BARRISTER FARIIS

5 0 0
                                    

   ✨ ✨✨✨✨✨
        *BARRISTER FARIIS*
     ✨✨✨✨✨
 

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).

          *P.W.A*✍️

*STORY*

*&*

*WRITING*

          
  UMMUH ABUU SADEEQ
          (Cuty pie).
        
      2⃣1⃣ & 2⃣2⃣

Da asuba tana farkawa ta ga rigar jikinta duk atattare cinyoyinta awaje ahankali ta tashi tashige toilet agurguje tayi wanka ta fito ta tada sallah, tana gama shirin makaranta ta zauna a falo tana jiran fitowarsa, ta kusan minti talatin amma babu shi, hijabi ta cire ta shiga gyaran falon kamar tayi kuka, tana tsaye ta jiyo takunsa ba tare da ta waigo ba ta cigaba da aikinta.

Kwanciya yayi asaman carpet ya rufe idanu, jin kamar baya falon ya sata juyowa, kwance ta gansa sanye da T-shirt yellow da baƙin wondo, k'arasowa tayi ta durƙusa can nesa dashi cikin muryar ta siririya da dad'i tace ina kwana ?.

Shiru yayi kamar baiji taba, itama bata sake cewa komai ba ta wuce d'aki ta kwanta tana hawaye ya za'ayi daga fara zuwanta makaranta ta fara fashi duka2 ma sau nawa taje, batasan lokacin da ya shigo ba sai jinsa tayi yana fad'in ki hak'ura da zuwa makaranta yau ga breakfast nan, ya ajiye ledar dake hannunsa ya fice.

A hankali yake tuk'i, abakin wani privet clinic yayi parking motarsa ya shiga ciki, kasancewar mutumin yasan da zuwansa kaitsaye yashiga ɗauke da sallama abakinsa kujerar dake kallon Dr ya zauna sannan ya mik'a masa hannu suka gaisa.

" Barr ka b'uya da yawa ".

' Dr kasan yanayin aikin namu babu wani hutu shysa ka jini shiru ban kuma dawo wa ba '.

" Gsky kam toh Allah ya taimaka ".

' Amin, Dr labaran allurai da drugs nazo k'arba kawai '.

" Fariis for your own good ka samawa kanka lfy ta hanyoyin bin shawarar da na baka akwanakin baya ".

Murmushi kawai ya yi yace Insha Allahu Dr.

Dubashi Dr labaran yayi sannan ya masa allurai ya kira nurse taje pharmacy ta siyo masa magunguna, nan suka yi sallama ya fito ya kama hanyar court.

K'ira'a yake ji yana bin surar cikin kwarewa har wani lumshe idanu yake don dad'i, wata farar Hilux ce tasha gabansa da gudu, da sauri ya taka burki yana bin motar da kallo baiyi aune ba yaga glass ɗin gaban motarsa sun tarwatse tasss yaji wani raɗaɗi ya ratsa damtsen hannunsa, sun saita bindigar zasu kuma harbinsa suka ja motar da mugun gudun tsiya don ganin 'yan sanda na gudu sun zata ko biyosu suke ga mutane kowa ta kansa yake titin duk ya hargitse da ababen hawa.

Da gudu yabi bayan motar duk da jinin dake tsiyaya a hannunsa, b'at suka b'ace masa kamar walk'iya, agefen titi yayi parking yana bin inda suka harbeshi da kallo tsaki yaja ya ciro wayarsa ya kira headquarter na police yace a baza jami'an tsaro tunda na traffic mugayen matsorata ne duk sun fece.


Zaune take a falon tayi shiru taji shigowarsa, da sauri ta ɗago tana kallonsa duk idanunsa sun rine, ta lura yau ba yadda tasa ba ganinsa bane kwata2 bashi da kuzari, ta damu tasan meke damunsa, hawaye ne ya cicciko kamar zatayi kuka ta ƙarasa inda yake kwance tace baka da lfy ne?.


Idanunsa ruf tsabar raɗaɗin da yake duk da yaje asibiti an cire harsashin har gado aka bashi amma ya k'i yarda saboda ya barta ita kad'ai, Dr labaran ne ya kawoshi har gida amma bai shigo ba ya wuce, ba tare da ya amsa mata ba ya tashi daga kwancen yana k'ok'arin miƙewa tsaye amma ya kasa saboda jirin da yake ji, bak'ara min zafi da radaɗi yake ji a hannunsa ba, sai rumtse idanu yake.


BARRISTER FARIISWhere stories live. Discover now