Ana cikin haka suka ji karar shigowar mota alamun har sun dawo daga pharmacy, Faheema ta mike ta tattara abubuwan datayi amfani da gefe, ba jima ba sukayi sallama suka shigo, cikin sauri Hibba ta karaso da Faheam biye da ita a baya da ledodi, "ya jikin nasa?" Ta tambayi Faheema cike da damuwa tana duban Ammar, yanda duk hankalinta ya da'ga yasa Faheema ta tausaya mata don tasan ba karamin so Mommynta ke yiwa Uncle Ammar ba "da dan' dama dama mommy, daman kafun kuzo na dan' goge masa jiki da ruwan sanyi saboda zafin jikin ya ragu"
"Toh madalla... sannu da kokari. Ya bai rufe jikinsa ba?" Hibba ta dubeshi cike da damuwa.
"Ai mommy idan mutum yana fama da high fever baida kyau rufuwa, it's better mutum ya kasance da light clothes har a samu temperature din nasa ya ragu" Hibba ta da'ga mata kai cike da Fahimta sannan ta dau'ra hannunta bisa goshin Ammar tana masa sannu, yadda Ammar yake jin ciwon jiki all over yasa ya kasa ma furta mata komai illa gyda amata kai dayayi. Faheema ta karba ledan hannun Faheam wanda shima ya karaso yana yiwa Ammar sannu, a hankali ta fito da kayan dake ciki, cike da kwarewa ta soma ha'da alluran da kuma ruwan drip. Mommynta ta dubeta "anan zaki sa masa drip din?"
"A'a sai dai muje daki"
"Toh mu taimaka masa mu shiga dashi ciki"
Jin abunda suke fadi a hankali Ammar ya soma kokarin mikewa suka taimakasa suka karasa daki, akan gado ya kwanta, Faheema ta gama ha'da masa ruwan drip da allura ciki ta saka masa tace wanan zaisa zazzabi da ciwon jikin ya ragu, sannu suka dinga masa tun yana jinsu har wani wahalalen bacci yazo yayi awon gaba dashi.
Hibba ta dubi yarta tana fa'din "sannu da kokari baby, Allah ya miki albarka"
"Ameen Ameen mommy"
Faheam ya dubeta yana murmushi yace "sannu Adda...you're already a certified doctor already, kawai ki fara aiki ba sai kin wani koma school ba"
Gabadayansu suka sa dariya, karar shigowar mota cikin gidan yayi indicating cewa daddynsu ya dawo, Hibba ta duba time taga it's almost 10pm, Ammar dai yana kwance idanunsa a lumshe, ruwan drip din yana di'ga yana bi ta hannunsa, Faheema itama ta dubeshi tace bayan 5 hours zata dawo ta duba drip din sai ta sake sa masa wani, Hibba tace ba matsla Allah ya kaimu anjima, tare suka karsa ta kashe wutan dakin suka fito tare, suna fitowa suka ci karo da daddynsu a parlor, sanye yake cikin suit looking clean and classy as usual, Faheam ya karasa ya karbi jakar hannunsa yana masa sannu da zuwa, Hassan ya shafi kan dansa yana murmushi, itama Faheema ta karaso tana fa'din "sannu da zuwa daddy, ya aiki?"
"Alhamdulillah my princess" ya bata ansa, Hibba itama ta karaso tana murmushi ta soma masa sannu da zuwa, kallo ya bita dashi yana murmushi yace "ya naganku duk a gida? Ina mara lafiyar?"
Hibba ta danyi murmushi tace "yana kwance ciki.."
"Yana kwance ciki, I thought it was serious? Meyasa baku je asibiti ba?"
"Ai sweetie your daughter deserves her medical license straight away, kasan ita tayi handling komai? Sanda na kiraka muna hanyar zuwa pharmacy nida Baba, by the time muka dawo jikin nasa yayi dan dama dama, yanzu ta gama sa masa drip yana daki"
Cike da mamaki Hassan ya dubi diyarsa yace "masha Allah this is wonderful, ko dayake ba abun mamaki bane, ban ta'ba samun wani shaka ko kokwanto game da ita ba, don ya'ta gwana ce ta wuce zaton kowa, I've always known she's going to do great, keep making us proud princess. Allah ya miki albarka"
Cike da jin dadin abunda daddynta ya fada ta rungumshi tace "Ameen...amma ya kamata ayi masa running tests daddy, duk da dai nasan bai wuce malaria dake damunsa ba"
Daddynta yace "toh gobe da safe Allah ya kaimu sai aje lab ayi masa test din koba haka ba"
Suka ce haka ne, tare suka karasa ya zauna. Hibba taje ta kawo mishi ruwa yasha, Faheam ya haura sama don ya kwanta, ita kuma Faheema daman bata ci abinci ba amman ganin it's late yasa ta debo fruit kawai ta soma ci, daddynta ya karasa dining shima light food yaci saboda dare yayi suka dan' ta'ba hira na kusan 30 mins kafun Hassan ya haura sama sai daya shiga ya leka Ammar tukuna wanda still yana bacci sannan ya haura sama, kafun Faheema taje sama zuwa dakinta itama sai data sake shiga ta duba Uncle Ammar sai data tabbatar everything is alright with him don tafi 20minutes kawai tana dubansa sannan ta kashe wutan ta fice daga dakin ta koma ta haura sama zuwa dakinta, by the time tayi wanka ta fito ta gama abunda takeyi, sha biyu har tayi, ta dauko wayarta taga miss calls sunkai ashirin a wayarta kuma duk na Nasar ne, sai a lokacin ma ta tuna bata kirashi ba ko ya isa gida lfy, tasan bazaiji dadi ba, time ta gani ta duba taga sha biyu ta gota, tayi tunanin kota kirashi a wanan lokacin, what'sapp ta hau ta tura mishi da sako nan take taga ya hau online yayi reply dinta, within few seconds sai ga kiranshi nan ta da'ga ta kara kunne, kafun ma ya fara magana ta soma bashi hakuri "dan Allah Nasar kayi hakuri, wlh bayan ka tafi we had an emergency ne, which I had to attend to"
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomanceBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...