Faheema basu gama hira da big mommy ba sai wuraren sha' dayen dare, big mommy ta karasa part din Alhaji ita kuma Faheema ta haura sama zuwa daki don ranar a gidan zata kwana. Tana hawa gado ta kunna data din wayarta, sakon hotuna ta fara gani daga Uncle Ammar, cikin sauri ta shiga contact dinsa tana budewa taga Akwatina guda biyu an ha'de su guri da'ya. Nan take wani irin farin ciki ya lulubeta ta soma nemansa a layi, bugu daya ya dauka "yay...uncle Ammar is coming back, Uncle Ammar is coming back..." ta soma mishi waka a kunne tana dariya cike da farin ciki.
Ammar yana jin muryarta ya soma murmushi amma jin abunda ta fa'di yasa ya bone, "waye haka zai dawo"
"Kai mana, ko ba jakar tafiyarka bane nake gani"
"Oh you mean the picture I sent to you? Ai ba nawa bane, jakar abokina ne zan raka airport"
Haba nan take Faheema tayi kicin kicin da fuska "Haba Uncle Ammar yanzu fisabillah haka akeyi? Wani abokinka ne zaka raka, ni bana son irin wanan..."
"Irin me?" Ya tambayeta
"Kana ja mun rai Uncle Ammar" ta karasa maganar kamar zatayi kuka
Dariya ne ya kubuce masa, "tam shikenan yi hakuri that was not my intention kar ayi mini kuka, bana abokina ne ba nawa ne, I'm preparing to come back"
"Da gaske?" Ta tambayeshi cikin karamin murya
"Affirmative"
Murmushi ta dan skar masa "Tam shikenan, I'll be expecting you Uncle Ammar"
"Meza tanadar mun?"
Lumshe idanu tayi a hankali tana dubansa sannan tace "me kakeso na tanadar maka?"
"Komai ma"
"Toh shikenan uncle Ammar, zanyi maka tanadi na musamman"
"Da gaske?"
"Da gaske" ta bashi ansa
Ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta da fine eyes dinsa, wani irin sanyin dadi yakeji yana ta'ba duk wani ga'ba na jikinsa, ji yake tamkar ya rufe idanunsa ya ganshi a gabanta.
"There's this chicken Afridata danace zan maka anytime ka dawo"
" wow really"
"Da gaske Uncle Ammar zakaji dadinsa sosai"
"Toh shikenan small, can't wait to taste it"
"And I can't wait to see you" ta karasa maganar tana murmushi. Shima murmurshin ya sakar mata "I can't wait to see you too " hira suka shiga yi sosai yana cigaba da zolayarta.
**********************
Washe gari ranar litinin kamar yanda Ammar ya daukarwa Faheema alkawari ya soma shirin barin Paris don ya dawo Nigeria, aikin daya tafi yi ya samu ya kamala, he has sealed every deal that sent him there. Yana gama shirinsa ya wuce airport din Paris charles dè gaule. Da safiyar ranar kuma Hibba ta tashi tunda wuri ta kimsa, saboda daddyn Faheema zashi Abuja meeting a ranar, jirgi na jiransa 10:am departure, ta samu ta ha'da mishi komai da komai da zai bukata tana jiran saukowarsa. Duk da opportunities din yan' aiki da takeda, Hibba bata sakar musu komai don duk abunda ya danganci kula da mijinta bata wasa, tunda ta haifi Fayha ta ajiye maganar koyarwa don Hassan ya nunar mata zai bude mata nata makarantar ta zama proprietress idan tana so, bata dai bashi go ahead ba har yanzu amma ya nuna mata anytime she's ready, he'll do it for her. Yanzu haka sanye take cikin riga da wando sai dan mayafi data yafa tana kai kawo tsakanin kitchen da parlor ta duba time taga 9:15, tasan at anytime zai sauko, Faheema tana kitchen tana kokarin soyawa kanta kwai da chips salad da zata ci as breakfast. Faheam baya nan tunda safe ya fita zuwa makarantarsu daya gama zai je ya karbo wasu results. Bafi 5 minutes ba daddyn Faheema ya sauko sanye cikin black suits da suke matukar fitting jikinsa, everything about him screams powerful, yana karasowa parlor ya kaure da tsaddar kamshin turarensa. Hibba ta karaso tana sakar masa lalausar murmushi "baby ka sauko"
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomanceBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...