By the time da Faheema ta iso gida la'asar harya gabato, ta kaarasa ciki, babu kowa gidan sai su Kemi a kitchen ta haura sama kai tsaye dakin momynta ta nufa tayi sallama ta shiga, zaune ta sameta gefen gado tana shirya kaya
Murmushi ta sakar ha'de da ansa sallamar "kin dawo Faheema"
"Na dawo mommy" Faheema ta fa'da tana zuba kayan data ruko kan kujera ta nema wuri ta zauna tana yaye gyalen kanta
"Washh na gaji wlh"
"Sannu da kokari dear, ya kika baro su Halima"
"Lfy su lau mommy, Ummi tace na gaisheki"
"Ina ansawa, suna nan Sunata faman shirye shirye ko"
"Eh toh nothing serious dai, suna danyi a hankali"
"Nima dai kam ya kamata na da'an lekasu cikin satin nan"
"Gaskiya dai kam mommy, ga sakon ankon naki nima na karbo nawa, dayan lace din na biya na baiwa Maman Hanan"
"Okay good" Hibba ta fa'da ta soma duba kayakin da take fiddowa. Sosai Hibba ta yaba kayan musamman ma lace din Faheema da zasuyi fitan dinner dashi, Faheema tace "Mommy sai nake ganin kamar Saqi din yafi kyau, ya tafi dani wallahi, ina jin kamar na had'esu duka na dinka dogayen riguna dasu"
"A'a why not ki dinka riga da skirt for the saqi zai fi kyau, na bridal shower kuma da dinner sai kiyi dogayen riguna"
Faheema tayi murmushi tace "toh mommy duk yanda kika ce, shiyasa nake son bidar shawarar ki wajen fashion da kwaliyya"
Hibba tayi murmushi tace "ai shi gyara da kwaliya yanada matukar muhimanci a rayuwar mace shiyasa nafi son kullun nayita ganin ki tsaf tsaf"
"Kai mommyna thank you so much, you're the best. I can't wait to rock these materials" ta fa'da cike da farin ciki tana ninke kayakin taje ta ajiyesu cikin wardrobe "mummy uncle Ammar fa, na shigo ban ganshi ba ya wuce ne?"
"Eh ya fita, yace zaije office ya dan'duba wasu abubuwan, sai zuwa anjima zai dawo" Hibba ta bata ansa, tana tuna yanda suka rabu da dan'uwan nata da safe, don jiki a sanyaye ya bar gidan tasan ta sosa mishi rai sosai da decision dinta amma babu yanda zatayi, he'll learn to live with it. Faheema ta jinjina kai "toh daddy fa, kunyi waya dashi"
"Munyi waya amma yace he'll be back early in the morning gobe"
Faheema tace "toh Allah ya kaimu, kuma ya dawo dashi lfy"
"Ameen Ameen"
Zanje na da'an watsa ruwa a jikina duk zafi nakeji wlh"
"Tam jekiyi wankan daga nan ki samu kiyi sallah, idan ki gama sai ki sauko. Nasan su Kemi sun kusan dawowa daga kasuwa ita da madam Laide"
"Toh mommy idan na iddar zan sauko" haka ta mike ta shige dakinta don tayi refreshen jikinta.
*****************
Bangaren Ammar kuwa, tun daya bar gidan yayarsa ya nufa company dinsu dake Bourdillon, yana zaune a office dinma gabadaya ya kasa concentrating, don akwai business deals da dama daya kamata yayi signing, sai yaji duk ya gagara, babu abunda ke yawo akansa illa kalamanta na cewa bazata amince mishi ya auri Faheema ba, duk ya kasa samun sukuni. Sai wajen Misalin karfe biyar na yamma, ya fito daga company din zai wuce gida wayarsa ta fara ringing, ya duba yaga abokinsa Ahmad Mufasa Jr ke kiransa, Jr shine younger brother din Mufasa wanda ya kasance abokin mahaifin Faheema, tare suke duk wani business deals, kuma sun jima sosai aminan juna ne na kud da kud, Jr zasuyi kusan sa'anni da Ammar don tare sukayi karatu a Singapore kuma akwai da'an shakuwa tsakaninsu don shi kadai ne abokin da Ammar yake hur'da, tun wanan tsautsayin daya afku dashi farkon zuwansa Lagos yasa yake taka tsantsan bai kara ajiye aboki ba sai kan Ahmed Jr. Kasancewar Jr auta yasa mahaifinsu Mufasa ya sakar masa sosai, sai dai bai cika samun nutsuwa bane, facaka yake da kudin mahaifinsa yanda yake so ga tarin yan'mata kala kala, Tun last week shima ya dawo kasar, yaje Brazil ya dawo yasa Ammar a gaba da kira, Amma Ammar na dodging don yasan fitan nasu na holewa ne shi kuma ba irin wanan rayuwar ya daukar wa kansa ba don yanada abun yi.
YOU ARE READING
❣️QALBINA 2❣️(FAHEEMA and AMMAR's love story)🔥
RomanceBai karasa sauran maganar dake bakinsa ba suka ji magana a bayansu "ke Faheema!..." Cikin sauri Faheema ta ware jikinta da nashi ta waigo tana duban mommnta dake saukowa saman matakala tana dubansu cike da ayar tambaya a kwayar idanunta, shima Amma...