Chapter 14

200 11 0
                                    

Bayan barinsu Ammar gidan, suna kan hanya sai da Jr ya sake tunasar masa akan kada yayi kasa da gwuiwa wajen tunkarar mahaifin Faheema kan maganar aurenta, idan yayi wasa toh yana ji yana gani zata zama mallakin wani, Ammar ya numfasa yace Insha Allah hakan ma bazata faru ba, he'll find time yayi discussing da Mr sooraj one on one. Sai da suka isa gidan Ammar, Jr ya da'an huta tukuna ya wuce nashi gidan.

Yau ta kasance ranar lahadi da safe misalin karfe sha'daya, Faheema ta mi'ke daga kan gado, jiya ta yini throughout da cramps sai yau dai ta samu ya lafa mata, taji jikinta ya da'n yi dama dama. A hankali ta mike ta shiga bayi ta tsaftace jikinta tayi wanka ta fito ta sanya kaya, wayarta ce ta fara vibrating ta dauko ta duba taga sakonni ke shigowa, ta bude taga Nasar ne, yana shaida mata he has been trying to reach her amma babu dama, ta kirashi when she sees his call. Tana gama karantawa kuwa tayi dialing numbersa, bugu da'ya ya daga kamar yana jira, cikin zazakar muryar nan nata mai kashe jiki tayi masa sallama, a hankali Nasar ya lumshe ido ya ansa yana jin wani irin sanyi dadi a ransa, tun jiya yaketa kokarin yaji muryarta amma bai samu dama ba, "your royal highness da girman kujerarki..." yayi mata kirarin daya saba cike da zolaya.

Murmushi Faheema ta danyi ta kira sunansa, "ai dole na gaida ki your royal highness, ganinki ko jin muryarki sai da ticket"

Ta danyi dariya tace "haka ma zaka ce"

"Haka ne mana, tun dana shigo kasar nan naketa kokarin samunki amma abun ya citura, daga naji number busy, ko call forwarded ko not reachable gabadaya, I was so worried, nayi tunanin ma ko zaki kira ki nemeni amma shiru"

Ajiyar zuciya Faheema ta sauke sannan ta soma bashi hakuri "I'm so sorry Nasar, wlh bawai na manta dakai bane, tun dana zo ne i've been trying to settle down shiyasa, abubuwa ne suka danyi mun yawa"

Nasar ya dan nesa sannan yace "toh shikenan, da fatan kina lafiya, yasu mommy?"

"Lfy su wlh, ya naka? Da fatan ka samesu lfy"

"Lfy lau, hajiya ma tana gaida ki"

Faheema ta dan murmusa tace "ina amsawa, nima ka tura nawa sakon gaisuwar gareta"

"Insha Allah zataji" ya bata ansa cike da matsanancin jin dadin abunda ta fadi don tun daya dawo a gida bashida wata zance sai na Faheema, maganarsa da'ya biyu Faheema har yan' gidan nasu sun saba da batunta, sun kosa suna so suga wacece wanan Faheemar data sauyawa dan uwan nasu tunani haka.

"Ya Nawla, kuna waya da ita?" Ya tambayeta

"Yes muna waya she's fine, tana can Florida ai can na barota"

Nasar ya dan jinjina don ko jiya sai da Nawlan ta kirashi suka gaisa, shi dai kam yana ganin kokarin Nawla wajen nuna masa kulawa da takeyi, from time to time ta kan dan kirashi su gaisa, she's so caring and loving towards him, unlike Faheema wace he hardly gets that kind of affection from her, sai dai shi yayi reaching out to her, amma ba dai tayi ba, atimes he thinks kamar tana mantawa da existence dinsa, yaso yayi kokarin cireta a ransa tun farkon rejecting dinsa da tayi amma ya kasa don yanda zuciyarsa ke muradinta bai jin zai iya rayuwa babu ita. A hankali ya dan numfasa sanna yace "what are you doing today?"

"Nothing, ina gida" ta bashi ansa

Yace "good, can I see you today? Ina so nazo mu gaisa, kinsan you promised me we are going to see anytime na shigo"

Faheema ta da'an nesa, tasan theres no way Nasar will back up akan son ganinta, dole ta hakura ta bari yazo ya ganta tunda ta da'u masa alkawari, kuma daukan alkawari kyansa cikawa, don haka tace dashi "toh shikenan Nasar you can come and see me amma sai na tambayi mommyn tukuna"

Wani irin farin ciki ne ya rufeshi don ko daga yanayi muryarsa zaka gane he's elated with her response  "Insha Allah zata ma bada izinin, what time kike tunanin zan iya zuwa"

❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥Where stories live. Discover now