Washe gari Faheema bata tashi da wuri ba saboda bata samu ishashen baccin ba, cikin dare ciwon mara na period ya sata a gaba, sai data sha pain killers tukuna ta samu relief, sai wuraren karfe goma na safiyar ranar, k'arar knocking din da akewa kofar d'akinta ya farkar daita, "Faheema! Faheema!! ......."
cikin muyar bacci ta amsa "na'am mommy" had'e da yin mika da salati
"ki tashi mana, daddy fa ya dawo tun dazun yana tambayarki"
A hankali Faheema ta furta "toh mommy na tashi ai, gani nan saukowa"
Jin yanda Faheema ta ansa yasa ta turo kofar ha'de da sallama ta ganta kudundune cikin bargo, "lfy na jiki haka?"
"Wlh mommy ciwon mara ne amma ya lafa mun yanzu"
Cikin tausayawa Hibba ta karaso ta dafa kanta "sorry baby, kin sha magani?"
"Nasha mommy"
"Tam yanzu ki tashi ki gyara jikinki sai ki sauko kiyi breakfast"
"Toh mommy" Faheema ta fa'da ha'de da mikewa. Ita kuma mommyn nata ta juya ta koma bangarenta . A hankali ta tashi da kyar ta zauna ta ziro kafafunta kasa tana mai dafe ha'barta dan har lokacin bacci bai fita cikin idanunta ba, ta mike cikin sanyi jiki ta nufi wardrobe dinta, ta kwaso toiletries sannan ta shige bayi ta tasoma yin brush tana kallon mirror dake gabanta, fatar jikinta ya kara haske ya koma kamar milky white, ga tsinin hancinta sai kyali yake kamar ta shafa vaseline, it daman tana period haka yanayin jikinta yake sauyawa, kirjinta ma haka ya kara cika. Tana gama brush ta kuskure bakinta sannan ta ha'da ruwan wanka. Bayan tayi wanka ta fito,ta shafa manta na Dove shea butter and Vanilla softening body lotion, sannan ta shirya cikin wata doguwar riga har kasa, curly hair dinta tayi packing dinsa cikin pink ribbon sannan ta d'aura hula a kai. Turare mai sanyin kamshi ta feshe gabad'aya ilahirin jikinta dashi, ta d'auki wayarta ta kunna ta dawo kan resting chair ta zauna tana duba sakonin cikin wayar ko zata ci karo dana Uncle Ammar amma shiru, tun jiya he hasn't reached out to her itama ta kasa samun shi, tayi shiru tana nazari, wayarce tayi vibrating a tunaninta shine ta duba taga sakon Nasar ne, yana shaida mata ya shigo Lagos jiya, ta dafe kai don bata ma san reply da zata bashi ba. A hankali ta mike jiki a sanyaye ta bar d'akin zuwa parlour'n, tana fitowa ta hango mommynta da daddynta zaune a dining har sun fara breakfast saboda rashin k'arasowarta. Tana ganin daddynta taji mood dinta yayi lighting bata san sanda ta saki murmushi ba ta karaso tana fa'din "oyoyo daddyna..."
Shima yana ganinta ya soma da "wa nake gani haka, is that my beautiful princess?"
Hugging din daddynta tazo tayi tana mishi sannu da zuwa ha'de da cewa tayi missing dinshi sosai, shima yace haka yayi missing dinta sosai, Hibba na kallonsu cike da sha'awa.
"Why are you late for breakfast?" Hassan ya tambayi diyarsa, don Faheam tun dazun yazo yayi karyawarsa ya koma sama, shiru tayi ta da'an kau dakai tana murmushi taja kujera ta zauna, Hibba ta d'ago ta du'beta tunda tasan abunda ke damun babyn nata tace "ni nace ta tayi baccinta, tunda ta dawo har yanzu bata samu isashen hutu ba"
"Wai haka?" Daddynta ya tambayeta
A shagwabe Faheema ta gyada masa kanta, yanda tayi abun yasa dukansu suka sa dariya, Hibba ta turo mata plate din abinci gabanta "oya ungo maza ki cinye" Faheema ta runtse idanunwata kad'an tana sake yatsina fuska kamar wata k'aramar yarinya "mommy... ta kirata cike da shagwa'ba atare suka d'ago daga mommyn nata har daddyn nata suka tsura mata ido domin jin damuwarta
"bana jin cin wannan abincin"
Hibba ta dubi abinci dake gabanta sinasir ce wacce miyanta taji naman kaza da kifi da alaiyahu idanunta na kanta har lokacin tace "to me zaki ci nasa Kemi tayi miki"
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomanceBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...