Chapter 4

335 16 7
                                    

Tun faruwar wanan Nasar ya lura Faheama ta soma baya baya dashi, bata sakewa dashi kamar da,  hankalinsa ya kara tashi. Secretly ya kira Nawla gefe yana mata tambaya don ya kasa sukuni a tunaninsa maybe akwai wani cikin rayuwar Faheema daya sha mishi gaba. Nawla ta nunan mishi babu kowa, ita dai hakan take, bata kula kowa. It's just that she's too focused. Hakan ya kara bawa Nasar karfin gwuiwa sanin cewa babu kowa cikin rayuwar gimbiyar tasa.

Bai kara mentioning maganar gareta ba, yayi ma kamar irin wanan maganar bai ta'ba ha'dasu ba. Yana mata kamar yanda ya saba har ta dawo ta dan soma sakewa dashi. Ranar da sukayi hutu zasu koma Orlando, shi da kanshi ya kaisu airport ya ajiyesu. Bai so rabuwarsu ba amma consolation dinshi da'ya idan ya dawo Nigeria zai samu ganintah. Haka ya hakura sukayi sallama jirginsu ya tashi zuwa Orlando.

                                  ******
Bangaren su Ammar kuwa, tun last week yake Abuja kusan satinsa da'ya kenan sai jiya ya dawo lagos, daman plan dinsa was to spend 3 days ya dawo amma tafiyar daya tasowa AK zuwa Singapore, yasa dole ya kara kwana biyu yayi clearing komai kan desk dinsa tukuna ya dawo Lagos. Yau ta kasance ranar Asabar ya karaso gidan yayarsa, daman in baida aiki haka a gidan yake yini. Farhan da Fayha zasuyi resuming school ranar Monday so yake ya kaisu shopping su siya kayan komawa school daga nan su biya gidan big mommy suyi sallama da ita, big mommy itace kakar su Faheema tunda ita ta rike mahaifinsu tun yana karami, Ammar yana tunani anyi watani kenan rabonshi daya je ya gaisheta, yasan zai sha fa'da kam, yanayin aikinsa daya juya masa ne yasa baya samun lokaci idan ba haka ba, baya fashi zuwa wajen hajiya don dashi da yayarsa sun dauketa tamkar uwar data tsuguna ta haifesu. Zaune yake a parlour sanye cikin kananan kaya, jersey tshirt na liverpool da black jeans sai p cap a kansa. Kayan sunyi fitting kyakyawar surar jikinsa, waya ce a hannunsa yana danawa, sosai yayi zurfi cikin abunda yakeyi, Faheam ne ya sauko daga sama ya karaso cikin parlor sanye cikin kananan kaya shima maroon shirt mai zanen Marvel comics longsleeve da blue jeans yana fadin "Uncle Ammar we're ready"

A hankali Ammar ya dago ya dubeshi sannan yace "su Fayha fa?"

"Gamu nan Uncle Ammar" sukaji muryar Fahya tana saukowa a guje tazo ta fa'da jikinsa, sanye take cikin riga da skirt sai yar karamar hijab da mommynta ta daura mata. "Let's go" ta fa'da cike da doki tana jan hannunsa. Murmushi Ammar yayi yace "toh mamana, but let's wait for Farhan"

"Ya'Farhan hurry up if not zamu tafi mu barka" ta fa'da tana kwadawa Farhan kira

Bafi 2 seconds sai ga Farhan nan ya sauko yana watsa mata harara "kifi ruwa gudu"

"Uncle Ammar kaji abunda yace ko, mu tafi kawai mu barshi" ta fa'da tana turo baki

Dariya Ammar yasa, Farhan ya karaso ha'de da buga tsaki ya zauna gefen Ammar " Manchu" Ammar ya kirashi yana murmushi sukayi hannun da suka saba, tsabar buga game din PS5 yasa Ammar yasa mishi suna Manchu, don Farhan harkan games da computer kam sai Allah. Mostly idan Ammar yana nan tare suke bugawa shiyasa Farhan baida wani abokin hira sai kawun nasa, Faheam shi kam he's neutral babu ruwanshi, obsession dinsa daya shine jiragen sama.Suna cikin haka, mahaifiyarsu Hibba  ta karaso cikin parlor sanye cikin sea green lace tayi daurin dankwali daya fitting kyakyawar fuskarta, daman ita a ko da yauce zaka ganta tsap tsap very neat and petite.

"Har kun shirya" ta tambayesu

"Eh naga lokaci ma na tafiya, ana neman uku saura bari mu wuce yanzu, akwai wani abu da kike bukata ne?" Ammar ya tambayeta.

Yar takarda ta miko masa "ungo ku tayani dubawa ko za samu spices dinan"

Ammar ya karba yana duba takarda  "tam za duba miki" ya fa'da yana sa a aljihu.

"Dan Allah a kula, no wasting of time please, a samu da dawo kafun daddy ya iso gida, ga makulin mota, kuma ku gaishe mun da Hajiya"

"Toh mommyn daddy za'a kula kuma zata ji" Ammar ya bata ansa yana dariya ya karbi car keys din sannan ya kamo hannun Fayha sukayi gaba, Faheam da Farhan na biye a baya suna jerawa, idan ka gansu gwanin sha'awa kusan kansu daya tamkar twins sai dai Farhan yafi kama da mamansa. Shi kuma Faheam yana kama da babbansu, ko wannensu ya dauko zubin arab heritage, don kana ganin kasan akwai jinin larabawa daka kwarara a jikinsu.

❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥Where stories live. Discover now