Chapter 20

374 22 3
                                    

Tun wanan wayar da sukayi da Nawlah Faheema ta dan ji sauki a ranta, kullum cikin dare sai ta tashi ta kaiwa Allah kukanta ya fito mata da mafita cikin lamarin nan, idan Alkhair ne tsakaninta da kawunta Allah ya tabbatar idan babu kuma Allah ya fito mata da wanda ya fishi, da wanan ta samu ta la'laba zuciyarta har ta dawo normal abunta babu wata sauran damuwa. Bangaren Ammar kuwa a cikin satin, yaji sauki sosai sai dai har zuwa lokacin baya zuwa ko ina, rai da rai yana gida, Yau ta kasance ranar asabar, Faheema na kwance akan doguwar kujera a parlorn kasa tana latsa wayarta hankalinta yayi matukar daukewa akan abunda take karantawa Ammar yashigo cikin parlorn har yazagayo ta bayan kujerar datake kwance akai bata sani ba, yayi tsaye akanta tare da  zuba mata mayyataccen idanunsa. Kamshin turarensa ne ya soma giftawa ta hancinta nan take kwakwalwarta ta bata cewa Uncle Ammar is around, ai kuwa tana da'gowa sukayi ido biyu dashi, wani irin frigita tayi ta dawo cikin hayacinta ha'de da wata irin wuntsulowa daga kan kujerar dake kwance tayo kasa, cikin sauri ya kamota kafun ta buga kai a kasa, yayi saurin meidata, dariya ne yayi niyar kubuce masa, ya sanya hannunsa yana shafo saman kanshi zuwa goshinsa yana kallonta tare da watsa mata idanunshi yace "kai amma gaskiya small anyi muguwar matsoraciya meye haka? Kalli dan Allah yadda kikayi sai kace wace tayi gamo"
Cike da shagwaba ta turo masa yar karamar bakinta "haba Uncle Ammar, ya bazan tsorata ba, how can you sneak up on me like that..yanzu gashi kasa na buga kai, wlh nima sai na rama..." ta dafe goshinta tana kokarin mikewa.

Zaro ido yayi yana kallonta cike da mamaki "au wai don ma naji tausayinki na tare shine zaki ce nasa kin buga kai? Lallai ma small"

"Wlh sai na rama Uncle Ammar..." ta kara fa'da a ha'de da mikewa. Ganin da gaske take yasa Ammar ya kara da sauri, pillow ta dauko ta bishi a guje tana ihun sai ta rama, shi kuwa sai faman dariya yake mata, ai kuwa suna isa daidai dining bata ankara ba ta bugi babbar yatsarta kan table, yar' kara ta sake don wanan karon kam da gaske n ta fa'di a kasa rike da kafarta  "wayyo Allah kafata" cikin sauri Ammar ya waiga ya ganta kasa zaune tana ware baki, cikin sauri ya karaso hankalinsa a tashe ya tsuguna gabanta bai san sanda ya tattarota jikinsa hankalinsa a tashe yana fa'din "Subhanallah meya faru small..."

"kafata uncle Ammar wayyo...yatsata zata cire"

Cikin sauri ya kamo kafar yana dubawa, yaga da gaske ne ta buge, sannu ya shiga mata yana massaging wajen "wayyo I'm so sorry small.. so sorry..." ya fada duk hankalinsa a tashe tamkar zai maidata ciki. Faheema kin yin shiru tayi sai faman ba're baki takeyi. Ammar ya marairaice mata "shhh dan Allah small kiyi hakuri kiyi shiru kafun mommynki tazo tayi tunanin nayi miki wani abu ne"

Kinyin shiru tayi sai faman rarashinta yakeyi yana bata baki, da yaga takiyin shiru ya sashi fa'din"toh gani ki rama.."

Cikin sheshekar kuka ta dago tana dubansa da fararen idanunta da suka cika da hawaye, "gani kinji..ki rama" ya sake maimaitawa

Matse hawayen tayi suka gangaro mata bisa soft cheeks dinta, a hankali yasa hannu ya soma goge mata hawayen "ki daina kukan kinji my love, ina ganin hawaye na zuba cikin kwayar idanunki tamkar ana zaran raina, indai ramawa zaisa ki daina kukan to gani ki rama" ya fa'da mata muryasa kasa kasa, fuskarsa dab da nata har suna iya shakar numfashin juna. A hankali yaga ta dakatar da kukan nata ta soma girgiza masa kai "menene?" Shiru tayi masa "Bazaka ki rama ba?"  Nan ma ta sake girgiza masa kanta, a hankali yaga ta matso ta daura kanta bisa kafadarsa, ajiyar zuciya ya sauke ya daura hannunsa bisa saman kanta yana shafa a hankali. He felt so at ease with her in his arms, felt like dwelling in the moment forever, Sunfi 2 minutes a hakan daga bisani suka soma jin ana saukowa, cikin sauri ta kwace jikinta daga nashi ta soma matsawa  "ya naji ihun kuka kamar na baby...? Ganinta sukayi ta karaso, idanunta suka sauka kan Faheema dake zaune a kasa sai faman narai narai takeyi da idanu, ga Ammar shima tsugune gabanta kamar mai rokan gafara, confusion ne ya riske Hibba tana dubansu da'ya bayan da'ya" What's going on here?" Ta kuma nanata tambayar

❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥Where stories live. Discover now