Part 15

6 0 0
                                    


**Maryam**

 ✍️✍️

      By Salamah zakariya

Page 15

Kamar yanada umma tafada, haka akayi, ranan alhamis da Rana ya Ibrahim yaturo driver sa, daga Abuja Dan dauko maryam.

Kan tashiga mota, Saida taci kukanta, Tana rak'i, sai tayi kamar tashiga sai tadawo.

Hakan yasa umma yimata tsawa tace" wai Maryam yaushe zaki girmane wai, ace mutum zaiyi tafiya don niman ilimi, Amma kiyita kuka saikace wace akace intaje Bata dawoba.

Maryam tayi Narai narai da ido sanan cikin shagwab'a tace "toh umma kinyi alkawarin zaki riga zuwa duk bayan kwana biyu. Ganin Tana b'ata wa mutum lokaci yasa umma ta amsa da " inshallah Zan riga zuwa.

Tafiyan hour daya sukayi daga paikoro zuwa Abuja. Sai da sukagara wani tafiyan kan suisa gidan yayan dake unguwan GRA. Horn driver yayi, mai gadin yabude masu gate cikin sauri.

A hankali yakarasa cikin haraban gidan, dake da fadi, a parking lots yayi parking din motan, Yana gama parking ya zagayo, yabude mata murfin motan.

Tana sauka takama hanyar main entrance cikin tafiyanta a hankali.

Ido hudu sukayi da aunty ramla da tafito da gunta jin an shigo da mota. Murmushi anty ramla ta sakarmata tana fadi " you are highly welcome, my love"

Murmushi itama ta mayar mata sanan ta bi takefen anty ramla tashigo cikin falour. Kozama batayiba sai ga driver yashigo rike da trolley dinta datazo dashi. Ajiye wa yayi sanan yajuya yafice.

Kitchen anty ramla tanufa murmushi kwance a fuskarta. Rike da jug takaraso inda maryam ke zaune, har tacire mayafin jikinta Dan Shan iska.

Zub'a mata ruwan tayi tasha, sanan suka gaisa. 

Anty ramla dakanta takaita dakin da zata zauna, sanan tashiga toilet Dan hada mata warm wata Dan tai wanka.

Kare ma dakin da komai na cikin shi yakasance pink color Maryam tayi Tana tabe Baki.

Fitowa anty ramla tayi Tana kallonta tace" shiga kiyi wanka shap shap, saiki fito kici abincin, kinsan yau akwai gist, takarashe Tana kashe mata ido daya.

Murmushi Maryam tayi tace " toh bari inyi sauri". Anty ramla Bata Kara cewa komai ba ta nufi kofa ta fita.

Ajiyar zuciya tasauke kamin tafara rag'e kayan jikinta, drawall ta bud'e, taciro towel sanan ta shige toilet.

Tana fitowa taciro abayanta pink color ta sanya, batare da tashafa ko mai ajiki ba.

Abincin su sukaci a dining table, cikin nutsuwa batare da sunyi majunan su maganaba. Suna gamawa suka dawo palour, suka fara hiransu, sunakuma kallon tv jefi jefi.

Sai yamma, kamin zeenat ta dawo gida.suna hada ido suka sakarwajuna murmushi kamin su rungume juna cikin farin ciki.

Washegari da safe Yaya Ibrahim yakaita makaranta da admission dinta yafito don yin sreaning, dakuma biyan school fees. Sai kusan karfe daya suka dawo gida bayan lecturar din daya mata sreaning yace next week Monday zasu fara lecture.


Ran monday nayi Yaya Ibrahim yasata agaba yakaita har makarantar, duk da bataso fara zuwa ranan ba.

Ciro wani farin takada tayi da mutumin ranan yabata, dubawa tayi ko suna da lectures kuma bayan Wanda yafita .

Ganin basu da lecture kuma a ranan yasa tafito cikin makarantar ta tare cab zuwa gida.

MaryamWhere stories live. Discover now