BABI NA TAKWAS

65 3 0
                                    

Page__8.

*FATHIYYA*

Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*

A fusace matuƙa ya bar ƙofar ɗakin nata zuwa nashi ɗakin, yau shi Fathiyya ke rufewa ƙofa saboda kawai ya fita hira, ita har tayi isar da zata wulaƙanta shi kamar wani yaronta ba mijinta ba, ai koda yake son ta bai yadda ta juya shi yadda take so ba, tabbas sai ya shayar da ita mamaki don zai gwada mata shi ɗin Farouq mijinta shine a samanta ba ita ba.

Akan gado ya zube wayoyin shi ya hau cire kayan jikinshi da yake jin sun yi mishi nauyi har yana fitar da gumi ga ƙirjin shi da yake ta hawa da sauka yana fitar da hucin ɓacin rai, ruwan sanyi ya sakarwa kan shi duk da yanayin garin akwai sanyi, sai dai duk da sanyin ruwan ya sanyaya jikin shi bai nasarar tafiyar da ɓacin ran shi ba saboda yanda zuciyar shi ke faman tafarfasa har yanzu.

Ƙaton towel ya ɗaura a kugun shi ya fito daga bathroom ɗin yana tsane ruwan jikin shi da karamin towel, ajiye towel ɗin hannun shi yayi akan kujerar ottoman dake gaban gado ya nufi gaban madubi ya shafa mai sama-sama ya shirya cikin fararen cotton pyjamas, turaren dunhill ya fesa a dukkanin jikin shi sannan ya koma kan gadon ya kwanta bayan ya janyo wayarshi don duba saƙon text ɗin daya ji ƙarar shigowar shi cikin wayar lokacin da yake shiryawa.

Bai san lokacin da murmushi ya subuce daga fuskar shi ba ganin sunan Samira rubuce a allon wayar shi alamar ita ta turo da saƙon tun bai buɗe yaga abinda saƙon ya ƙunsa ba, ganin sunanta kawai ya tafi da dukkan ɓacin ran daya samu kan shi ciki.

Sauri-sauri ya buɗe saƙon don ya matsu da yaga abinda ta rubuto mishi, hannayen shi har rawa suke yi tsabar zumuɗi.

       _"Ina jin labarin soyayya ne a da tamkar tatsuniya, amma a yanzu bayan na haɗu da kai sai na gaskata soyayya wata aba ce wadda ke da tasirin sanya farin ciki a cikin zuciya. Ina fatan zaka kasance tare da ni domin zama maganin damuwata na tsawon rayuwa. Da fatan ka koma gida lafiya"_

Murmushi kawai yake yi tare da maimaita karanta saƙon kamar mai bitar karatu, wani irin farin ciki tare da shauƙi ne yaji sun lulluɓe shi. Tabbas Maminsa gata tayi mishi data dage sai ya ƙara auren nan gashi tun ba'a kai ga yin auren ba ma ya fahimci hakan, wata irin soyayyar Samira ce yaji tana bin dukkanin sassan jikin shi tana gaurayawa, bai taɓa yadda mutum is capable of loving more than one person at the same time ba sai yanzu, shi a tunanin shi daga kan Fathiyya ba zai iya ƙara son wata ɗiya macen ba a duniya sai gashi tun tafiyar bata yi nisa ba zuciyar shi ta ƙaryata hasashen shi.

Ya daɗe yana juyi akan gadon yana ayyano Samira da kyakkyawar fuskarta, yanayin kallon ta daya kasa ɓoye tarin soyayyar da take yi mishi, da yadda take nuna jin kunyar shi, murmushin ta zuwa sanyin muryarta mai daɗi, ba zai ce ga lokacin da bacci ya ɗauke shi ba sai farkawa yayi yaga hasken ranar da ya ɓullo ta tsakankanin labule yana kashe mishi ido.

A gagguce ya sauko daga kan gadon ya faɗa toilet don yau dai ya makara sallah, abun da ya daɗe bai yi ba don ko bai tashi ba Fathiyya zata tashe shi, 'mts' yayi tsaki cikin ran shi da zuciyar shi ta bijiro mishi da Fathiyya da sassafen nan.

Fathiyya kuwa da ƙyar ta iya tashi daga ƙasa ta koma kan gado ta kwanta ba tare data cire kayan jikinta ba saboda kanta dake tsananin sara mata ko ƙwaƙƙwaran motsi bata son yi don sai taji kamar kan nata ne zai faɗo.

Ta daɗe a kwance idanunta na tsiyayar hawaye ga ciwon kan ya matsa mata bare ta samu bacci ya ɗauketa ko taji sauƙin damuwar dake cunkushe cikin ranta, mahaifiyarta ta tuna da a duk lokacin da take cikin damuwa takan ga ta tashi ta fuskanci ubangiji don miƙa mishi dukkanin lamurranta, don haka a sanyaye ta miƙe zaune haɗe da saurin dafe kanta da yayi bala'in yi mata nauyi, bedside drawer ta janyo inda take ajiyar magungunan ta ta duba tayi sa'a akwai paracetamol ta balli guda biyu ta buɗe ƴar karamar bedroom fridge ɗinta ta fito da robar ruwa ta sha maganin.

FATHIYYAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin