Page__5.
*FATHIYYA*
Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR**YAN TAGWAYE.....*✍️
*PAID BOOK....*#400GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA ƊAYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
A tura shaidar biya zuwa ga
+44 7894 142004
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
______________________________
Daga office gidan su dake Maitama ta wuce don tana da burin ganin mahaifiyarta.Tun daga bakin gate ma'aikatan gidan nasu ke gaisheta, sama-sama ta amsa musu ta wuce ciki, kallo suka bita da shi sanin ba haka ta saba amsa gaisuwar su ba, Fathiyya mace ce mai sakakkiyar fuska da rashin ɗaukar kanta wata aba shi yasa take zaune da kowa lafiya, daga yanayin mu'amalar ta da mutane baka taɓa cewa ita ɗin 'yar wani ba ce.
A main parlour na gidan ta iske ƙannenta Firdaus da Zahar. "Oyoyo sis" suka ce tare da tasowa suka rungume ta.
Itan ma rungume su tayi tana mai jin kewar 'yan uwan nata na daɗa lullubeta don ba ko yaushe take samun ganin su ba saboda tana daɗewa bata zo gidan ba suma kuma ba son yawan fita suke yi ba don haka sai su daɗe basu haɗu ba.
Zama suka yi akan doguwar kujera mai cin mutum uku, ƙannen nata suka saka ta a tsakiya kowacce ta kama hannun ta ɗaya ta riƙe.
"Sai ku kaɗai a gidan, ina Mamma?"
"Yanzu kuwa ta tashi ta shiga ciki, don Allah sis ki zauna mu yi hira kafin ki shiga wurin Mamma wallahi mun yi missing ɗin ki".
Harara ta danƙarawa Firdaus da tayi maganar. "Kuna missing ɗin nawa amma kuka kasa zuwa inda nake ku gan ni".
Dariya suka saka gaba ɗayan su, Firdaus na cewa "Allah sis ba zaki gane ba ne, Allah dole ce kawai ke fitar damu daga gida kamar dai zuwa school haka sai ko gidanki" ta ƙarashe maganar tana dariya.
Baki ta tabe tace "kwa ji da shi idan kaya ne, naga nan gaba ma aure za'a yi muku sai muga karshen rashin son barin gida", ta daɗe a wurin ƙannen nata suna hira kafin ta tashi ta shiga wurin mahaifiyar ta, ɗan zaman nan da tayi da su sai taji dukkan wata damuwarta ta yaye amma tana shiga ɗakin Mamma da suka haɗa ido sai taji wani irin rauni ya lulluɓe ta, a take idanun nata ya kawo ruwa ta fara zubar da hawaye.
Tashi Mamma tayi zaune daga kishigiɗar da tayi akan lafiyayyen gadonta ƙirar ƙasar Turkey.
"Ke kuma lafiyarki daga shigowa sai kuka? Ina Farouq ɗin, wani abu ne ya faru?"
Zama tayi a bakin gadon ta kifa kanta a kan cinyar Mamma tana cigaba da kuka har da shesheƙa.
Hannu Mamma tasa tana shafa mata kai zuwa gadon bayanta da sigar lallashi, bata hanata kukan ba har sai da tayi ya isheta kafin ta ɗago ta kalli Mamma tace "Mami ce ta nemawa Farouq aure tunda bana haihuwa, don Allah Mamma da gaske ne cikina bana haihuwa ba ne ni ɗin bana daga cikin mata masu haihuwa, kenan na zama juya tunda su ne basa haihuwa?"
Girgiza kanta Mamma tayi tace "ke ba juya bace Fathiyya, haihuwa ai lokaci gareta kuma Allah da yake bayarwa bai manta dake ba, In Sha Allah sai kin hayayyafa zuri'a masu albarka, aure kuma da Hajiya Sauda ta nemawa Farouq ba laifi tayi ba tunda ba haramci bane don haka akul kika saka damuwar ƙarin auren shi a ranki, baki sani ba ma ko ƙarin auren nashi ya zama wani sanadi na alkhairi a gareki.
YOU ARE READING
FATHIYYA
RomanceFathiyya! Labari akan wasu abokai kuma aminai guda biyu wato FAROUQ da MAHMOUD, inda ƙaddara tayi wa rayuwarsu ƙullin goro akan mace ɗaya mai suna FATHIYYA. FAROUQ shine masoyinta kuma mijinta da take jin cewa mutuwa ce kaɗai zata iya rabasu, kwats...