Jin muryar Faheema tana ihun sunan Ammar tana mishi oyoyo yasa Hibba ta mike daga kwanciyar da take a daki, hijab ta zira sannan ta fito a ranta tana fa'din Faheema dai kam har yanzu yaranta bai gama barin jiki, ihun da take ko Fayha ma iyakacinta.
A hankali ta soma saukowa daga saman matakala, tana idasa saukowa parlorn ta tsaya curuss sakamakon sight din data tadda. Wani irin harbawa kirjinta yayi ganin Faheema kwance bisa kirjin Ammar idanunta a lumshe suna magana kasa kasa tana murmushi, shima yana biye mata. Hibba kasa motsawa tayi tana binsu da ido musamman ma Ammar da yake kallon Faheema da wani irin abu cikin kwayar idanunsa da bazata iya misaltawa ba. Innalillahi ta fa'da kasan ranta, What's going on here?
Basu ma san da shigowarta ba, kasa hakura tayi ta furta "keh Faheema!"
Firgigit sukayi suka waigo a tare suka ganta, a hankali ta soma takowa inda suke, Faheema ce ta da'an ja jikinta ganin kallon tuhumar da mommynta ke binta dashi, shi kuwa Ammar ko a jikinsa.
"Me nake gani haka, Faheema what are you doing?"
A rikice Faheema ta soma bata ansa da "uhm..mommy, ina yiwa Uncle Ammar sannu da zuwa ne"
"Kina masa sannu da zuwa shine kike shigewa jikinsa kika mance da kanki haka?" Ta karasa maganar cike da tuhuma
Ganin Faheema tayi shiru tana dubanta kamar bata fahimce dalilin dayasa take mata wanan tambayar ba ya sata fadin "Baki san kin girma ba yanzu Faheema? Da da yanzu ba da'ya bane, You're no longer a little girl"
"But mommy...uncle Ammar ne fa"
"Ko ba Uncle Ammar din ba" ta bata ansa ta juyo tana duban Ammar din dayayi shiru yana dubansu "kai kuma you just stood there kana kallonta..."
Cike da rashin damuwa ya bata ansa " toh Ya' Hibba she just explained to you, like she said she's just greeting me that's all"
Wani irin kallo Hibba ta watsa mishi, cike da rashin yarda tace "Gaisuwar ne sai an ha'de da runguma, toh ban yarda da wanan ba, kana jini ko. Idan ita bata san me takeyi ba kai ai you should know better..."
Murmushi Ammar yayi ya koma ya samu wuri ya zauna yana fa'din "toh ya'Hibba za'ayi hatara insha Allah it won't happen again"
A hankali taga ya dubi Faheema, itama kallon Faheema tayi wace ta tsaya galala kamar wace kwai ya fashewa a ciki, Ganin Ammar ya maida zancen nata wasa bai ma dauki abun serious ba yasa taji hankalinta ya kara tashi, ta juyo tana dubansa, so many thoughts started rushing to her at once. Ba dai....? No it can't be true ta fadawa kanta. Tun lokaci daya zo ya tareta da wanan maganar a lokacin tayi watsi da maganar tasa. Kuma ta nunar mushi Faheema is a no go area for him, ta haramta gareshi.
She thought he had let go of the whole thing tun wanan lokacin, amma wanan kallon data ga yana yiwa Faheema, duk wanda yasan menene asalin allamun so yaga wanan kallon da Ammar yake yiwa Faheema yasan me kallon yake nufi don kallo ne mai dauke da din'bin so da tsantsar kauna, bata ta'ba ganin ya yiwa wata ya' mace ba sai a kanta,
tasan da hakan ne don tana ganin irin wanan kallon a wajen mijinta har ma wanda yafi hakan, don haka dole ta taka mishi birki! Tun ba'ayi nisa ba, Faheema is innocent, the poor girl is too innocent for him, gwanda tun wuri yaje ya nemo matarsa a waje amma badai yar'ta ba don bazata bashi ba. Me zata cewa mahaifinta? Ta ina ma zata fara? Me zata cewa Hajiya? Me zata cewa yan'uwan mijinta? Faheema might be too oblivious to his feelings don tasan yarinyar ta daukeshi as nothing more than her uncle, yanda ta dauki kanen babbanta su uncle Sadik haka ta dauki Ammar shima as her Uncle kuma abun yazo ya ha'de da shakuwa mai tsanani tsakaninsu, tun kafun ta kai haka suka ku'la bond mai karfi, komai nata Uncle Ammar, magana da'ya biyu Uncle Ammar ne, tun kafun takai haka school shi zai kaita, islamiya ma haka zai kaita ya dawo da ita, homework da school assignment da karatu shi yake tayata yi har ta karasa ta samu scholarship a turai ta tafi amma duk da hakan bond din nasu bai yanke ba sai ma abunda ya karu.
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomansaBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...