BARRISTER FARIIS

6 1 0
                                    

   ✨ ✨✨✨✨✨
        *BARRISTER FARIIS*
     ✨✨✨✨✨
 

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*

( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ ).

          *P.W.A*✍️

*STORY*

*&*

*WRITING*

          
  UMMUH ABUU SADEEQ
          (Cuty pie).

  1⃣8⃣

Laptop ne agabansa yana aiki yayin da Fido ke kwance kusa dashi tana masa surutu, sam hankalinsa naga aikin da yake, saukowa tayi tana faɗin nikam Yaya na tafi, baice da ita komai ba ya cigaba da abinda yake, kusan minti talatin ya ɗauka kafin ya rufe laptop d'in ya shiga toilet ya wanko fuskarsa wani barci2 yake ji ga yamma tayi, mukullin mashin d'insa ya d'auka ya fito kai tsaye d'akin Momy ya nufa daga bakin k'ofar ya tsaya yana sallama ganin Baby yasa ya had'e rai ya shige d'akin waya ya tarar Momy'n nayi saida ta gama wayar yace ' Momy barka da warhaka kin dawo lfy? '.

" Wani matsiyacin kallo ta watsa masa sannan tace sai yau kasan na dawo? ".

" Eh kusan haka don bai dad'e da Fido ta sanar dani ba ya fad'a kai tsaye ".

" Ai da uwar kace bazaka ce haka ba amma da yake ni marainiyar wayonka ce yau kusan kwana uku kenan da dawowata amma sai ynz kaga daman zuwa aiko ban haifeka ba yaci naci albarkacin barinka da nayi harka kai iyanzu kana numfashi wllh ".

Bai tanka mata ba ya tashi ya wuce ɗakinsa don zagin umminsa da Momy tayi yasa ranshi b'aci kan gado ya fad'a ya lumshe idanu nan da nan kuwa barci ya kwashesa, kiraye kirayen sallah ne ya tashe shi daga barcin tsaki yaja ganin barcin da beyi niyya ba ya kwashesa agogon ɗake manne a bangon ɗakin ya kalla yaga har anyi sallah'r magrib da sauri ya tashi yayo alwala ya tada sallah ya jima yana addu'oi kafin ya kuma hayewa gadon sai barci.

~~~~~~~~~              ~~~~~~~~~

Zaune yake acikin motarsa yayin da ya kife kansa a sitiyari, ahankali ya d'auki wayarsa dake faman ringing ya kara a kunne daga can Sagir yace are you off to work?.

" Cikin sanyi yace yes ".

' Okey gani nan ahanya ya katse wayar minti goma ya k'araso da Sagir, motar Fariis ya bud'e ya shiga yana binshi da kallo ganin yayi shiru kuma bai d'ago ba '.

' Barrister are you sick?, Sagir ya fad'a yana d'ago fuskar Fariis '.

Murya k'asa2 yace stomach ache bazan iya driving ba.

" Ayyah sorry dawo nan sai nayi driving ".

Suna isa gida Sagir ya zagaya ya bud'e masa k'ofa suka ƙarasa shiga ciki, ko takalmin ƙafarsa bai iya cirewa ba haka yayi kwanciyarsa haɗe da rumtse ido sosai cikin ke masa ciwo, ataƙaice sai da yayi kwana takwas bashi da lfy ko wajen aiki baya zuwa Sagir ne ke kula dashi, yau dai ya samu ya koma aikin amma koda yaje bai iya yin komai ba haka ya dawo gida da wuri ya kwanta don baya jindad'i sosai.

Bayan sati biyu tsaye take a kitchen tana taya Uwale girki inda ta ɗauki trayn abincin zata kai dinning lokacin shikuma yake saukowa daga stairs kunnensa saƙale da headphone yana shan waka, afakaice yake kallonta saboda rabonsa da ganinta kusan 3 weeks kenan tun ranar da ya hasketa da fitilar mashin da dare bai sake ganinta ba shi har mantawa yake da ita, har ya kai bakin k'ofa ya dawo daidai sannan ta juyo zata koma kitchen, a d'an tsorace ta waro manyan idanunta tana kallonsa shima kasa dai kallonta yayi ganin ta d'an rame.

Da sauri ta sunkuyar da kai zata wuce, yace " You don't know how to greet sai bin mutane da manyan idanu koh?".

Jin numfashinsa awuyanta hakan yasa ta kasa cewa komai, kafaɗarsa ya ɗaga yace No need basai na sanar dake good and bad ba kije ki gaida Momy yana gama faɗa ya wuce, aikin da bata koma sun cigaba da Uwale ba kenan ta wuce ɗaki tayi wanka ta shirya cikin atampa riga da siket tayi kyau duk da babu kwalliya afuskarta, hijab tasa ta fito ta nufi ɗakin Momy aƙofar ɗakin ta haɗu da ita zata tafi aiki har k'asa Jiddah ta durƙusa tana gaisheta.

BARRISTER FARIISWhere stories live. Discover now