Bangaren Faheema kuwa tana zaune a parlor da yar' takarda a hannunta tana dubawa wacce tun sanda Ammar ya fita akan idanunta bata sake haurawa sama dakinta ba, tunda safe suketa aiki da mommynta a kasa, suna gamawa mommynta ta haura sama itama Faheema ta haura taje ta watsa ruwa a jikinta sannan ta dawo parlorn ta zauna tana duba takardarta, karatu take amma tunaninta na can wani wurin, a yanzu haka babu abunda idanunta suke kwadayin sake gani illa uncle Ammar, har yanzu baiyi texting dinta ba tunda ya tafi, remote ta dauko ta rage sanyin ac parlor sannan ta kira Kemi tace mata ta ha'do mata coffee ta kawo mata, kemi cike da ba'rin jiki da zafin nama ta shiga kitchen taje ta ha'do mata coffee cikin mug ta daura mata kan tray ta kawo mata, godiya Faheema ta mata ta karba ta ajiye a gefe, a hankali ta mayar da hankalinta kan wayarta duk notification da zai shigo wayarta sai ta duba taga kona uncle Ammar ne, kasa hakuri tayi ta soma masa typing text ta tura masa tana tambayarsa ya isa gida lfy kuma karfe nawa zai shigo anjima da kuma abunda yakeso yaci ta girka masa? Bayan ta tura masa tayi shiru tana sauraronsa, shiru shiru babu reply har na tsawon 30mins tun tana duba wayar har tazo ta hakura, bangaren Ammar kuwa baccin da bai samu yayi ba kenan da Jr ya sashi a gaba don yana kwanciya baifi 20mins da rufe idanunsa ba sai gasu Mikhael suma sun shigo dubashi, suka cika shi da hayaniya da surutu, haka dole ya tashi ya hakura da baccin, har so sukayi su jashi su fita shkatawa ya basu excuses yace yana so ya huta, suka ce sun daga mai kafa tunda bai jima da farfadowa ba, basu suka bar gidan nasa ba sai wuraren la'asar ya rakasu ya tsaya massallaci yayi sallah tukuna ya dawo gida, kai tsaye bayi ya fa'da ya watsa ruwa a jikinsa saboda zafin da akeyi don babu mamaki su tashi da ruwa cikin daren don zafin yayi yawa, yana fitowa daga wanka ya dauki wayarsa ya kuna data, nan take karar sakonin suka soma shigowa wayarsa, ya dauko ya duba yaga texts din Faheema, "o my God..." ya dafe kai yana karantawa, har da miss call daya ya gani daga gareta, gabadaya ya manta shab da batun zuwansa gida, zuwansu Mikhael ne yasa baiyi tracking time ba ballantana ya samu time din texting dinta, text ya tura mata reply sharp sharp yana bata hakuri yace gashi nan zuwa, wasu abubuwa ne suka rikeshi amma tayi hakuri gashi nan, a hanzarce ya soma shiri cikin kananan kaya, dogon wandon camouflage, sai black tshirt da black p cap daya saba sanyawa a kansa, ya fesa ilahirin jikinsa da daddaden turarensa mai tafiyar da ruhi, yana gama shiri ya fito ya nufi inda ya tanada domin ajiye motocinsa ya dauki da'ya daga ciki yashiga tare da yiwa motar key yasoma ja cike da kwarewa masu gadi suka bude masa gate ya fita ya dau hanyar zuwa gidan yayarsa, within 8 mins sai gashi a layin gidan ya karasa gaban makekken gate din gidan yayi horning security suka bude masa ya shiga yaje yayi parking, daddaden kamshin daya saba fita a jikinsa ne yake karade duk inda ya shiga, yana taku a hankali, yana shiga parlor da sallama babu kowa ya karasa ciki, a hankali idanunsa suka sauka kan Faheema kwance kan three seater tayi zurfi da bacci da allamu tana cikin karatu ne bacci ya tafi da ita don ga littafi nan kwance bisa kirjinta, ido ya kura mata sosai tana ajiyar numfashi a hankali, kanta babu dankwali sai gashin kanta dake a tsefe yayi mata hijabi har ya wuce kafadarta ya zubo gadon bayanta, binta yake da wani irin kallo bai san sanda ya lumshe ido ba, duk jikinta babu abunda yake daukar masa hankali kamar long silky curly hair dinta, a hankali ya karaso cikin parlorn yana bin rigar jikinta da kallo wanda ya dan yaye a hankali har kana iya hango rise and fall din saman soft breasts dinta, yayi saurin ha'diye abun daya taso masa a makoshi sakamakon wani irin abu da yaji ya tsikareshi, a hankali ya karaso ya janyo gyalen dake yashe a gefenta ya rufe mata kirjinta dashi yana ajiyar numfashi, motsi yaga ta danyi sannan ta bude idanunta a hankali sukayi ido biyu, sosai ta kura masa ido tana kallonsa kamar tana so ta tantance ko shine, tana gama tantancewa tayi zumbur ta mike tsaye da wani irin matsanancin sauri daga kan kujerar datake kwance don wani irin masefafiyar faduwar gaba taji from no where ta dira cikin tsakiyar kirjinta wanda bata taba jin irinsa ba a duk iya tsawon rayuwarta, take zuciyarta tashiga rawa da tsalle game da ganinsa. Kallonta yayi na ya mintuna bai ce komai ba sannan ya tako ya iso gabanta ya tsaya yana kallonta tare da lumshe idanunsa, itama sosai take kallonsa kamar a lokacin ta fara ganinsa, a hankali bugun kirjin nata ya soma raguwa bayan ta gama tantancewa shine a hankali ta sakar masa lalausar murmushi. Shima murmushin ya sakar mata, Faheema tayi shiru tare da jin wani irin sanyayiyar dadi yana bin lungu da sako na ilahirin jikinta, ganinsa yanzu agabanta yasa komai nata ya tsaya cak tarasa me ma yakama tace masa, cike da tsantsar farincikin dawowarsa da jan hankalinsa gareta ta dauko gyalenta ta yafa akai "Uncle Ammar...yaushe ka shigo?"
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomanceBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...