*Maryam***
By✍️✍️
Salamah zakariya
Page 6
Muhammadul Ameen Pov
Yau da sauri ya shirya zuwa office Dan clearing wasu aiyukan, Dan he will be living to saudiya to see his mom. Koda ya isa kamfanin Bai amsa gaisuwan da workers kemaiba.
Cikin tafiyar sa na izza ya karaso cikin office din nasa. Zama yayi kan kujeransa. Jawo laptop dinsa yayi yafara submitting wasu file ta mail din kamfanin.
Zeenat pov
Da asuba zeenat ta tashi yau Dan samun gurbi a wajen aiki, sai da ta sallami yayanta da matarshi kafin ta tare cab zuwa A & Y perfumes and more campany Tana zuwa kuwa ta tarar ba layi Dan kusan itace farkon zuwa gurin. Sai da 7:00 am dot. Yayi kafin abude gate din camfanin. Masha Allah tafada a kasan zuciyar ta saboda tsananin hadewan kamfanin, alokacin da tashiga ne ma wasu ma 'aikatan suke shigowa. Ganin kowa ya kama aikin shine yasa ta yanke hukuncin tambayar office din manager kamfanin. A daidai lokacin ne tahango wata mata na hufanta murmushi kwance a fuskarta sai da to gab da gab da juna kafin matan tace "" how can I help you ma"" ahankali zeenat tace "can you please show me the way to the Managers office. Jinjina Kai matan tayi tace "follow me" matance agaba itakuma Tana biya da ita, har suka karasa bakin office din. Abakin kofar matan ta juya tabarta. Handle din kofar tarike zuciyan ta na bugawa, adua ta karanto a zuciyanta sanan ta shiga cikin office din. Wani mutun tagani zaune ya kafa waya a kuni da alama magana yakeyi. Ganin ta yasa ya katse wayan Yana fadin I will called you back.
"Gaishe shi tayi ""bayabo ba falasa ya amsa kamin yace " how may I help you"
Da mamaki tace " am here for the interview. Gabanshi ne yafadi tunowa da kalaman ogan nashi da yace in 24 hours time, wani zuciyan ne yace ya dauketa kawai dukda batabi procedure din neman aiki ba, daga ka yayi Yana Kare mata kallo balefi she's neat and classic. Amma saidai hijab din datasa yafiya tsayi zai hanata yin wasu aiyukan. Ganin b'ata wakanshi lokaci yakeyi kawai saiyace takawo credentials dinta yaduba. Dubawa yayi kan yabata appointment letter tacika. Gyaran murya yayi kanya fara koro mata dokokin kamfanin dakuma . Bayan yagama ne ta tashi da niyan yimai salama. dakatar da ita yayi tahanyar cewa"and miss zeenat yau zaki fara aiki, Dan hakanan ma yasa muka dauke ki aiki batare da mun bi wasu procedure ba. Mamaki me yakama zeenat Dan ita a tunaninta sai gobe ko jibi zata fara aiki. Ajiye mamakin ta tayi a gefe kan ta amsa da" ok sir . Batare da bata lokaciba yamata jagora zuwa office din. Shiya fara shi ciki kamin ita, Wani sanyayan kamshi ne ya buki hancinta da ya sanya ta lumshe ido kamin tabude su, Dan Kare ma hadeden office din kallon. Gaisuwan da taji manager nayine yasanyata juyowa. Gabantane yafadi ganin halitan Allah (S W T) domin kyanshi ya wuce misali, Dan a iya rayuwanta Bata ta'ba ganin kyakyawan mutum Kamar wanan mutumin dake zaune a office dinan ba. Tataro dukan nutsuwanta tayi kamin itana ta gaisheshi, dukda ba amsawa yayi ba. Sai da yagama rubutun da yakeyi sanan yadaga Kai yadubesu yace " what brought you here into my office this morning" da mamaki manager yakalle shi yace" sir am here with the PA". dauke idonshi yayi kan manager, ya dawo dashi kanta, Kare mata kallo yayi fuska a yatsine. Can sai manager daya gaji da tsayuwa yace"sir can I go" gyada Kai yayi ba tare da ya amsashi ba.
Kallon shi zeenat ta tsayayi batare da gajiya ba . Dago Kai yayi fuska a daure yace"would you stop staring at me and start your duty". A razane ta matso tace "what should I do sir " paper ya Miko mata na schedule din abin dayakeyi a kullum, amsa tayi taje tazauna tayi Dan tasamu taduba dakyau. Aranan yini duk sukayi suna aiki. Sai wuraren 4:30am yace ta tafi gida. A yayin da itakuma bataso hakan ba Dan Bata gaji da kallon kyakyawan fuskarshi ba dukda shi baisan tanayi ba.