Da dare misalin 9pm faheema tayi shirin wanka kenan, daga ita sai bathrobe sanye a jikinta sai kuma towel data daura kanta tayi turban, skin care routine taketa faman yi a fuskarta, breakouts din sun ragu sai dai suna kokarin su bar mata spots a fuska wanda take kokarin avoiding saboda fair skin dinta. Nivea face wash tasa ta wanke fuskarta sannan ta dauko face tonner tana kokarin goge fuskarta dashi sai ga text din Ammar ya shigo wayarta, budewa tayi taga hotunan tsadadun smart watches na apple guda biyu ya turo mata yace ta za'ba. Daya mai round head peach color, da'ya kuma white mai square shaped, white din yayi mata kyau sosai don haka tace dashi white takeso, yace okay zai sa a kawo mata, godiya tayi mishi cike da jin dadi.
"What are you up to?" Ya tambayeta
"Wanka zan shiga yanzu, ina skin care"
"Mene skin care?"
Yan' smileys ta turo masa guda biyu kamar haka "🙄🙄 baka san skin care ba Uncle Ammar?"
"Ban sani ba.."
"Skin care is a range of practices that support skin integrity and to enhance its appearance, and relieve skin conditions. Ina amfani da skin care products nayi enhancing nawa"
" uhum wanan abun naku ne na mata ai"
"Wlh Uncle Ammar I'm having breakouts all over my face 😩😩 I'm starting to have spots"
"Since when?"
"Tunda na dawo, bakayi noticing ba?"
"I didn't notice anything"
"Kaii Uncle Ammar...har mommy ma tayi noticing, it's very obvious fa. Bari kaga"
Camera tayi switching tayi snapping fuskarta tayi zooming sosai sannan ta tura masa, Ammar yana daga kwance kan gadonsa yaji shigowar hotunan ya duba yaga ta turo masa hotunan fuskarta, ya kurawa hotunan ido sosai, spots din daya fito mata yaga kadan ne ta side din fuskarta, it's not even that obvious idan mutum baya kura ido sosai ba, but to him she's still looking as beautiful as ever.
"I don't see anything" ya tura mata da reply
"Hmmm Uncle Ammar ka kalla da kyau, kawai dai baka son fa'di ne"
"Small I see nothing wrong, spot or spotless you're still the most beautiful woman I've ever laid eyes on , you don't have to bother yourself about all these things"
Murmushi tayi data karanta reply dinsa tace "haka dai kace"
"Haka ne"
Shiru ne ya ziyarcesu kowa da abunda yake tunani game da dan'uwansa, sunfi 2 mins a hakan sannan Ammar ya turo mata da sakon "Zaki kwanta yanzu?"
"Eh zanyi wanka na kwanta"
"Toh shikenan sleep well, karki manta kiyi addua kafun ki kwanta kinji.."
"Insha Allah Uncle Ammar"
"And small..."
"Na'am..."
"I love you with all my heart, just know you mean the whole world to me and I'll be standing by until the day you say yes to me. You don't have to reply until you're ready Good night❤️"
Shiru tayi tana karanta sakonsa kirjinta na bugawa da matsanancin karfi, tafi 5 minutes a hakan tanata nanata kalamansa cikin kwakwalwarta tana jin wani irin sanyi a ranta at the same time fargaba, lumshe idanunta tayi tana ayano abubuwa da dama cikin ranta ta. A hankali ta mike ta karasa cikin bayinta dake dauke da komai na more rayuwa a cikinta, very neat and classic, essential oils dinta masu dadin kamshi ta zuba cikin ruwan wanka data tara cikin bathtub sannan ta kwance towel din jikinta, a hankali ta zira santala santalar cinyoyinta ciki ta zauna ha'de da lumshe ido tana jin yanda dumi da kamshin ruwan ke ratsa ko ina a jikinta, babu abunda ke mata yawo a kwakwalwa ila kalaman uncle Ammar, from time to time take jin wani irin sanyi da farin ciki na ratsa ko ina a jikinta, soaking tayi na kusan 12 mins sanan ta fara wanka ta cu'da ko ina a jikinta, wanka sosai tayi ta fito ta daura towel a jikinta ta goge sanan ta daura bathrobe ta karasa daki, wayarta ce taketa faman kawo haske alamun notifications na shigowa ta karasa ta dauko taga sakonin Nasar ne, wanda tun jiya yaketa kokarin samun attention dinta amma abun ya citura, reply ta masa tace she's a bit busy yanzu ta fito wanka amma she'll chat him up idan ta gama yace toh yana jira, ko data gama shiri ta hau lafiyar gado suka fara chatting already ta gaji don babu abunda takeji a wanan lokacin sai bacci, tun yana janta da hira tana responding har bacci yayi awon gaba da ita ta Kyaleshi.
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomanceBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...