"Uncle Ammar?" Yaji ta kira sunansa
Bude idanunsa yayi a hankali yace "na'am small..."
"Ka hakura?"
"Na me kenan?"
"Na rashin picking calls dinka da banyi ba on time?"
"Hmm ya zanyi..na hakura"
"Yay.." yaji ta fada cike da farin ciki
"Uncle Ammar?"
"Uhmm.."
"Yaushe zaka dawo?"
Shiru yayi sannan yace
"Yaushe kikeso na dawo?""Yau inda hali" ta fa'da tana washe baki
Dariya ya da'an sake "yau kuma small?"
"Eh mana"
"hmm okay, i'll think about it"
Marairaice masa tayi "uncle Ammar you promised fa, kace 5 days zakayi"
"It's only been 2 days since I left"
"Ehen still... ko baka so ka dawo ka gani, kowa yanata fa'din cewa na kara girma, kaima nasan when you see me you'll be surprised, zaka daina kirana smallie"
Dariya ya sake "ai ko kinfi Newark girma bazan daina kiranki small ba, so just forget about it"
Ta turo dan karamin bakinta kamar yana ganinta "hmmm... nidai yanzu kawai ka fa'da mun ranar da zaka dawo"
"Well let's see...hopefully this week insha Allah"
"Really?"
"Insha Allah"
"Toh uncle Ammar, Allah ya kaimu, can't wait"
Suna cikin maganar kiran ya soma disconnecting ta duba taga Nasar ne ke kiranta, bata da'ga ba ya cigaba da ringing har ya katse, call din ya dawo zatayi magana still abun ya sake disconnecting wanan karon declining tayi, Ammar ya tambayeta "kamar someone is trying to call you" murmushi tayi tace " yeah..it's just my colleague in school, I'll call him back when we're done"
Wani irin harbawa kirjinsa yayi jin ta ambaci na miji ne ke kiranta, nan take ya tsinci kansa cikin wani irin matsanancin faduwar gaba da tashin hankali "who is this your colleague?" Ya tambayeta
Innocently ta soma bashi labarin Nasar yanda suke mutunci a school, bata dai ambato mishi cewa ya nuna yana sonta ba, amma tunda ta fara masa wanan bayanin hankalinsa yayi mugun mugun tashi, bai dai nuna mata halin da yake ciki ba har ta gama yace mata okay, bai sake making further enquiries ba don wanda yaji is already enough, zai iya sa zuciyarsa bugawa, gudun kar ya fallass kansa a gabanta ya sashi fa'din "toh shikenan small, bari na barki ki huta ko, you need to rest. I'll talk to you later"
Faheema tace toh dukda dai bata so sun daina magana ba, amma ta lura kamar baya son ya cigaba da magana tace dashi "toh uncle Ammar, I'll talk to you later"
Haka ya katse kiran, yayi shiru yana nazari, har yanzu zuciyarsa bata daina bugawa ba, ya rintsa idanunsa, he can't even try to imagine her with another guy, Faheema rayuwarsa ce, bai jin zai iya rayuwa babu ita. tunaninta yaki barin cikin kwal'kwaluwarsa, yarasa wani irin zazzafan kauna yake mata ? Ya rasa me yasa yake sonta irin haka da har yake jin idan ya rasata arayuwarsa zai iya mutuwa ? Amma toh ya zaiyi? Ta ina zai fara bulowa wanan lamarin? Ya tuno zantukan Hajiya. Ita kanta yasan da wuya ta amince masa akan Faheema, so many odds were against it, sauran aikin da bai karasa ba kenan banda aikin tunani babu abunda yakeyi. Bangaren Faheema kuma yana katse kiran wayar Nasar ya kuma shigowa, tayi picking.
"Haba gimbiya, daga tafiya gida kuma shikenan an yada mutane, ai ba haka rayuwa tace ba" ya fa'da cike da zolaya
Dariya ta dan'yi "I'm sorry Nasar I've been very busy wlh these past few days, kasan sha'anin tafiya. Amma na iso gida lfy alhamdulillah, would have called you since but tun dazun muna tare dasu mommy ne"
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomanceBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...