BABI NA GOMA SHA UKU

72 4 0
                                    

Page__13.

*FATHIYYA*

Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*

Tana shigowa gidan jakar hannunta da mayafinta kawai ta ajiye ta kira masu aikinta suka hau faman ƙalƙale gidan duk kuwa da ba wani datti da yayi tunda kullum ne sai sun yi gyaran.

Sai da suka gama aikin taga komai yayi mata yadda take so tabi dukkanin gidan da turarukan wutan Scentsational scents masu matuƙar daɗi ta kukkuna a burners a cikin kowacce kusurwa ta gidan don haka wani irin kamshi ne yake tashi a gidan kafin ta faɗa kitchen tana aiki sauri-sauri don bata so Farouq ya dawo gidan bata gama ba. White basmati rice tayi da baked potatoes haɗe da shredded chicken soup sai pineapple and coconut drink da tayi mishi kasancewar yana son irin lemon sosai, sai fruits data yanka tasa a fridge.

Ɗakinta ta koma tayi wanka ta shirya cikin atampa Cote D'ivoire ɗinkin riga da skirt fitted, kwalliya ta zauna ta tsantsarawa kyakkyawar fuskarta sai faman sheƙi take yi kamar wata 'yar tsana don kyau, turarukanta masu sanyi haɗe da Khumrah's ɗin Scentsations Scents tabi dukkanin jikinta ta mulke duk yadda ta juya wani irin sihirtaccen kamshi kawai take fitarwa.

Wai wannan kwalliyar da ƙalƙale gida da girkin da tayi duk don ta samu Farouq ya amsa message ɗinta ne a ɗazu da safe tana fatan hakan ya kawo ƙarshen dogon fushin daya ɗauka da ita.

Parlourn ƙasa ta dawo ta zauna tana dakon shigowar shi gidan gabanta na faɗuwa kaɗan-kaɗan tana fata ba shigo-shigo babu zurfi yayi mata ba kada taje ya watsa mata ƙasa a ido ba wai ya huce bane sai dai kuma tasan halin Farouq in da bai fara saukowa ba da ko zata ɗige ba zai kulata ba, idan tayi wannan tunanin ne take samun 'yar nutsuwa kaɗan har ta saki jikinta ta cigaba da yin hidindimunta.

Bai shigo gidan ba sai bayan Isha yana cika yana batsewa kamar wani kububuwa, jiki a mace ta tashi ta taro shi tare da cewa "barka da dawowa Sweetheart" tare da miƙa hannu ta karɓi jakar Laptop ɗin shi, ga mamakinta sai taga ya sakar mata jakar saɓanin cikin kwanakin nan da yake gwasaleta ko ta taso da nufin tarbar shi.

Tana biye dashi a baya har suka haya sama, suna shiga bedroom ɗin tayi saurin ajiye jakar a bakin gado ta shiga bathroom ta haɗa mishi ruwan wanka.

Fitowa tayi tana faɗa mishi "Sweetheart ka shiga kayi wankan na haɗa ruwan".

"Um-hm" kawai yace ya cigaba da danna wayar shi, a lokacin ma chatting suke yi da Sameera akan manhajar whatsapp tana yi mishi ƙorafin rashin ganin shi a yau bayan ta saka rai da zuwan shi bayan tashin shi daga office shi kuma yana bata haƙuri akan rashin zuwan nashi sai faman lallaɓata yake yi kamar wata ƙaramar yarinya tana ƙara botsarewa.

Fathiyya dai na zaune tana kallon shi yadda yake ta faman sakin murmushi kamar bashi ne idan ya murɗe mata take rasa dukkanin wata nutsuwar ta ba amma gashi nan a gabanta yana yiwa wata a arha don tana da tabbacin da Sameera suke hirar nan yake irin wannan murmushin.

Sai bayan shuɗewar wasu mintuna sannan ya tashi ya fara cire kayan jikin shi, tashi tayi zata taya shi tana matsowa kusa dashi ya ɗaga mata hannu alamun ta bar shi fuskar nan tashi a murtuƙe.

Komawa tayi ta zauna jikinta a sanyaye, sai da ya shige bathroom ɗin har ya rufe ƙofar kafin ta tashi ta kwashe kayan daya cire idan ya fito zata kai su banɗakin ta zuba a laundry basket, wardrobe ɗin shi ta buɗe ta fito mishi da kayan da zai saka sweatpants ne da t-shirt da yafi tu'ammali dasu idan har yana gida a zaune.

Sai da ta feshe su da turare kafin ta ajiye tana jiran fitowar shi daga wankan, tana nan zaune ya fito daga bathroom ɗin, da hanzarinta ta tashi ta karɓi towel ɗin hannun shi ta taya shi goge jikin na shi, da taimakonta ya shirya cikin kayan data fito mishi da su.

FATHIYYAWhere stories live. Discover now