koma ciki bedroom tashige tana tunanin maganar Hjy Sadau wacce suka yi makaranta tare kawarta ce sosai tun bayan da mijinta yasa mu transfer zuwa jos shekaru shida kenan rabon dasu ga juna shine da tazo kawo yarinyarta makaranta ta biyo don su gaisa.
Sallamar su Nawwal da suka dawo daga islamiyyah yasa ta sakin murmushi tana masu oyoyo.
Fido ce ta zube saman gadon tana faɗin, wash momy na gaji yunwa nake ji.
Nima wllh cewar Nawwal.Ynz me zaku ci ta tmbye su?.
Asim yace nidai Momy pototoe ketchup nake son ci.Nawwal tace ni koma mene ne zanci don nagaji da shan caramels.
To ke kuma fa momy ta tmbyi Fido?.
Ni dai fried chicken salad wanda yaya fariis ya bamu jiya shi nake so.
Don uwarki sai kije ya baki daga yau kar na kuma ganin ku tare in ba haka ba sai ranku yayi mugun ɓaci ku tashi muje eatry ta riƙewa asim hannu yaran kuma na binta abaya har suka fita.Direba na ganin su, yasan inda zasu domin kusan kullum shike kaisu cin abincin, mota ya ciro suka wuce sai da suka biya super market kowa ya ɗibi kayan kwalama sannan suka dawo gida lokacin Daddy na falon shi da Fariis suna hira yana ganin shigowar Momy ya bar falon da harara ta rakashi, shi da bai masan tana yi ba.
Kusa da Daddyn ta zauna wanda ya zuba mata idanu yana mamakin ta ace da kuɗin shi babu wanda bai sanshi ba amma sai dai a siyo abinda zasu ci a waje tana mace amma bazata iya girki ba wannan abu da ciwo yake.
Kuje ku kwanta cewar Momy dake kallon yaran suna ta ciye2nsu, duk suka miƙe suna wa Daddyn sai da safe, sai da taga sun shige ɗakin su ta kalli mijinta wanda ko magana bai mata ba.
Daddyn Nawwal Hajiyarmu fa ba tada lfy.
A kaikaice ya juyo yana saurarenta sannan ya ce meya same ta, tun yaushe kenan?.
Hmmm ɗazu Hajara ta kira ni take gaya min har ruwa sai da aka ƙara mata, ciwon ta ne ya tashi fa.Subuhanallah Allah ya bata lfy gobe sai ki shirya muje mu duba ta koh?.
Toh amma baka ce goben zaka koma aiki ba tana wani marairaice fuska.Eh daga can sai na wuce ai.
Aa kawai ka wuce inka dawo sai kaje tunda ma taji sauki.
Shikenan Allah ya bata lfy amma dasu Nawwal zakije?.
Aa dubiya fa zani ba dade wa zanyi ba, Baby zata zauna dasu gobe da safe zata zo.
Ya kamata a nemi wasu ƴan aikin don baby ba zata iya da ɗawainiyar yaran nan ita kaɗai ba.Kar kadamu zan kira su dawo da sauran masu kula da aikace2n gidan, ni na fara jin barci kai ba ynz zaka kwanta bane?.
Ina kallon labarai inna gama zan kwanta.
Nan ta barshi sai da ya gama kallon sannan ya kashe komi ya bi bayanta lokacin ta daɗe da barci shima ya kwanta.
Fariis kam tuni yayi barci cike da damuwa da kaɗaici bai san sanda barcin ma ya ɗauke sa ba.....................