Atlanta, Georgia U.S.A
Faheema Sooraj zaune take a class da waya rike a hannunta tana video call da kanninta Faheam, takardu ne zube a gabanta, da gani karatu take ta bari tana call din, sanye take cikin tsadadiyar material sky blue mai ratsin white flowers, tayi dankwali da same material din akanta tazo tayi wrap round da farin gyale, idanunta sanye da reading glasses, sai faman murmushi takeyi tana sauraron abunda Faheam yake fad'i inda yake bata labarin abunda ke faruwa a gida, tunda ta koma school a Atlanta Georgia dake kasar America tana karanta course din Medicine bata kara dawowa ba yanzu tayi kusan semesters shida kenan da tafiyarta, kuma tayi nisa sosai da karantun sam bata wasa, yanzu haka jarabawarsu ce ta matso kuma a halin da ake ciki babu abunda takeso illa ta samu ta kammala ta dawo gida taga iyayenta da yan'uwanta don tayi missing dinsu sosai, murmushi take inda Faheam yake gaya mata daddy yayi approving zuwa flying school dinsa, daman Faheam tun yana karami yakeda burin zama pilot maganarsa da'ya biyu yana son ya tuka jirgin sama, mahaifinsu ya bashi goyon baya yace insha Allah yana gama secondary school za'a nema masa admission, yanzu haka yayi graduating daga secondary school yana shekara goma sha biyar zai shiga na sha shida kenan, Faheam shine yake bin Faheema daga shi sai kaninsa Farhan wanda shima yazo ya kamoshi yanzu, Farhan dogo ne sosai tsawon daddynsu ya dauko, idan ka gansu tare sai ka aza tagwayene shida wansa. Farhan shekararsa 14 yana S.S.1 sai kuma autarsu Fayha wace take shekara goma tana J.S.S1. Su hu'du ne a wajen iyayensu.
"Na kusan zuwa na sameki a U.S Adda, amma na Florida aka samu, kinsan da Jordan ne toh an bincika makarantar na samun dan delay and the charge difference is about $10,000 suna ha'dawa da private pilot license har ATPL in less than 2 years so shine daddy yace gwanda naje nayi a Florida"
"Kai amma naji dadin wanan maganr, at last zamuji gari da maganar flying, me mommy tace?"
"Me kuwa zata ce ai dole ta bada approval dinta"
Dariya Faheema ta sake don tasan yanda mommy nasu take bala'in ji dasu musamman Faheam, ko itama Faheema tafiyar nata sai data jishi da kuka suka rabu a airport, gashi Faheam shima zai zo ya tafi.
"Ina Farhan?"
"Yana sama"
Ta'be baki Faheema tayi don tasan halin Farhan sarai shi rai da rai yana daki baya ta'ba shiga cikin mutane, duk cikinsu yafi miskilanci, mommynsu tayi fa'da harta gaji, abokan hiransa sune daddy da uncle Ammar idan basu nan zaka jishi tsit kamar baya gidan, yana can dakinsa yana buga video games, baida hayaniya sam.
"Fayha fa?"
"tayi bacci"
"Meyasa aka bari take bacci by this time? Yamma fa ya gabato"
"Wai cikinta ke ciwo tasha magani ta kwanta tun da suka dawo hutu daga school take complain ciwon ciki"
"Kai Subhanallah amma dai tana shan magani ko"
"Eh tana sha kinsan shan maganinta sai anyi da gaske"
Faheema ta gyada kai tana tunanin rashin son magani irin na kanwarta, gashi tunda daddy ya maidasu boarding school ita da Farhan aka soma tunanin yanda Fayha zatayi coping acan, don koya za'ayi Fayha ba zata dauki magani tasha sai taga uban bari.
"kinsan Uncle Ammar yazo ?" Faheam ya katse mata tunani
Zaro ido tayi cike da mamaki " Uncle Ammar yazo gida?
Faheam ya gyada mata kai
"Yaushe? Kuma fa jiya munyi waya dashi bai sanar dani ba"
"Yau da safe ya iso, muma unexpectedly muka gansa, it seems like akwai aikin da sukeyi shida daddy"
"kai zan kirasa yanzun nan muna gama waya" ta fa'da jikinta na bari.
Haka suka cigaba da labarin gida har na tsawon 20 mins tukuna Faheam yace mommy na kiransa zai je ya sameta a sama. Faheema tace toh ya gaisheta zata kirata anjima idan ta fito a class, yace toh. Haka sukayi sallama ta katse kira. Suna gama waya da Faheam ta soma neman uncle Ammar a layinsa.
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomanceBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...