Chapter 7

279 10 0
                                    

Washe gari Faheema ta shirya zata gida wajensu big mommy tare da Faheam zai rakata, tana driving hadadiyar motarta wanda daddynta ya mika mata tun data cika 19years har suka iso gidan mai gadi ya bude musu gate ta shiga tayi parking, luckily for her big daddy yana gida murna a cikin Faheema kamar  kamar zasu fa'di a kasa ita da big mommy, big daddy ma haka taje ta rungumeshi duk dashi girma yazo masa sosai, "wai wai wai.. wa nake gani haka Likita bokan turai, just take a look at my beautiful doctor" big daddy ya fa'da yana dariya cike da matukar farin cikin ganinta.

Big mommy kasa rufe baki tayi tana fa'din "oyoyo oyoyo yar jikalen tawa, zozozo naji dumin jikinki yar'jikata guda, kinga yanda kika girma kuwa, kice na kusan samun suriki kenan" ta fa'da tana bude hannunta, Faheema ta sake karasawa taje ta fa'da jikinta suna rungume da juna cike da farin ciki.

Gaisuwa suka somayi, suna tambayarta ya hanya ya karatu kuma tace duk lafiya lau, yar'aikin gidan ta shigo tazo ta jera musu kayan motsa baki, aka shiga hira, Faheema ta jawo katuwar ledar tsaraba data shigo dashi ta mika musu, big mommy ta karba tana fa'din "student kuma da tsaraba Faheema, ke da kike fama da karatu a can ina ke ina daukan nauyin wani tsaraba" faheema tana dariya tace "ai wanan tsarabar taki ce ke kadai Big mommy banda big daddy"

Big daddy ya dubeta "banda ni kuma, me nayi aka ware ni a tsaraba?"

Dubansa tayi tace "Allah yasa kana nan, daman da biyu nazo gidan nan" ta juyo ta dubi big mommy" big mommy na kawo karar mijinki"

"O oh, to me kuma mijin nawa ya miki wanan Karan"

"Big momma could you imagine big daddy yanata ya'da ni wai bana kikranshi wai tunda na tafi sau da'ya mukayi waya, bayan kusan ko wani sati sai na kirashi munyi waya. Faheam dan Allah kai ba shaida bane dana dawo ai kaga call logs dina"

Faheam zaiyi magana, Hajiya ta dakatar dashi ta juyo tana duban mijin nata "wai haka?"

Dariya big daddy ya somayi yana girgiza kai "Faheema kenan rigima, yanzu har karata aka kawo gabana?"

"Yo ai dole na kawo kararka big daddy, tunda abun ya zama haka"

Gabadayansu sukasa dariya, "toh shikenan, yanzu dai nine da laifi ko, toh na ansa laifina. Sau da'ya ne nasan kin jera kwanaki baki kirani ba, amma you always call"

"Ah toh big daddy idan kaga ban kiraka ba toh exams nakeyi, kuma lokacin ai nayi maka bayani"

Big daddy yayi murmushi yace "toh shikenan, I agree with you on that. Kin kira kinyi mun bayani. In ce shikenan laifin?"

Shiru tayi sannan tace "for now kam shikenan, don nasan nan gaba bazaka rasa yin wani laifin ba"

Dukansu suka sa dariya, big daddy yace "toh apologies big daughter, bari na bada hakuri tun kafun a kamani da laifin gaban. An hakura?"

Faheema ta washe baki "eh an hakura, big mommy kina iya tsam mishi tsarabar"

Suka sa dariya, big mommy ta fara ciro kaya daga cikin leda, expensive lace da turare ta siyawa Hajiya shi kuma alhaji ta siya mishi agogo da turare da jalabiya masu matukar kyau guda biyu, gabadayansu suka nuna farin cikinsu sosai game da tsarabar, big daddy ya dubeta yace "sannu da kokari my doctor Allah yayi albarka"

"Ameen ameen"

Ya karatun dai, da fatan an gama semester da exams lafiya"

"Lfy lau alhamdulillah big daddy"

"Hutun sati nawa aka baku?"

"3 weeks ne but I'm going to spend a month insha Allah kafun na koma"

"toh masha Allah, ai muna so ki huta sosai tare damu. Allah ya kaimu lfy"

❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥Where stories live. Discover now