BABI NA BIYU

166 8 2
                                    

Page__2.

*FATHIYYA*

Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*

*YAN TAGWAYE.....*✍️
*PAID BOOK....*#400

GA MASU BUKATAR ƳAN BIYU DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA ƊAYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)

ACCOUNT NUMBER

2083371244

Zenith Bank

Aisha m salis

A tura shaidar biya zuwa ga

+44 7894 142004

KATIN WAYA

+234 706 528 3730

________________________________
 Duk da tarin arziƙin da Alhaji Isma'il Madawaki keda shi, sai ya zamana dukkanin ƴaƴanshi mata ne ba yada ɗa namiji ko ɗaya in ba ɗan Amininshi da yake riƙo ba mai suna Mahmoud wato mijin ƴar shi Zinnira.

Mahmoud ɗa ne ga aminin Alhaji Isma'il da harkar kasuwanci ta haɗa su, da sannu kuma sai ya zamana shaƙuwa da zumunci ya ƙullu sosai a tsakaninsu ta yadda gaba ɗayansu suka koma tamkar ƴan uwan juna wato Alhaji Kabir Nafaɗa, ana haka wata rana tafiya ta kamasu zuwa Kano wajen harkar kasuwancin su inda zasu ajiye Haajar matar Alhaji Kabir wato mahaifiyar Mahmoud tare da Mahmoud ɗin da a lokacin bai wuce shekara biyar ba a garin Zaria zata je ganin gida, suna daf da shiga garin Kaduna suka samu accident.

Nan take ALLAH yayi wa Haajar rasuwa ita da drivern dake jan motar, Alhaji Isma'il da Mahmoud kuwa ko ƙwarzane basu yi ba, yayin da mahaifin Mahmoud kuma ke kwance cikin jini rai a hannun ALLAH bai ƙarasa mutuwa ba, ana ƙoƙarin ɗaukar shi zuwa asibiti ne ya riƙe hannun Alhaji Isma'il tare da janyo hannun Mahmoud dake faman girgizarshi yana kuka ya haɗe waje ɗaya, cikin jin jiki yake cewa  "Abokina ga amanar ɗanka Mahmoud nan na baka ka kula dashi sosai, nasan nauyi ne mai girma na ɗora akan ka amma yaƙini da kuma yardar da nake da ita akan ka ya sanya ni yin hakan, kayi haƙuri ni nasan ba lallai ne na tashi ba amma ina da tabbacin cewa matuƙar yarona ya rayu a hannunka to zai samu ingantacciyar rayuwa...."  kafin ya ƙarasa maganar ma ranshi ya ƙarasa fita.

Sosai Alhaji Isma'il ya yi kuka ya shiga damuwa da tashin hankalin rashin aboki, amini kuma ɗan uwa a gareshi  daga ƙarshe ya haƙura ya maida komai ga ALLAH don dukkanin mai rai mamaci ne, wannan dalilin ne yasa Mahmoud ya dawo zama a hannun shi lokacin Zinnira nada shekara ɗaya da haihuwa ya haɗa su duka ya ci gaba da basu kulawa, irin kulawar da idan ka gansu ba zaka taɓa iya banbance wa kace Zinnira ce ƴarshi shi Mahmoud ba ɗanshi bane saboda irin soyayyar da yake nuna mishi da yanda ya jashi a jiki, duk inda zai je kama daga kan Masallaci har zuwa harkar kasuwancin shi duka zaka samu Mahmoud a tare dashi, idan ba makaranta ba ko bacci babu abunda ke rabasu.

Hakan yasa ko daya gama haɗa degree ɗinshi na farko a fannin software engineering yana son fita waje ya haɗo masters Alhaji Isma'il ya hana shi saboda baya son ya yi nisa dashi musamman daya kasance shi ke kula da duka harkokin companies ɗin shi don shi bai yi karatun boko mai zurfi ba, iyakar shi Secondary School kaɗai ce yayi ya gama.

A lokacin kuma babbar ƴarshi Zinnira ta kammala karatunta na secondry school inda mahaifiyarta ta dage akan lalle ilalla sai dai a kaita waje taci gaba da karatunta a can saboda matsalolin da ake fama dasu na rashin cigaban karatu a fannin jami'o'i anan gida Najeriya, ko kaɗan Alhaji Isma'il baiso hakan ba har sai da Hajiya Maryam ta roƙi Mahmoud yasa baki cikin maganar sannan ya amince, a ɓangare ɗaya shima ko kaɗan bayan son zuwan Zinnira waje karatu saboda yanda yake matuƙar so da ƙaunarta, gashi yayi ta nuna mata hakan amma tayi kamar bata san yana yi ba don bashi bane a gabanta ganin cewa shi ba ɗan kowa bane face wanda mahaifinta ya tallafawa yake riƙe da cinshi da shan shi.

FATHIYYAWhere stories live. Discover now