Chapter 16

246 12 3
                                    

Gabadaya kallon kallo aka shigayi a parlorn, Hibba ta kurawa Faheema ido tana kallonta, ita kuma Faheema ta kurawa Ammar ido haka shima ido ya kura mata yana binta da wani irin kallo tamkar zai hadiyeta cike da zallar shaukinta, cikin zuciyarsa yake jin wani irin sabon kaunarta na bin lungu da sako na gangar jikinsa at the same time yana jin tsoro ko ta jiyo maganarsu da yakeyi da yayarsa. Hibba itama kanta ta shiga cikin rudani don from nowhere taga Faheema din, can kasan zuciyarta tana addua Allah yasa bata ji maganar da sukeyi ba. Ana cikin haka Faheam ya sauko sanye jikin jalabiya da alamun ya sauko zai je masallaci sallar magrib, cak shima ya tsaya ganin yanayin daya tadasu yana binsu da kallo "lfy..why is everyone tensed?"

Sai a lokacin Hibba ta kirkiro murmushin karfin hali ta dubeshi tace "babana har ka sauko"

"Eh na sauko mommy.." a hankali ya dawo da dubansa kan kawun nasa yana fa'din "uncle Ammar ka shigo, ya jikin"

Karfin hali Ammar ya tattaro yace "alhamdulillah da sauki Manchu, kayi shirin sallah"

"Eh na shirya, muje ko?"

Ammar yace toh, yana kokarin mikewa still idanunsa na kan Faheema, Sai a lokacin Faheema ta kawo wa kanta jarumtaka ta soma takowa ciki tana tafiya a hankali kamar wace kwai ya fashewa a ciki, a hankali Ammar ya dubi yayarsa cikin sanyayar murya yace sun wuce masallaci, tace toh sai sun dawo.

Suna fita, a hankali Faheema tazo ta samu wuri gefen mommynta ta zauna tayi shiru. Hibba ta dubeta "ya naga kin shigo duk kinbi kinyi wani iri?har ya wuce?"

Faheema ta gyada mata kai daga nan bata sake cewa komai ba, Hibba ta dubeta sama da kasa, nan take jikinta ya bata cewa tsap Faheema taji maganar da sukayi da Ammar "ya naga kin kinyi shiru?"

Hankali ta furta mata "ba komai mommy"

Cike da sanyin jiki Hibba ta kamo hannunta ta kira sunanta a hankali. Faheema ta ansa mata da "na'am..."

"Faheema nasan probably shigowarki kinji part of discussion da muke da kawunki but kada ki kuskura ki ce zaki saka wanan abun a ranki kina jin ko? Tun wuri inaso kiyi watsi da wanan maganar kamar ba ayita ba don Aure bazai ta'ba yuwa a tsakaninku ba, kap family babu wanda zai yarda da wanan ha'din, kinga dai Ammar kanina ne ko, ke kuma ya'ta and more than anything else I'll be after you both happiness but I'm your mother and I know what's best for you, kina zaune Allah zai fito miki da mijin aurenki, shima na fa'da masa yaje waje ya nemo macen aure amma ba ke ba, we have plans for you, munada burinmu sosai akanki nida daddynki, kuma alhamdulillah so far baki ta'ba disappointing dinmu ba, so ki kawar da wanan zancen daga zuciyarki ki cigaba da addua kina harkarki kamar ba ayita ba"

Tunda mommynta ta fara magana Faheema tayi shiru tana sauraronta, gabadaya cikin rudani take, ta rasa yadda zatayi da rayuwarta a wanan lokacin, komai jinsa take kamar a mafarki. Wai tsaya ma tukuna, ta ina zata fara digesting irin wanan information din? It's just too much for her, and uncle Ammar... the way he looked at her kafun ya fita, the conflicting emotions, there's just something about that look that made her heart flutter kuma ya jefata cikin confusion, yanzu haka she's just trying to picture everything but she's just seeing him in an entirely different light yanzu...

"Baki jina ne Faheema?" Hibba ta jeho mata tambayar tana dubanta

Cikin sauri Faheema ta dubeta tana zaro ido sannan ta soma girgiza kai "toh naga inata magana kinyi shiru kin kyaleni, kodai sonshi kike kema? in son nashi kike kamar yanda yake kirari sai ki fa'da tun wuri asan abunyi"

A hankali Faheema ta soma girgiza kai tana fa'din "a'a mommy...I..I just don't know what to do....the information is just too much for me to handle...I just can't think..."

"There's nothing to think about Faheema, I just told you, forget about everything and move on with your life, kina zaune Allah zai fito miki da wanda yafi dacewa dake, nima ina nan ina miki addua...a hankali zakiga komai ya tafi yanda ya dace, kinji ko naby...ki kwantar da hankalinki ki kawar da wanan tunanin" Hibba ta karasa maganar cikin sigar rarashi

❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥Where stories live. Discover now